← Book details Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 20

Sashe 19

Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin data fito kin karasawa gaban mirron tayi ta toge daga bakin kofar bathroom din tana kallonshi tace"soulmate dan Allah ka rabu dani na tafi iya gaisawa zamuyi da mama saina dawo "wani mayan kallo ya mata dayasa yawun da zata hadiya ya sarketa ta hau tari da sauri ya miki yana bude fridge ya dauko mata ruwa ta sha dagowa tayi tana harararsa tace"dama so kake na kwaru shiyasa kake min irin wannan kallon"murmushi yayi yana daukarta yace "tsiyata dake duk abinda ya sameki saiki camfa kice nine to bari mu gani idan da gaskene abinda kika fada"direta yayi akan gadon ta mike zata sauka ya riketa yana cewa"abinda yasa zan nuna miki nayi kewarki yanzu sbd lokacin da zamu taho dasu mai martaba ina kallo kina min dariya na share don nasan akwai ranar dazan rike ki ba mai cetonki shiyasa nima na gama tara ki sai yau maman baby dina"kiss ya sauke mata wanda ba zato yaso fitar ta a hankalinta ba shiri ta rungumeshi tana kwantar da kanta akan kirjinshi zagaye hannunsa yayi a bayan ta tare da cire towel din dake jikinta ya fara bata zafafan abubuwa masu rudar da kwakwalwa gabadaya sun manta komai sun shiga cikin shaukin farantawa junan su wand ba karamin kewa sukai ba kasa rabuwa da juna sukai sunajin tamkar su dauwama a haka Yarima kan ya nuna mata yadda ake missing don har saida tayi kuka ya rabu da ita.

Washe gari suka je asibiti akai mata scanning kuma an tabbatar yan biyu ne maza wai murna dama ba'a mgn ba kunya Yarima yana kallon dasu mai martaba a gurin amma ya rungumi dady yana masa albishir ba iya su mama ba hatta mai martaba saida ya masa dariya.

Cikin tsokana Hajiya tace"baban mazaje wato gasa kake dani don kaga yayana duk maza kaima kake haifar maza ko"? hade rai Yarima yana kallonta zaiyi magana yaji mama tace"amma baby tafiyar da zakayi kai kadai zaka koma daga baya idan ta haihu ta biyo ka "? ba kunya ya tada rigimar tare zasu tafi mama tace bai isa ba mai martaba yace ta barsu su tafi dole ta hakura tun dare suka gama shiri washe gari kamar wanda ake korarsu tun wuri suka wuce mama har mamakin wannan sammakon nasu tayi.

Ba karamar tarba suka samu ba gun aunty Feshen ba tayi murnar dawowar su har ba iyaka ta rungume Ahmad tana masa barka da dawowa duk da yaso manta ta.

Karfe shida Umar na harabar gidan da ball a hannunsa wata buturiyar yarinya ta shigo da murnar ta tana tambayarsa ina Ahmad.

Umar ya riga yasan halin Ahmad don haka ya sheka mata karya cewa sun fita da dadynsu tare fita tayi tana ce masa idan ya dawo tana nemansa zata dawo fitowar Ahmad kenan Umar ya fesa masa July nazo nemansa.

Ahmad dake rike da wani kyakkyawan agogo yana shirin budeshi a kwallinsa yace"me kace mata"? dariya Umar yayi yana cewa"nace kun fita kaida dadynmu shine ta tafi amma wai zata dawo kana da farin jini"harararsa Ahmad yayi yana cewa"rufe min baki haka kada wani yaji muje mum tace na kira ka "juyawa sukai suna shiga ciki gidan dariya sosai Umar keyi abin na cinsa kuma ya kasa fada Zainab tace"bansan haukan ka rufa ma mutane baki "rufe baki Umar yayi yana kallon Ahmed daya zuba masa ido dan yasan dashi yake yace"mum juliana ce tazo neman sa "matsowa Ahmad yayi zai rike shi yana cewa "wannan munafiki mum karya yake bata zo nema na ba "Zainab tace"to naji zo zauna inma tazo neman ka mizaka mata share abbana tsokana yau yake ji da ita.

