← Book details Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 20

Sashe 15

Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gudu Aliyah ta shigo gidan Bilki kamar an jefo ta tana huci ta soma kwalla kiran Bilki a razane ta fito daga daki tana cewa"haba dan Allah Aliyah wanne irin abu ne? wannan ai saiki sa hawan jini na ya tahi irin wannan kira haka kamar wacce ciwon hauka ya kamata".

Cikin bacin rai Aliyah tace "oh abinda zaki ce kenan sbd baki gaji mutunci ba zuwa nayi ki bani kudina dana ara miki dan wallahi bazan yarda ki lumar min dashi ba idan kuma ba haka ba zamu hade a gaban hukuma".

Kallon mmk Bilki ke mata tace"yanzu Aliya duk irin mutuncin da muke dake ni kike fada ma wai zamu hadu a gaban hukuma akan wata shegiya dubu ishirin to bazan biya dama matsalar bakar kawa kenan sai dai ta kaita halaka ta baro Allah ya isa tsakani na dake".

Kallon banza Aliyah tayi mata tana cewa"yauga munafikar mace ni kin manta abinda kikai min na miki dare kika min rana nifa na hada auren ki da Umar amma sbd baki san halacci ba ni kuma kike dan waken zagaye gurin mijina kamar ba tare da ke muke yawaon ba saida kika sa ya sake ni dama nace saina dau fansa shiyasa na turo Bashir a boye yazo ya jone dake dan nasan halin san zuciyar ki duk wata shawara Bashir dani yake kafin ya aikata kuma ko Zainab da yace ki aura masa ni nace yace haka idan kin gama cin kudin sa da sunan zaki bashi Zainab nace masa idan anje gurin daurin aure yace da Hindu za'a daura ba Zainab ba shiyasa na zuga ki kika kore ta sannan nasa ya wargaza rayuwar Hindun da bakya so ta wulakanta yanzu fada min tsakanin nida ke waye ya samu nasara akan wani kuma wallahi saikin biya ni kudi na kinji na fada miki".

Bilki data gama kulewa da maganganun Aliyah cikin bacin rai tace"bazan biya ba mitsiyaciya makira Allah ya isa ban yafe miki ba tsinanniyar mace ni nadauki duk yarda ta na baki ina miki kallon mai sona bansan da makiyiyata nake kawance ba bankadaddiya yar tasha karamar 'yar iska wallahi duk abida kika taka na fiki nima din kafar baya ce".

Shakota Aliyah tayi tana cewa"idan kika sake zagi na wallahi saina zubar miki da hakora akwai mitsiyaciya bankadaddiya irin ki bari na nuna miki kala ta banga mai ceton ki ba yau ko ni ko ke".

Kara shake ta Aliyah tayi tana matse ta a jikin bango dan Aliyah irin mayan matan nan ne gabadaya idon Bilki yayi jawur dan wuya Inna ce ta fito a daki zata tafi gidan da take aiki ta jiyo fadan nasu zuwa tayi tana cewa"a'a meke faruwa haka dan Allah Aliyah bari sake ta ba girman ku bane ace kuna fada".

Sakinta Aliyah tayi tana cewa "kinci darajar inna amma yau dasai kin gane kuren ki"ta fada tana nufar kofa zata fice bilki dake binta da kallon tsana tace"karya kike baki isa naci darajar wani ba nafi karfin haka"a fusace Aliyah ta juyo tace "au haka kika ce? to bari naga abinda kika fi karfi "tare ta inna tayi tana janta zuwa waje tace"dan Allah Aliyah ku bari kije ki tafi zata biya ki kudin ki"wucewa Aliya tayi batare da ta sake mgn ba inna ma ta kama haryar ta tana mmkn wanne irin kawance ne wannan kamar a film.

Alhmdllh su dady sunkai Mahmud asibiti kuma an tabbatar musu bai mutu ba, ba karamin farin ciki sukai saidai gubar tayi masa illa sosai.

Yarima tun suman dayai bai farfado ba saida safe yana tashi a firgice ya soma kwalla kiran Mahmud dakyar mai martaba ya shawo kansa ya fahimci bai mutu ba yana asibiti sai sannan ya samu nutsuwa.

Zainab dama batasan abinda ke faruwa ba dan jiya tana shiga part din mama da bata ganta ba bata kawo komai ba dama ta gaji kawai shirin bacci tayi saida safe mama take fada mata ba karamin tsora tayi ba da kuma mmkn waye zai bawa Mahmud guba a fadin masarautar nan.

Mai martaba wannan karon ya shirya tsaf akan za'a tsanan ta mugun binkice sai an gano wanda yasa aka bawa Mahmud guba da wanda yasa aka bawa Yarima guba dan idan yai sake za'a karar masa da ahli yana kallo.

Bayan wata daya komai yayi sauki musamman jikin Mahmud dan da harya daina tafiya ma daga baya ya zo yana dan takawa.

Dukkan familyn suna asibiti gurin Mahmud Yarima daya shigo yana waya dan duban Mahmud yayi yana sauke wayar ya zauna a kusa dashi yana rike hannunsa cikin murmushi yace "dan uwana yaya jikin naka yanzu kana jin alamar wani rashin dadi a jikin ka ko a'a fada min idan kanaji zan fita dakai waje a sake duba ka"? .

Dagowa Mahmud yayi yana kallon Yaha data tsaya can bakin kofa kamar mara gaskiya ya girgiza kai yana cewa "bana jin komai ina jina kamar yadda nake da dan Allah yayana kayi hakuri da irin zaman da mukai a baya nayi kuskure dana kasa gane cewa kana sona bansan rudanin da shedan ya jefa ni ba ka yafe min "ya fada hawaye na zuba a idonsa abinda kowa ya juma bai gani ba.

