Sashe 14
Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Buturiyar dake dakin kusa da ita jin kalar kiran da take mata yasa tasan ba lafiya ba da sauri ta shigo dakin ganin halin da Zainab din ke ciki kuma dama Yarima ya mata bayani cewa koda bata da fly ga number wayar asibiti ta kira cikin gaggawa ta koma dakinta tana kiran number daya bata cewa suzo Zainab ba lafiya.
Dawowa tayi gurin Zainab dake ta murkususu a kasa jin doorbell yayi kara yasa ta tashi da sauri ta fita taje ta bude musu.
Cikin gaggawa suke hawa stairs din tunda suka fara hawa suke jin kukan baby da alama ta haihu suna shiga suka ga katon baby boy fatsi tar dashi sai kuka yake ita ma kuma tana cikin mawuyacin hali.
A rikice suka daga ta suna shiga toilet da ita Feshen kuma taji da yaron komai cikin sauri sauri suke yinsa bayan sun gyara ta suka fito da ita suka wuce asibiti bayan Feshen ta gama shirya yaron cikin kyawawan kaya.
Ayyuririiiiii mun samu baby boy yan Annuri ku shirya zuwa London ya same ku zamu sha shagali👻.
Kwanan ta biyu a asibiti suka dawo gida kuma jikin ta alhmdllh yayi ragal tayi tafiya, madara mai kama da nono ko dan basai nace babyn yai kama da Yarima ba dama hausawa sunce kyan da ya gaji uban sa to nan ma haka ne.
Zainab na zaune tana kallon babynta cikin farin ciki taji kamshin turaren da ko tana kabari yakai mata ziyara zata shaida da sauri ta dago dan tabbatar da abinda taji gaskiya ne.
Yarima ne tsaye bakin kofar bedroom din ya zuba mata ido yana murmushi mai burgewa mikewa tayi cikin farin cikin ganin sa taje ta rungumeshi saurin dago da ita yai yana kallonta yace "ina cikin"? dariya ta saki tana nuna masa gadon kallon sa yakai inda take nuna masa aikam sai ya sake bude ido akan babyn yana karasawa ya dauke shi cikin nuna tsantsan murna ya kalleta yana cewa "thank u my wife na gode kinmin komai Allah ya barmu tare "amin Zainab tace tana zama kusa dashi Yarima dake kallon babyn yace"beautiful like diamond, yaushe aka haife shi"? Zainab na kallon fuskarsa tace "yau kwana hudu"hada su yai da babyn ya rungume cikin dadin murya yace"sorry babyna daddyn ka ya tafi ya barka ko ayimin afuwa dole ce ta sani nasan kayi hakuri "dariya Zainab tayi tana cewa "kuma yanzu idan kaji yace babu komai daddyna fa yaya zakayi"? Murmushi Yarima yayi yana ajiye babyn ya cire kayan sa zai shiga wanka yace mata "me zanyi kuwa bayan farin cikin na samu yaro dan baiwa"yana kaiwa na ya shige toilet.
Lokacin daya fito Zainab na waya da mama ba kunya yazo ya zauna ya fara zubawa mama shagwaba baki bude Zainab ke kallon shi ko sai yaushe zai daina yiwa mama shagwaba? wata zuciyar tace mata sai ranar daya fara ganin nasa yaran suna yi masa kila ya daina Yarima ya saka ma babyn sunan mahaifin mama Ahmad mama tayi farin ciki sosai dajin wannan sunan.
Musty ne ya kira shi a waya cewa za suzo suna mama ta kira shi tace masa matar sa ta haihu maimakon Yarima ya bashi amsa sai yace "may be nima ban sani ba "da mmk Musty yace "kamar ya baka sani ba ina tare kuke? kaga prince bana son iskanci mene wai kake min boyan matar ka baka so na ganta kamar mara gaskiya sunan ma dazan zo sai kamin bakin ciki"tabe baki Yarima yayi yace "kaifa baza ka gane min mata yanzu ba sai lokacin dana diba ya cika dan wallahi idan ma ka rakito matar ka kuka zo zansa a hana ku shigowa saidai kuyi honey moon ku juya idan baby ne zan turo maka shi a waya ka gani"cikin haushi Musty yace "bana so ka hada har babyn ka dafa su ka cinye dan iska kawai "yana fadin haka ya kashe kiran murmushi Zainab tayi tana cewa "kana takurawa uncle din nan naka dan Allah ka barshi man yazo"kallonta Yarima yayi yace "ke rabu dashi dan rainin hankali".
Hindu ma an haihu Bashir kuwa baya ma gari yafi wata da barin kano Bilki tayi kuka ha saida hawan jini ya hauta mahaifanta Hindi kan sunyi da nasani har ba iyaka dan saida sukai shari'a da Bilki anan sauran dan abin hannunta duk ya kare dakyar ta samu kawarta Aliyah ta bata rancen kudi zata dora jari daga baya ta biya ta amma kafin ta bata saida ta mata tas ta gama kwashe mata sauran ragowar albarkar data rage mata halin mummunar kawa kenan rusawa mutum rayuwa.
Allah ya tsare mu👏
A gurguje bayan wani dogon lokaci mai tsaho Ahmad yayi girma abinsa sai shagwaba kamar abinci dama barewa bata gudu danta yayi rarrafe.
Suna zaune a palor da dare Yarima ya rasa yadda zaiyi da Ahmad ya dame shi ya cika masa kunne dole tasa ya mike yana goyon sa ya fara zagaya palon har said yayi bacci sannan ya kira Siana ta dauke shi ta saka masa kayan bacci.
