← Book details Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 20

Sashe 17

Yarima Abdulmaleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaha kam dakyar Abba ya dawo da ita bayan sa bakin mai martaba sannan ya hakura suna zaune a palor mai martaba ya kalli Yarima yana cewa "Muhammad lokaci yayi daya kamata ace an daura maka dayan auren ka ko"? wani irin faduwa gaban Zainab yayi ta dago cikin tashin hankali tana kallon Yarima da shima ita ya kalla yana Murmushi dan yaga yadda zatai ganin murmushi yake kamar abin bai dame shiba ta dauke kai daga kallonsa tana hadiye abinda ya tsaya mata yake neman hanata yin kyakkyawan numfashi .

Yarima da har yanzu murmushi yake ya kalli mai martaba yana cewa "kakana mun gama mgn da dan uwana jiya ya sameni akan cewa dama tun farko shine yake sonta ni kuma inason dan uwana sosai shiyasa na bar masa ita fatan kakan zaiyi farin ciki da jin haka"? Murmushi mai martaba yayi yana kallon Mahmud yace"shikenan duka daya kuke Mahmud mai yasa tun wuri bakai mgn cewa kaine kake sonta ba da tun a wancen lokacin an hada naku auren dana Muhammad amma yanzun ma bata baci ba za'ai muku Allah yasa albarka "ameen sukace wani numfashi Zainab ta sauke tana kallon Yarima daya daga mata gira ta sakar masa harara tana mikewa tabar falon sun dade suna tattaunawa kafin kowa yayi part dinsa.

Direct Yarima part din mama ya shiga dan yafi tunanin Zainab nacan zama yayi a palor yana waya da Abeed abokinsa fitowar Zainab kenan ya dago yana kallon ta tare da aje wayar sbd wata irin kwalliya data tsara ta daukar hankali tasa doguwar riga baka mai adon farin fulawa kanta ba kwali tayi parking zama tayi a kusa dashi tana murmushi tace "yadai soulmate nayi kyau ne"? kallonta kawai yake ya kasa mgn kara matsowa tayi kusa dashi tana dora hannunta a kafadar shi ta matso da fuskarta jikin tashi sosai ganin yadda ya rude yasa ta tallafo fuskarsa tana hada bakin su.

Wai bari na rufe idona🫣 karna makance.

Saida suka dau lokaci a haka kafin ta sake shi dakyar ya saita kanshi yana zamewa ya kwanta akan cinyarta yana rufe ido ita kuma take kallonsa tsantsan kyan sa da yake dashi tare da dora yatsarta akan lips dinsa tana shafawa bude ido yayi yana kallonta yace "i love u you're the one who make me happy you're the one i want keep i love u so much"murmushi tayi cikin jin dadi tace"i love u too my soulmate "mikewa zaune yayi suna facing juna wani irin yanayi suka shiga na shauki kowa yana son gwada ma dan uwan sa irin son da yake masa hannunta ta zagaya a wuyansa shi kuma ya zagaya nasa zuwa bayanta yana shirin kissing dinta mama tace"baby maza tashi ku tafi inda kuka nufa "matsawa Zainab tayi da sauri daga jikinsa amma saiya kara riketa.

Cikin mmk mama tace "wai baby kun manta a inda kuke ne yanzu da kuma dadyn kune fa yaya zakuyi"? cikin mazewa Yarima yace "idan da shine cewa zaiyi Allah ya muku albarka "mama tace "lallai baby lamarinka yafi karfina harda ke dota kika biye masa"? Zainab data juya baya tana dariya tace" soulmate dan gyara min zip dina mama karki damu mudin abu daya ne a haka muke"ganin yadda mama ta zuba musu ido yasa suka dawo kusa da ita Zainab na cewa "sai maman mu Allah ya bar mana ke"kai mama ta girgiza tana cewa "Allah ya shirye ku".

Bayan sati biyu akai bikin Mahmud Yarima ne yayi masa wali ba karamin farin ciki su Abba sukai ba dan hatta lefe Yarima ne ya hada masa rakiya kuwa har daki ya musu nasiha sosai sannan shima ya koma gurin zezensa.

Komawar su London ta kama gobe suna gurin mai martaba ana zaune Salmah ta shigo cikin tashin hankali kowa mikewa yayi ana tambayar ta kuka tasa tana durkusa a gun tace"yanzu mamina ta kirani a waya yayan mahaifina ya rasu dazu "mai martaba yace "subhanallahi kamisu ne mai rasuwar"? kai Salmah ta daga tana cewa"eh shine"dubansu mai martaba yayi cikin damuwa yace "kowa yayi shiri babu wanda za'a bari mu tafi bauchi "amsawa sukai kowa na fita Yarima na shiga part dinshi yaga Zainab ta fito a wanka kallonta yayi yana zama yace"sauri ki shirya wani guri zamuje ina su boy"? da mmk ta kalleshi amma batai mgn saida ta shirya tace boy na part din mama "mikewa yayi suna fita bata kara tsinkewa ba sai data ga tafiyar harda su mai martaba gashi babu halin tambaya haka suka fita zuwa airport ba bata lokaci suka nufi Bauchi .

