← Book details Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 20

Sashe 18

Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

YA RASULULLAH
Ka saita bayi akan hanya ta islama a koyarwar ka harda ladabin sanya takalma abinci kwa kar a cishi sai ansa hannun dama bismillah ayi baza a ci da shaidan ba.

Ya shugaba kasan abinda dake xuciyata ko a munbari ko a ayari kana ko a halin kadaita banda kai aya sayyidil khalki Yusrah banda sauran bukata ka cika burika na akan ka rainon Halimatus-sadiyyah.

Gaisuwa mai tarin yawa
Indo Abla's Rabi'ahh Bichi my Feedoh and maman khaleel ❤4ever.
[11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲

*👑Yarima Abdul-malik*👑

*ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫

@YUSRAHMS ABUBAKAR#

🅿️1️⃣4️⃣

Cikin nutsuwar damuwa Moddibo ya fara musu bayani"dalilin dayasa Umar yabar gida shine na tashi zan kaiwa sarkin Gombe ziyara sai Umar yace yana son muje tare dashi Umar shine auta na kuma inaji dashi ina sonsa fiye da sauran yarana muka tafi tare dashi ina farin cikin ganin sarki ya yaba da hankalinsa da nutsuwar sa sai ya sameni akan yana son zai bawa Umar auren yarsa da murna ta na amshi mgn amma dana same shi akan ga abinda sarki yace kansa tsaye yace wallahi baya sonta ranar dama ana gobe zamu dawo gida ne Umar haka ya daga min hankali sai mun taho a ranar sbd wannan mgn ko fada kin komawa yayi sbd kada kunyar sarki tasa ya amince babu irin lallashin daban masa ba dakyar na samu yaje yaga yarinyar amma duk da haka yaki yarda ".

Shiru modibbo yayi zuwa wani lokaci har kowa ya fidda rai bazai sake mgn sai kuma sukaji yace "bayan mun dawo gida da wata daya sakon sarki ya same ni akan idan mun gama daidaitawa da Umar shi a shirye yake banyi kasa a gwiwa ba gani ga Zainab (Addah) na sake samunsa akan mgnr amma dai batun daya ne baya sonta shi ba yanzu zaiyi aure ba raina ya baci dajin haka nasan Umar yaro ne mai biyayya amma a wannan lokacin ya juya min baya idan ina lallahin sa sai naga tamkar kara hura masa wutar kiyayyar yarinyar nake yi a xuciyarsa wannan abinda yayi ya bakanta min sai ya nayi masa barazana da cewa saidai ya bar masarauta ya kama gabansa indai bazai fidda ni kunya ba".

Banyi tunanin idan nace haka zai tafi ba amma sbd kiyayyar yarinyar a jininsa take saiya amince ya barmu akan ya aure ta ya kama hanya batare da kowa ya sani ba hatta kayan jikinsa saida ya sauya su yasa na talakawa kwarai da kar ayi masa kallon wani kuma ya rufe fuskarshi domin kowa ya sanshi bai dauki ko tsinke daga cikin dukiyarsa ba tana nan har yanzu ina jiran ranar da zanga jininsa domin dukiya ta dansa ce ".

Cikin dare yabar gida amma labari bai sameni ba saida gari ya waye sosai wasu fadawa da suka gane shi suka zo sukace min Umar yabar gida jiya da dare lokacin da suka iske ni da wannan mgn nasa abi bayansa na baza mutane ta ko'ina cewa su bishi a boye suga inda zaije wadanda suka shiga kano neman sa sune suka zomin da labarin cewa Umar nacan ya sauka a wata anguwa farawa gurin wani malamin addini da naji haka zuciya ta tayi sanyi kuma hankali na ya dan kwanta nasa wasu boyayyun mutane suke kula min da duk wani motsinsa har yayi shakara guda a kano ko murmushi Umar yayi sai sun fada min ance yayi aure a cikin wannan shekara dayan".

Bayan auren sa da wata biyar suna zaune shida malamin suka tsinci wata budurwa data kasance bata cikin hankalinta har suka fara yi mata magani ta samu lafiya itama umar ya aure ta mamaki ne ya kamani da naji ya auri mace har biyu bayan kin auren ne yasa yabar gida lokacin da masu kula min dashi suka zomin da labarin Allah ya azurta Umar dina da samun haihuwa daga sabuwar matarsa nayi matukar farin ciki kuma nasan tunda haka ta faru zai nemi ya dawo gida amma baiyi hakan ba har shekaru takwas suka wuce baida niya da naga haka saina kudura a zuciyata zanje da kaina na taho dashi ".

Rana mafi muni a gurina shine ranar da masu suka lura dashi suka zomin da bakin labarin cewa mota ta buge Umar kuma tun a gurin ya mutu nayi kuka nayi bakin ciki har sai da hawan jini ya same ni nayi jinya sosai a wannan lokacin wanda ko Zainabu ban fadawa ba gudun abunda zai faru da ita nabar sirrin mutuwar a zuciyata nayi tunanin zan warke da wuri nasa aje kano a taho min da iyalansa suzo suga danginsa amma abun nawa sai gaba yake karshe sai kasar waje aka fita dani don a nema min magani shikenan karshen rabo na dajin labarin su kenan wannan kuma shine dalilin barin Umar gida da rayuwar da yayi ".