🌹Mrs Al'ameen Ahmad*

Aminci ga mufitahul jannatun na'ima.
Aminci ga kiblar bayi a ran kiyama.
Aminci ga mai shiryawa cikin salama .
Aminci ga duk mai matsayi dakai ya samu .
Aminci ga duk mai girma dakai ya samu .
Aminci ga duk mai daraja dakai ya samu.
Aminci ga fatuhul-akbar aya imamu Yusrah Musa ce tare dani da gaisuwa ta. 👏🍒🍒🍒🍒🍒.
[11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲

*👑Yarima Abdul-malik*👑

*ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫

#Yusrah Musa Abubakar

Dedicated to
Maman khaleel
Zarah Musa

🅿️1️⃣5️⃣

Satin su uku da komawa London Ahmad da Farouq suka fara zuwa makaranta Zainab ma wata babbar makarantar Yarima ya sai mata don ta sake kwarewa akan fannin couse din aikin likitanci.

Salmah na da ciki itada Hajara mama ke fada ma Zainab harda murnarta zata je Nigeria amma Yarima yace ko airport baza taje ba ta dauka wasa yake saida suka haihu taga ya dauki iya Ahmad sun tafi harda kukanta amma yayi kamar baisan me take ba itama tayi fushi dashi daya kirata a waya taki dagawa har ya dawo kuwa, duka mace suka haifa 'yar Salmah taci sunan hajiya Aisha 'yar Mahmud taci sunan Zainab suna ce mata Amra.

Bayan yan watanni Zainab ta haihu 'yan biyu maza murna dama ba'a mgn kamar yadda Yarima yace haka yayi ranar suna sukaci sunan dady Yusuf da Abba Ibrahim su Fati kam anzo suna sai farin ciki ake don Musty cewa yayi daga nan zasuyi honey moon dinsu kullum sai sun fita shida Fati sunga gari Zainab cikin tsokana tace "Allah idan kikai wasa kafin ku koma zaki jewa da ammi tsaraba dan naga abin naku ya wuce gona da iri "Fati dake dariya tace" to dafa me kike tunani sai kuje suna "harararta Zainab tayi zatai mgn mama ta karaso gurin sai kawai tai shiru.

Ahmad da Farouq kullum sai sun fita da Rufaidah ya nuna mata abubuwa har mama na tsokanar sa tace"babana kodai son rufaida kake? idan 'yar gida za'a yi shikenan mun huta "tun kafin Ahmad yayi mgn Farouq yace"tab that mean war kenan wallahi idan July ta ganta akwai yaki domin a school din mu ba wacce take kula shi sun san halin ta tsoron July suke masifaffiya ce sosai"duka Ahmad ya kai masa cikin hade rai yace "karya yake grandy ni July ba sonta nake ba ko sallah fa yan gidan su basayi me zanyi da kirista"ya fada yana kaiwa Farouq wani sabon dukan.

Murmushi mama tayi tana cewa "to kinji fa dota danki nada farin jini tun yana yaro ya fara tara masoya gashi har kin samu suruka wai July ".

Dariya Zainab tayi tace"akwai wata 'yar bayan gidan mu itama sonshi take sunanta sweety ai inaga kawai idan zaku tafi zai biku yayi karatun shi acan daga baya ya dawo muma hankalin mu zaifi kwanciya".

Bata fuska Ahmad yayi yana cewa "nifa mum karya yake min ba wacce take sona".

