Sashe 13
Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🅿️9️⃣
Zaune suke a gaban mai martaba kowa yana sauraron Yahanasu domin itace ta kawo korafi cikin muryar tausayi tace "ranka ya dade ni kuwa kuna jin labarin Yarima naga kowa ya manta da shi ba'a zancen sa kamar wanda yabar duniyar".
Cikin bacin rai mama tace "da ace kowa ya manta dashi uwa bazata manta da danta ba balle dukkan mu muna waya dashi kuma yana halin lafiya Yahanasu ina son ki tsaya iya matsayin ki ba ruwan da maganar sa akan zai dawo ko bazai dawo ba kinga Yaha bana son shishshigi malami a wajen rabon giya shiru mama tayi dan ta manta ma ita a gaban mai martaba suke haushi ne ya kama ta.
Yaha kuwa kallonta kawai take ta kasa mgn Abba da shima yaji haushin maganar Yahan yace "towai ke ina ruwan ki mene naki na tambayar anajin labarin sa"?
Dan shiru tai kamar bazatai magana ba sai kuma tace "naji lokacin dazai tafi ance wata hudu zaiyi ya dawo amma gashi har mun shiga wata na goma da tafiyar sa gashi bansan ina mgnr Hajara ta kwana ba domin shi muke jira Yaya ma ya kira ni nace masa ya kusa dawowa kodan ba laifinsa bane tunda ya tafi da wacce ta fishi sanin gari idonta a tsaye yak____tsawa Abba ya daka mata zaikai mata bugu dady ya rike shi.
Kokarin kwacewa yake cikin fushi yace"dan Allah ya ka barni wannan mara mutuncin bansan tsautsayin da yasa na aure ta Yahanasu sam bata dace dani ba yanzu sbd hassada wannan yarinyar zata kalla tace wai idonta a tsaye yake tana nufin ba yarinyar kwarai bace kenan"dady hakuri yake bawa Abba dan baya so abin yai nisa idan ya burkice bamai iya saita shi akan dadi.
Mama kan farin ciki tayi dan ko ba komai Abba na hana Yaha aikata wasu abubuwan taso dady ya sake shi ya nuna mata abinda ta fada tayi karya ba haka bane.
Salmah da tun dazu take kallon su dan batasan kowa ba tsakanin Yarima da Zainab sai labarin su da take ji tace"eh ya kamata a nuna mata kuskuren ta duk da banga yarinyar ba a iya zaman da mukai da Yahanasu nasan halin ta na kushe abin da bata ra'ayi na tabbata abinda ta fada akan ta ba gaskiya bane kuyi tunani tana so ya auri yar yayan ta ai bazata so matar saba idan ma ta sota saidai son fuska biyu dan Allah a duba dakyau kada a zargi yarinyar nan".
Abba dake hararar Yaha yace "keda kikasan gaskiya kenan amma ita ai ba tsoron Allah take ba "dady yace Ibrahim kayi shiru haka a gaban mai martaba kuke fa kokun manta?ya kamata ku nutsu"dukkan su shiru sukai mai martaba da tun dazu yake binsu da kallo sai yanzu yai magana "to Ibrahim dina idan ka gama fadan saikai mana addu'a shedan din daya shigo ya fita" ya fada yana murmushi dariya sukai dan ko kadan mai martaba bai nuna bacin rai da abinda ya faru yanzu ba.
Addu'a Abba yayi bayan an shafa mai martaba ya fara magana "to alhmdllh na fahimci inda Yahanasu ta dosa nufin ta lokaci yayi daya kamata ace Muhammad ya dawo anyi biki kamar yadda aka tsara na gamsu da wannan amma ban amince ba kar na sakejin an soki matar Muhammad domin yarinya ce mai tarbiyya.
Hajiya ta dora da cewa "wallahi kam gaskiya yarinyar nan bata da gurin kushe nida a barshi da matar sa ma karya wani kara aure a takura masa.
Mai martaba yace "a'a Aishatu mun riga mun karbi masa auren ta a gurin mahaifanta dan haka baza a fasa ba saidai idan ba matar sa bace.
Abba zaiyi mgn dady yace "Ibrahim kaga kayi hakuri Allah ya zaba mana mafi alkari"duka suka ce amin mama da batai niyyar fada musu cewa Zainab nada ciki ba ta rike sirrin a zuciyarta so take a musu ba zata saidai kawai su ga sun dawo musu da baby amma yanzu ta yanke shawarar fada musu lokacin da kowa yaji labarin hamdala yake da farin ciki.
Banda Yaha data mike tana fita a palon cike da kaduwa abinda take gudu ya faru idonta a rufe ta shiga part dinta a bedroom ta samu Hajara na kwalliya cikin barin rai ta kama watsi da kayan tana cewa "asararriya ni incan ina nema miki lafiya ke kina nan kina kwalliya gidan ubanwa zakije amma dai ba fita zaki ba "? .
Rike kugu tai tana jijjiga tace "wai dan Allah umma ina ruwan ki da sabga tane? nifa na tsani sa ido aikin banz____bata karasa ba Yaha ta wanka mata mari cikin fusata tace "yanzun Hajara abin naki yakai ace ni Yahanasu kanwar ubanki zaki iya zagi na wallahi daga yau baki isa ki kara fita daga masarautar nan ba tunda an baku hutu har sai Abdul-malik ya dawo gidan ubanwa kike zuwa kullum a cikin garin? wa kika sani"?.
Kuka Hajara ta fashe da shi tana fita daga bedroom din tace "na rantse da Allah baki isa ba sai naje duk inda nake so kuma sanda naga dama baki da ikon hana ni "cikin kunan rai Yaha ta bita da kallo ji take kamar ta kama ta tayi ta duka har sai ta daina motsi.