Kuka sosai modibbo keyi ya duka bisa gwiwoyin sa a gaban Zainab yana rike hannunta yace"ina neman gafararki jikata lallai nayi kuskure kuma nidin mai laifi ne a gareki ina roko ki yafe min nayi miki ba daidai ba bansan wacce kalar rayuwa kika samu kanki ba bayan rasuwar Umar ki gafarce ni " kuka Zainab ta kama tana girgiza kai gaba daya ta kasa mgn dukkan sauran ahlin modibbo ma kuka suke da wadanda suka san Umar da jikanun da basu sanshi ba sosai moddibo ya bawa Zainab hakuri yaki tashi gaban ta har saida tace ta yafe shi.

Kallon Yahanasu mama tayi tana mata alamar kin gani ko babu wanda bashi da dangi saidai kaddara ta raba shi dasu sunkuyar dakai Yaha tayi cikin kunya dan komai na masarautar yafi nasu lallai tayi kuskure dole ta nemi gafarar Zainab abinda ta mata.

Bayan komai ya lafa sosai modibbo yayiwa mai martaba godiya da rike masa jika da yayi hannu biyu babu kyama mai martaba ya nuna masa babu komai yiwa kaine ba karamin farin ciki modibbo yayi ba ganin Ahmad da Umar ga kuma Yarima mijinta aka gabatar masa da mama cewa yayar mahaifiyar Zainab ce uwa daya uba daya yayi godiya har ya rasa inda zaisa kanka yaji daidai .

Mama ta taya Zainab farin ciki ganin ta samu dangin mahaifin ta Yaha kam da kukan ta tanemi gafarar Zainab ita kuma ta nuna mata komai ya wuce dama can bata rike ta ba.

Azahar nayi sukai shirin komawa Abuja amma sai modibbo yace abar Zainab ta musu kwana biyu daga baya za'a kawo ta mai martaba ya amince duba da suma suna bukatar ta a halin yanzu bayan sunyi sallama aka musu rakiya zuwa airport har da Ahmad da umar suka tafi domin Zainab din ta samu nutsuwa sosai kuma ta fahimci su modibbon Yarima kuwa ba'a mgn hade rai yayi zaiyi magana mama ta janyi shi dole ya hakura.

Iya tsantsan gata Zainab na gani daga gurin kowa kamar basu da jikanu haka suke mata gata kuma ko da wasa bata fada musu irin zaman da sukai da Bilki ba domin ita ba mai tsegumi bace.

Haka rayuwa take tafiya har Zainab tayi wata guda a bauchi ta saba da kowa kuma ta gane kowa abin mamaki babu wanda ya kula tana da ciki saida tudunsa ya fara fita anan taga sabon gata tamkar yarinyar goye suka maida ta har dariya take idan sukai mata wani abun data cika wata biyu modibbo yace ya kamata ta koma gurin mijinta domin kar su shiga hakkinsa.

Ranar da zata tafi bayan ta gama shiri tana shiga gurin modibbo saida tayi tuntube sbd mamaki Yarima ta gani zaune suna zance da Addah yaci uban wanka kamar ka sace shi ka gudu suna hada ido suka ji kamar su rungumi juna saidai ba hali.

Nasiha sosai suka mata tare da damka dukkan wata dukiyar Umar a hannun Yarima tunda shine mijinta dole shine mai alhakin kula mata da dukiyar da suka zo tafiya Zainab kuka take ita bazata tafi yau ba Yarima dake kallonta a ransa yace ji wannan yarinyar tana neman dora min hawan jini dakyar ta yarda suka tafi har airport tana kuka bata daina ba shi kuma bai hana taba yace gara ta morewa sabon da sukai haka suka zo Abuja ko mgn batai masa ba saboda dariyar da yake mata.

Anan ma kamar wata bakuwa haka suka tarbe ta kowa na murnar dawowar ta bayan an gama gaisawa part din Yarima suka shiga duk abin nan bai lura tana da ciki ba saida ta cire hijab din jikin ta sannan ya gani matsawa yayi kusa da ita yana dora hannunsa akan cikin dagowa tayi tana kallonsa ya daga mata gira alamar yadai.

Dan hade rai tayi domin ita fushi take dashi ganin yadda take kallonsa ya jawota jikinsa yana rungumeta cikin kasa da murya sosai yace"wato ciki gareki amma kika ki fada min don karna gaisa da my little one dina to Allah ya kama ki sorry baby yanzun kuwa zaka gaisa da dadynka"bata fuska tayi jin abinda yace ta soma yaja baya tana cewa "nifa bani da lafiya "kallonta yayi yace"oh da gaske haka mara lafiya yake nuna karfi daman ji yadda kike girgiza jikin ki fa kuma kice baki da lafiya yarinya baki isa ba bari nayo wanka kiga abinda zai faru "yana fadin haka ya shige toilet da gudunta tayi hanyar fita amma sai taji a kule tsayawa tayi a bakin kofar harya fito kallonsa tayi a marairaice tace"don Allah soulmate ka bude min kofa kaya kawai zan dauko a part din mama na dawo bani dasu anan"murmushin mugunta ya mata yana nuna mata kan gado kalla tayi taga sabin kaya iya ganin ta kuma duka nata ne kamar zatai kuka take kallonsa har lokacin murmushi yake yace"yadai mumyn baby na akwai magana"harararsa tayi tana daukar towel ta wuce domin tayi wanka.
Chapter 18 · 0% Book details