Zainab dake kallon shi tun dazu tana son tayi dariya tace "kadan ka gani tunda haka ka rika yiwa mama shagwaba abinda bakai mata bama gashi kai anai maka "harara Yarima ya cilla mata yana cewa "ina ruwan ki so ne ya kawo haka"shiru Zainab tayi tana dariya.
Shekarar Ahmad hudu suka shirya zuwa Nigeria lokacin Zainab nada wani cikin murna gurin Zainab zata koma Nigeria bayan shekara biyar rabon ta da ita a daren dakyar tayi bacci dan farin cikin gobe kamar iyanzu suna tare da mama.
Washe gari gabadaya masarauta ta dauka Yarima zai dawo dan Hajara ba'a barta a baya ba da kanta taje kitchen ta tsaya akan girkin da akewa Yarima bayan an gama komai part din Yaha tasa aka kaima kafin ya sauka ita kuma ta wuce bedroom dan ta shirya.
Yahanasu dake labe ganin Hajara ta wuce yasa ta fito tana bude kulolin abincin ta barbade da guba ta mayar a hankali ta rufe cikin sanda ta koma part dinta tana dariyar farin ciki tasan yau duk tsiya burinta zai cika Yarima bazai sake rayuwa a duniya ba.
Tunda ta zuba tabar palon ba wanda ya shigo dawowar Mahmud kenan daga hospital ya dauko yunwa da gajiya ganin kuloli yasa shi fasa hucewa ya zauna yana budawa yunwa yakeji sosai dan haka ya dau plate yana diban abincin ya wuce dashi part dinsa zaici acan.
Ko wanka baiyi ba saida yaci abincin sannan yayi wanka ya shirya ya wuce garden dan yadan huta yaji ana Yarima zai dawo ma so yake su hadu ya fada masa gaskiyar dalilin dayasa umma take so ya auri Hajara dan ya gaji da wannan shashancin gara su daidaita da dan uwansa gaba ba abune mai kyau ba.
Gaskiya ne Mahmud gaba babu kyau. ⛔
Fadawan dake gadi a garden ne sukaji nishi yana fita kamar an shake wani za'a kashe da manyan fitilu masu haske suka fara dubawa can suka hango Mahmud kwance cikin tsoro sukace "waye wannan "? bai iya mgn ba sai hannu da yake daga musu daya daga ciki ne ya dan gane shi yace "ai kamar Yarima Mahmud nake gani "zuba ido sukai sosai suka gane shine cikin sauri sukai kansa suna salati suka daukeshi zuwa fada.
Suna shiga palon mai martaba cikin firgici kowa ya mike tsaye ana tambayar mai ya faru cikin girmamawa fadawan suka fadi inda suka ganshi gabadaya salati kowa yake to mai ya samu Mahmud din.
Saukar su Yarima kenan yace Zainab ta wuce part din mama da Ahmad su huta zaije gurin mai martaba yayi mmkn ganin gidan a hargitse bai tambayi kowa ba direct palon mai martaba ya shiga ganin palon a cike yasa shi leka inda aka zagaye.
Mahmud ya gani cikin mawuyacin hali ga Yaha na kuka kamar zatai hauka cikin sauri yai kneel down a kusa da Mahmud dasu dady ke rike dashi ga jini na fita ta hancinsa.
Durkusawa Yarima yayi yana girgiza shi yace "Mahmud lfy me ya faru dakai haka meke damun ka? bude ido Mahmud yayi dan tunda aka kawo shi yaki budewa ganin Yarima ne da gaske yasa ya fara kokarin barin jikin dady rungumeshi Yarima yayi cikin tashin hankali yace"me ya faru da kaine dan uwana "? idan Mahmud na zubar da hawaye yace"yayana dan Allah kayi hakuri ka yafe min tunda na taso mgnr arziki bata taba hada ni dakai ba kuma duk umma ce sila tace ba sona kake ba dan Allah ka yafe ni kada na mutu da alhakin zumunci a kaina".
Yarima duk a rude yake dan baya ma jin abinda Mahmud din ke fada masa kallon dady yayi yana cewa "dady ya kamata akaishi asibit_____bai karasa ba yaji yan falon suna salati girgiza shi Yarima keyi yana taba kirjin shi yace"Mahmud dan Allah ka tashi kada ka tafi ka barni".
Matsowa mai martaba yayi cikin dauriya yace"Muhammad kayi hakuri Mahmud ya riga mu gidan gaskiya yanzu kaunar da zaka nuna masa yayi farin ciki itace addu'a.
Mikewa Yarima yayi yana girgiza kai ya kasa mgn ba zato suka ga ya fadi kasa a sume a rude mai martaba yayi kansa ganin zai rasa biyu.
Dady dake durkushe shida Abba a gaban Mahmud yace "Mahmud fa ba mutuwa yayi mu kaishi asibiti tukuna "mikewa yayi wasu na taimaka masa ya fita da Mahmud aka sashi a mota suka wuce asibiti dan a tabbatar ya mutu ko yana da rai.
*Mrs Al'ameen Ahmed*
Be with me at always my lover's.
Ina gaisuwa sosai INDO da HAJARA ABLA'S Allah yabar kauna.
Maman khaleel ke ta daban ce.
#🌹YMA DUTSE 🌹#
*#Ana takai tawa za'ai makurar alfarma tajul-izzullahil-a'ala mai girma*#.
*#Komai idan aka bamu saidan daya na dayan da ba'a ji na biyunsa ba*#.
*#Mai alfarma abin yabo dan Allah Annabi kula da mu*#.
[11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲
*👑Yarima Abdul-malik*👑
*ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫
*#Yusrah Musa Abubakar*#
🅿🔟