← Book details Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 20

Sashe 10

Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama na part din ta tasa aje a taho mata da Zainab kamar yadda ta basu umarni haka suka taho da ita sun rirrike ta da kyar take daga kafa duk inda suka gifta bayi ne ke zubewa suna gaisuwa har suka iso gun mama murmushi mama tai tana kallonta tace "sannu kinji dota Allah ya miki albarka ya baku zuri'a ta gari sunkuyar da kai Zainab tai hawaye na sauko mata so take tacewa mama ta fasa auren amma ta kasa mgn kyakkyawan gyara mama tasa akai mata wanda saida taji gara na Yariman ma yafi sauki akan nasu bayan sun gama shirya ta gurin mama suka dawo da ita suna fita a palon a gaba mama ta sata sai taci abinci idan ta gama ga hadin magunguna nan ta sha dakyar take cusawa har lokacin jikinta rawa yake suna haka Yarima ya shigo bako kunya ya zauna kusa da mama yana kwantar da kansa a jikinta yace "fatan kin tashi lfy momyna "dago shi mama tai tana murmushi tace "lfy na tashi babyna fatan kaci abinci "? Bata fuska yai jin abinda maman tace ganin haka yasa taci gaba da cewa "daman na sani ga abinci wanne kake son ci "shiru yai dan haka tadau spoon tana debowa tace "amsa mana babyna "kalar tausayi ya koma yana kallonta a shagwabe kai mama ta girgiza dan saidai tamai abinda ta saba dura Zainab abin har daure mata kai yake tunda tazo gidan nan bata taba ganin yaci abinci dan kanshi ba saidai a masa dura mikewa yai bayan mama ta gama bashi ya shiga bedroom din ta jin kamar zaiyi amai itama tashi tai tana cewa Zainab "dota kema kici abincin nan idan ba haka ba zan miki dura kamar yadda naiwa baby bari in dawo "fita tai Zainab na zaune Yarima ya fito yana kallonta yace "wai ke baki iya gaisuwa ba ko nayi miki laifi ne yau din "? Dagowa Zainab tai ganin idonsa a kanta yasa tai saurin dauke kai tana mikewa tai hanyar bedroom din ta da kallo ya bita kamar zaiyi dariya sai kuma yace "dan gurgu dawo ki zauna ni tafiya zanyi idan kunya ta kike ji "rabuwa dashi tai ta shige ciki shi kuma ya mike yana fita a part din.

Kyauta mai matukar girma Zainab ta samu a gurin familyn gidan dan Yaha ma dole saida ta bada sarkar da ta ajiye sbd auren Hajara kamar ta kurma ihu lokacin data mikawa jakadiya ranar kusan kasa bacci tai kuka kam dama tayi shi tunda aka fice da sarkar daga part dinta sarka ce ta lu'u lu'u kowa yayi mmkn wannan kyauta ta Yahanasu da hajiya na sa mata albarka kuka ta kama sbd bakin ciki amma sai tace dadin addu'ar hajiyan ce ta sata kuka.

Cikin kwana biyun daya rage su tafi ba karamin gyara tasha ba har mmk take idan taga yadda mama ke kula da ita batai tunanin zata sake samun irin wannan gatan ba tun bayan rasuwar mahaifanta dan abbanta mutum ne wanda ya iya soyayyar yaron sa ya kuma bashi tarbiyya ta shikimammiyar hanya shi yasa ta tashi da nutsuwar ta Umar mutum ne wanda yasan abinda yake ba hayaniya a rayuwarsa.