Anyi bikin Mustapha lafiya an gama duk abinda akai saida Musty ya turawa Yarima ba yadda Zainab batai dashi ba akan ya bata tagani fur yaki domin yasan komai zai dame idan ta gani yana gama gani ya goge dan karta dauka baya nan ta gani.
A London kan masha Allah zama suke cikin walwala ba karamin kyau sukai ba musamman Zainab da yanzu cikin ta ya tsufa suna zaune a palor doorbell yai kara mikewa Yarima yayi yana budewa wani soja ne cikin girmamawa ya masa rada juyawa Yarima yayi yana kallon Zainab da alaman damuwa a tattare dashi komawa yayi maimakon ya zauna sai yai upstairs mmk ne ya kama Zainab gashi ita yanzu tafiya wuya take mata balle ta bishi.
Tana zaune can sai gashi yana saukowa da kayan sojoji a jikinsa yana gyara bindigar hannunsa mikewa Zainab tayi tana kallonsa da sabon mmk tace "ina zakaje"? shiru bai bata amsa ba har wata mace baturiya ta shigo Yarima ya mata bayyanin yana so ta zauna anan tare da Zainab kafin su dawo zasuje Russia kwana goma zasuyi.
Amsa masa matar tayi da fara'a domin dama suna mutunci sosai dashi juyawa yayi suna fuskantar juna da Zainab ganin yadda hawaye yake zuba a idon ta yasa yaji tamkar ya fasa tafiyar yadau excuse baisan wanne kalar lallashi zai mata ba sai kawai ya juya cikin dakewar xuciya zai fice daga palon dan duk jarumtar mutum soyayya rauni take sashi.
Sunan da Zainab bata taba kiransa dashi ba yau ta kira da karfi cikin kuka tace "Abdul-malik! "cak ya tsaya amma bai juyo ba ganin haka yasa Zainab ta karasa inda yake tana rungumeshi ta baya cikin kuka tace "dan Allah karka tafi ka barni"xuciyarsa babu dadi ya juyo da ita zuwa gaban shi yana goge mata hawayen yace"kiyi hakuri kwana goma ne ba dadewa zamuyi ba zan dawo gare ki in Allah ya yarda ki kwantar da hankalin ki kada babyna shima yaji momyn shi na kuka kinji"kaita daga masa shi kuma ya bude kofa yana fita ko waiwayen ta baiyi ba wani irin kuka ne ya kuma zuwa mata ta kifa kanta jikin kofar tana yi matsowa kusa da ita matar tayi tana bata hakuri da kwantar mata da hankali dakyar ta samu tayi shiru suka koma cikin palon.
Yau masarauta cike take da murna domin Salmah nada juna biyu ba karamin farin ciki akai ba musamman Abba daya fidda rai da haihuwa.
Zaune Salmah take a palonta sai ganin Yahanasu tai kamar an cillo ta da mmk Salmah ke kallon ta ita kuma wannan lfy jitai Yaha tace"ke tun wuri ki nemawa cikin nan ubanshi dan saidai indashi kika zo dama kina kama da masu yawon tambadanci.
Mikewa Salmah tayi tana murmushi tazo har gaban Yahanasu tace"ke dallacan gafara gefe ke asuwa nasan duk abinda zaki fada ta haushi ta biyo ciki kuma ba ni nabawa kaina ba Allah ya bani idan kuma zaki ja da ikonsa ne to bismillah dan na fahimci ke bakar muguwar jahila ce ".
Daga hannu Yaha tayi zata mareta Salmah ta rike hannun tana mata kallon baki isa ba tace"humm yau ga hauka dangi dangi ke harkin isa wannan kazamin hannun naki ya taba min fuska never in history wallahi daga yau kada ki kuskura ki kara marmarin taba ni idan kuma kin dauka wasa ne ki jarraba saina dumama miki jiki da duka"tana fadin haka ta ture ta gefe ta wuce.
Da kallo Yaha ta bita ji take kamar ta fasa ihu dan takaici wannan yarinyar da bata fi sa'ar Mahmud ba idan takai ma amma har ita take bugawa warning zama tayi akan kujera tana kada kafa.
Hajara dake kallon su tun dazu ta sheke da dariya tana nuna Yaha a kule Yahanasu tace "dan uwarki me kike ma dariya"? tsayawa da dariyar Hajara tayi tana cewa"gani nayi duk iya makircin ki da feleken ki da fallin ki ya kare gashi kishiyar ki har take fada miki mgn sbd ta mayar dake sakarya".
Mikewa Yaha tayi a fusace tai kanta tana cewa "mitsiyaciya ni zaki cewa sakarya wallahi kika bari na kama ki saina fasa miki jiki".
Da gudu Hajara ta fice tana dariya tace "kaji min umma da wani cin zali mai zazzabi daban mai shan magani daban nasan kishiyar ki kike son fadawa wadannan maganganun bazaki iya ba sbd kina tsoron duka shine kika fake da guzuma kike zakin karsana wallahi babu abinda kika isa kimin".
Abu kamar wasa yau Yarima kwanan su 21 da tafiya amma babu alamar su gashi kotayi kiransa a waya saidai taji a kashe gabadaya tasa damuwa a ranta bata ko iya sakewa taci abinci.
Zaune take misalin karfe 1pm na dare ta kasa bacci tunani ya hana ta sakat waya ta daga da niyyar ta gwada kiransa ko zatai sa'a ta shiga batasan lokacin data cillar da wayar ba ta saki wata kara tana kiran aunty Feshen.