Rungumeshi Yarima yayi yace cewa "Mahmud nine ya kamata na baka hakuri kasantuwa ta babba na jaka a jikina tun farko amma banyi hakan ba laifi nane yanzu ne ya kamata mu gyara kuskuren mu"kallon mai martaba yayi"kakana kasa mana albarka tare da addu'ar kanmu ya hadu kenan har abada"murmushi mai martaba yayi cikin jin dadi yace"Allah ya muku albarka jikanu na Allah yasa kun dore kenan"ameen su dady suka amsa gabadaya cikin jin dadi.

kuka Yaha ta fashe da shi tana durkusawa a gaban mai martaba tace"ranka ya nice ya kamata a yiwa hukunci lokacin daya kamata ace kunsan gaskiyar komai game da abinda da nake aikatawa kuma ku yafe min ba kowa ne ya bawa Sujara guba ya sawa Yarima a cikin abinsha ba bayan ni sannan gubar da Mahmud yaci ma nice na zuba cikin abincin da za'a sauki Yarima dashi sai Mahmud yaci"juyawa tayi tana kallon mama tace dan Allah kema Amina ki yafe min zubar miki ciki danai sau biyu batare da ansan nice ba naso zubda na Yariman ma abun yaki yuwuwa sbd Allah yayi saiya rayu a duniya na sani ke ba kishiya ta bace amma na dauke ki da zafi na hana zaman auren ki yayi dadi tun a farko dan Allah ki yafe min "ta karasa maganar cikin tsananin kuka tana hade hannunta guri daya alamar neman gafara.

Tabbas mama bazata manta ba akan zubda cikin nan sun samu sabani sosai da dady har yace idan bata son haihuwa dashi ne ta fada masa sai yasan matsayin sa a gurin ta.

Kowa kamewa yayi ya kasa mgn kawai kallonta suke da kuma mmkn maganar data fada Abba kam baba wata neman shawara ko sauraro yace taje ya sake ta cikin kuka Yaha ta soma bashi hakuri hankali tashe dan tana matukar son Abba, rufe idonsa yayi yace "idan har na kirga uku na bude baki bacewa gani na ba saina dau mummunan mataki akanki Yahanasu"fara kirgawa yayi Yaha dake durkushe cikin kuka tace "dan Allah ku bashi hakuri ya mayar dani wallahi na tuba"jin yace biyu yasa dayake tasan halinsa ta mike tana fita da gudu daga room din babu wanda yasa musu baki cikin sha'aninsu dan hakan shine yafi cancanta da ita.

Mai martaba cewa yayi a sallami Mahmud kawai su tafi tare dashi gida hakan kuwa akai kuma ko kadan Mahmud bai nuna damuwa da Abba ya saki Yahanasu ba domin hakan shine daidai a gareta.

Lokacin da zasu shiga masarautar daidai nan motar Yaha ke fita alamar tayi gidan su.

Uhmm sauka lafiya.

Bayan ya kwanaki komai ya lafa Zainab ta haihu an kuma samun namiji Yarima ya saka mai sunan mahaifinta Umar ba karamar murna tayi ba Salmah itama ta haihu namiji abindai kwanin sha'awa ansawa yaron suna Fauzan.

Suna zaune a palon mama Zainab tasaka Ahmad a gaba yaci abinci yaki karshe saita karfi ta bashi mama dake zaune da mmk tace"dota wai shima baya cin abinci da kansa saidai a bashi kamar babansa"? murmushi Zainab tayi tana cewa "wallahi kullum haka nake fama ni harna gaji ma bacci nan bazaiyi ba sai ya goye shi ai shagwabar dayai miki shima ake masa kuma har ta zarce wacce yayi".

Dariya mama tayi daidai Yarima ya shigo ya sakar wa Zainab harara don yaji abin da tace zama yayi zaifara aikinsa Zainab tace" a rika sara dai ana duba bakin gatari "kallonta yayi tamai signa da ido cewa Ahmad na kallon shi wani kallo ya mata yana cewa"mah dina kina jinta fa idan banyi miki shagwaba wa zanwa a duniyar nan"? murmushi mama tai "gaskiya ne baby amma ya kamata ka daina tunda kaima yanzun anayi maka shagwaba ba taka bace saidai kace kayi da".

Hade gira yayi yana cewa "shikenan na daina naji na girma "kallonsa mama tayi "oh baby rigima wasa nake maka har yanzun a gurina kai yaro ne"murmushi yayi"yana kara hararar Zainab yace "shiyasa nake sonki mamana nasan dama bakya yimin kallon babba har yanzu ni yaro ne"shafa kansa mama tayi tace "kai yaro sosai bani da wani bayanka, yauwa baby ina son gobe zamuje kano gurin ammi ko zaka samu dama sai muje tare?"? kai Yarima ya jinjina "in sha Allahu "yana kallon Zainab yace "to sarkin hada mutum da mamansa sai aje ayi shiri tun wuri basai goben ba".

Kashe masa ido tayi tace"ai ba hadi bane gaskiya ce na fada "tana fadin haka ta mike tana daukar Umar ta wuce part dinsa dan ta shirya musu kayan tafiya. Washe gari tun wuri suka shirya Zainab murnarta da yawa dan tayi niyyar zataje makaranta taga uncle Mustapha da kuma anguwarsu gurin Fati da Inna dan bata lissafi da Bilki.
Chapter 15 · 0% Book details