Ana gobe zasu tafi mama na part dinta suna zaune tana mata nasiha Yarima ya kira mama a waya bayan ta daga yace "am mama ina son paper da biro "da mmk mama tace "me zakai dasu kuma wa zanbawa ya kawo maka"? Dan kasa yai da murya yace "please ki bawa dotar ki ta kawo min dan Allah ina jira "mama dake kallon Zainab data zaro ido tace "baby mgn muke da ita zan turo wani ya kawo maka ko kazo da kanka ka karba"cikin shagwaba yace "haba mah dina yanzu zata dawo tana kawo min kinsan bansan koda wanne lokaci a rika shigowa inda nake dan Allah ki bari ta kawo min"ok dota je ki kaiwa baby paper da biro ki dawo yanzu sai mu karasa maganar "murmushi yai lokacin da mama tace haka kafin ya kashe kiran mikewa Zainab tai jikin ta na rawa tasa hijab ta fita dare ne amma kamar rana sbd hasken fitilun daya haska ko'ina a masarautar bayi ne keta ayyukansu wasu na zaune suna dan hira dai dai zata shiga part din taji anja hijab dinta da sauri ta juyo dan dama a tsorace take cikin mmk take kallon Hajara data rike mata kamar tana da gadon sa tun batai mgn ba taji Hajaran tace ke yar tsuntuwa uban me zaki a wannan part din idan bakin saba da karuwanci ba ko kunya bakiji ba ki sato jiki ki taho yawon kwartanci anyi asara dai kodan ba laifinki bane laifin wadancan bakaken munafikan naki da suke goya miki baya duk zanci uwar________bata iya karasawa ba jin wani irin gigitaccen Mari ya sauka akan fuskarta cikin fushi Zainab ta soma mgn"me kike daukar kanki an fada miki kowa sa'an rainin kine? duk abinda kika taka na fiki ki sani kinyi tsararo baki kai ba naji ni ba jinin sarauta bace amma inason kisan cewa ko ke da kika kasance jinin sarautar a yanzu aka jera tsakanin ni da ke kinsan wa yafi dacewa da wannan sunan idan har bakya kallon fuskar ki a mudubi gobe ki fara dan ko kadan bakya kama da jinin sarauta kinfi kama da jinin farauta ina miki gargadi daf da duka ni yanzun ba sa'ar yinki bace na zarcewa tunanin ki idan kika kara tara ta da irin wannan banzar mgnr jikin ki ne zai fada miki kuma bamai daukar mataki a kaina na daki banza juyawa tai tana kallon mahmud daya zuba musu ido tace "yaya Mahmud kai ya kamata ka fada mata wacce ni idan bata sani ba tunda bakuwa ce "dariya ce ta kama Mahmud ganin yadda Hajara kebin Zainab da kallo yace "mantawa nai amma yanzu ai ta gane wace ke "mai da kallo sa yayi gurin Hajara yana cewa "madam kinga sakamakon tauri kai sai kizo mu wuce dan ba iya rama marin ki zaki ba "wata ashar Hajara ta sakar masa tana kara shan gaban Zainab tace "ke ai ban gama dake ba gidan uban wa zaki saina tattaka ki a gurin nan yadda gaba idan kin hangoni zaki sauya hanya da wuri "wani irin kallo Zainab ke mata batare data sake magana ba ta janye ta gefe tana wucewa karo tai da mutum da sauri tai baya dan batai tunanin Yarima bane saida taji ya dauke ta tagane dan ba mai wannan ikon idan bashi ba bude kofa yai ya shiga tare da rufowa wanda yasa Hajara fasa ihu tana dukan Mahmud dan shi ta fito rakawa wani gun da tasan zata ga wannan abin da bata fito ba ganin yadda bayi suke kallon ta yasa ta daina dukan Mahmud ta soma dankara musu zagi ba arziki suka baje wasu na dry wasu na Allah ya kara.

Hajara suna komawa part din Yaha ta kama kuka cikin tashin hankali Yaha tace "menene me akai miki "? Cikin kuka Hajaran tace "ba Mahmud bane yace na raka shi shine muka hadu da Zainab a gabansa ta mareni amma sai ya kamai mun dariya wai maganin tsokana ta "bacin raine karara a fuskar Yaha tace "ta mare ki lallai ta mari ajalinta kai kuma dan ubanka mara kishin zuci a gaban ka wata banza mara asali ta mari yar uwarka amma sbd matacciyar zuciya baka tattaka taba kayi koli koli da ita shashasha baka da wani amfani "wucewa Mahmud yai zuwa part din shi yana cewa "akan me zan daki yar mutane tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa yake duka wallahi nan gaba ko cewa kikai Hajara ga Zainab zoki mata duka to saidai ita Hajaran taki taci duka nima fa wani san inason gaskiya banga laifin taba data mareta itan kinji irin maganganun data rika fadawa zainab din itama ta rama tace batai kama da jinin sarauta tafi kama da jinin farauta kuma kalli Hajaran ki gani sai kace 'yar gidan masu kiwon karnuka "ya karasa maganar yana dry cikin hangulowa Yaha tace uban ta ne yake kama da jinin farauta shegiya tsintacciyar kan hanya kawai mara asali wa ya sani ma ko shegiya ce tazo ta samu guri tayiwa mutane karya san ranta kila ma bata da iyaye yar karuwa ce ".

Uhm Yaha kenan manya maganin karagar kasa.

Yarima kam suna shiga ya dire ta akan gado yana mika mata hannu alamar ta bashi paper cikin sauri ta mika masa duk ta kadandane sbd daukan ta dayai ta matse ta a hannunta dagowa yai yana kallonta yace "aikin lalata pepan bazai rubutu ba, wai dama kin iya fada haka ashe dage na aura ba sani ba shikenan na huta zaki iyayin fada da makiyanki yanzu zaki koma ki kawo min wata pepan ne "? Shiru tai fin minti biyar taki mgn rabuwa da ita yayi ya dauko sabon littafi ya yagi pepan ya fara rubutu zaro ido Zainab tai me hakan ke nufi dama yana da littafi ma dan yasa ta wahala ne saida ya gama rubutun sa tsaf sannan ya linke pepar yana ajiyewa ya juyo inda take zaune yace "me kike jira ko anan zaki kwana na kira mama na sanar da ita kince zaku hadu da safe "? Cikin sauri ta girgiza kai tana sauka a gadon tare ta yai batare dayai mgn ba ya cire hijab din dake jikin ta jan hannunta yayi suka koma bakin gadon yace "dama ba peper zaki kawo min ba kwana kawai zaki taya ni tsoro nakeji "duk da tashin hankalin da take ciki saida ta dago tana masa kallon mmkn da shima yaga hakan gira ya dage yana mata kallon so what dan marairaicewa tai kamar zatai kuka kuma ta kasa mgn tana ji tana gani ya daga waya ya kira mama yace tsoro yake ji Zainab zata taya shi kwana mama har kwarewa tai sbd mmk dakyar tace saida safe saboda kwaruwar datai murmushi yai bai sake bi tan hawayen da take ba ya dauke ta suka hau gadon yana kashe fitilan dakin.

Saida safe zeey tsiyata da sabon shiga kenan barawo da sallama wai shishshigi malami da rabon giya.
Chapter 10 · 0% Book details