Fati tace"dama nasan sharrin zeey ne rabu da ita me zakai dasu ga Rufaida kawarka ita kake so"kin mgn Ahmad yayi mama tace "a'a ku kyale min babana shi babu wacce yake so tashi tafi kada su takura min kai su hana kayi karatu "mikewa yayi yana barin gurin ganin Farouq zai bishi ya dau sandan da suke buga ball yana nuna shi yace"idan ka biyu ni "dariya Farouq yayi yace"to wazai jefo maka kwallon da zaka buga idan ban biyo kaba"banza ya masa ya wuce da gudu shima Farouq din ya bishi don kar yasawa kofar lock.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya lokacin Fati itama ta kusa saukewa amma Zainab bata sa rai da zuwa ba don tasan Yarima bazai barta ba.

Batasan ma anyi haihuwar ba sai ana gobe zasu tafi yace tayi shiri fati ta samu yan biyu murna agun Zainab kamar ya mata albishir da aljannah harda wani abokin Yarima mai suna Abeed da matarsa suka tafi yace yana so yaga yadda Nigeria take itakam Zainab bata taba ganin sa ba amma musulmi ne.

Ba karamar tarba suka samu agun mama ba yaran kuwa gabadaya suna gurin mai martaba Salmah da ta shigo tana musu barka da zuwa dariya Zainab tayi tana kallonta tace"wallahi Salmah yaranki duka da Abba suke kama "Salmah data harareta tace "to dani kike so suyi kama ai akace kyan da ya gaji ubansa oho dai kema nakin da dadynsu suke kama "dariya mama ta musu tace "yau kuma shirmen da zakuyi kenan"? Salmah tace"dan Allah gane min hanya aunty wai makaho yaso gulma abinda na fada gaskiya ne"mama tace"a'a ni babu ruwana karma ku sako dani".

Washe gari suka wuce kano aka debi garar suna inda namijin yaci suna Abdul-malik macen Zainab anan take cikin tsokana fati tace"sai mu rika ce musu baby da dota".

Wata uwar harara Zainab ta bata tana fada harda kufan baki dama tasan tsokana tasa suka saka sunan su wallahi bazai yiwu suna kirar mata sunan miji ba.

Musty yace"ni Abdul-malik dane a gurina dan haka boy ma zan rika cewa yaron"fati na dariya ganin yadda Zainab ta tsime tace"hum haba dota arziki nefa kayi bako ya yanka ka mene dan munce haka kudin yayan mune"duka Zainab takai mata cikin haushi.

Satin su biyu a kano Zainab tace zata wuce bauchi gurin su Addah ta bawa mama su Ahmad ta koma dasu Abuja mama tace a'a taje dasu suma agansu tare da Salmah suka wuce babbar karba modibbo yayi musu Yarima sbd ya baro Abeed a Abuja da yayi kwana daya sai ya tafi ya barsu daga baya zasu taho.

Da tayi sati biyu itama ta koma Abuja dan Salmah ta riga ta tafiya komawar ta da kwana uku sukai shirin tafiya london Mahmud a gaban kowa yadau Amra yace ya bawa Yarima kyautar ta kowa yayi mmk saidai sunsan da dakuma yanzu ba daya bane godiya sosai Yarima ya masa ya kuma karba hannu biyu .

Tun dare Yarima yacewa Abeed zai wuce dasu Ahmad london su zauna a gurin sa kafin su karaso yana son Zainab zatayi hajj ne.

Zainab basan sunyi haka da Abeed ba tunda Yarima bai fada mata saudia zasu tafi ba saida washe gari suka je airport taga abu saba'in hankalinta.

Cikin mamaki tace"soulmate ya naga haka? ina kuma zamuje naga ka bawa Abeed yaran gabadaya "? bai bata amsa ba sai gurin Abeed dayaje sukai mgn kasa kasa sannan ya dawo inda take ganin yadda tayi da fuska yasa Yarima yayi murmushi tana kallo jirjinsu ya tashi ta dauka wasa yake mata amma sai taga ko a jikin sa.
Chapter 19 · 0% Book details