*Mrs Al'ameen Ahmad ce*🌹.
[11/25, 5:28 PM] Yusrah Musa Abubakar: *Typing*📲

*👑Yarima Abdul-malik*👑

*💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION*💫

*#YUSRAHMS ABUBAKAR*#

Dedicated to

Maman khaleel
Zarah Musa d'an Adam

🅿️1️⃣3️⃣

Lokacin da suka sauka masarautar makil suka sameta da mutane kyakkyawar tarba suka samu daga gurin sarki bayan sunyi masa ta'aziyya Salmah ta karasa ciki dasu mama domin su samu wurin zama su huta har dare Zainab na zuba ido ko zataga Ahmad amma shiru duk hankalinta ya tashi domin itafa tun a gida rabonta dashi bayan tayi masa wanka bata sake ganin sa ba iya Farouq ne a gurinta.

Salmah na cikin fada gun iyayenta bayan ta kawowa su mama komai tace bari ta shiga ciki ba'a jima ba ta dawo tare da maminta tana cewa "mami gasu ku gaisa lokacin da suka shiga gurin Addah bakya nan shiyasa nace bari na kira ki" zama tayi sukai gaisawar mutunci dasu mama inda take kallon Zainab cikin mmk tana kama da wani data sani saidai ta manta waye mai kama da irin wannan fuskar sallama ta musu tana fita zainab nason tambayar mama ina Ahmad ta kasa haka ta hakura dakyar tayi bacci.

Washe gari tun asuba wayoyi keta ringing wanda shine silar tashin dukkan su mama a bacci sukai sallah bayan gari yayi haske mama ke tambayar Zainab "dota waye yake kiran waya da asuba "? dan murmushi Zainab tayi tace"soulmate ne "kafin mama tayi mgn Hajara tace"nima wallahi Mahmud yake ta kirana"mama data dago tana kallon su tace"kai kunji yaya da rashin hankali mai zakuyi musu"? Zainab tace "kila ko son ganinmu suke kinsan tun jiya fa "da sauri mama ta kalleta ba shiri tana cewa "kwarai dota sannunki da kokari to babu inda zakuje"ji tayi daga bayansu ance"mu gamu munzo ai"ido mama ta zaro tana kallon su tace "yauga wani hauka uban me kuka zoyi nandin dama ba gurin su mai martaba zaku tafi ba mema ya biyo daku tanan din"? da hannu Mahmud ya nuna mata Hajara yana cewa minti daya kawai shaf shaf "mikewa mama tayi tana nuna musu kofar fita tace"maza kubi nan kafin na kira muku Ibrahim "dan hade rai Yarima yayi yana kallon Zainab alamar minti daya ta girgiza masa kai tana nuna mama kwafa yayi yana jan hannun Mahmud yace"zo muje kyale su akwai gaba"mama tace "yauwa kufi ruwa gudu "suna fita mama tace "kuma saura naji kunje saimun koma gida ku rabu dasu "dariya Zainab tayi tace "da aiki suda zasu tafi gobe mukwa sai anyi bakwai "mama dake kokarin kiran ammi tace "ko dubu zamuyi haka zasu hakura".

Ranar da akayi uku gabadaya ana tare guri guda a palor harda su mai martaba domin tafiya zasuyi addu'a akeyi kowa na amsawa da ameen bayan an shafa aka sake gaisawa da ta'aziyya sai sannan Zainab taga Ahmad kwana uku rabonta dashi mama na kallonta harda sauke ajiyan zuciya kamar zatai mata dariya zeey masoyan yaya.

Addah ce tace"amma dai bayau zaku tafi ba? ku bari sai gobe dan Allah "Salmah tace"eh yau zasu tafi gabadaya domin ba'a bar kowa acan ba sai wakilai "Farouq daya hango Ahmad ya fara kokawar kwacewa a hannun Zainab ya tafi gurinsa ita kuma taki sakinsa kuka ya fara mama tace"dota ki barshi ya je mana ba gurin dadynsa zaijeba"? shiru Zainab tayi Addah ta mike tana cewa "da alama wannan jikar tawa akwai kunya kodai fabulatana c______cikin firgici Addah ta kasa karasa maganar tana kallon Zainab da mmk tace "ranka ya dade kalli wannan yarinyar "ba moddibo ba kowa na palon Zainab ya zubawa ido harda su mai martaba dansu fahimci abinda yake faruwa me Addah ke nufi.

Mikewa moddibo yayi yana Karasowa gurin da Zainab take zaune saida ya kare mata kallo ya juya inda Addah take yana cewa "alhmdllh abinda na dade ina nema abinda kullum nake alfahari dashi nake mafarki da kwadayin gamuwa dashi zinaren da a kowacce rana yake sheki a idona abinda ya kasance shine nutsuwar zuciyata kuma farin ciki na ya iso gareni lokacin da ban taba tunanin zan ganshi ko na sameshi ba wannan yarinyar duk inda kika fito ke jinin Umar dina ce idan har ba gizo idona kemin ba da abinda nake muradi kuma ba rudewa nayi ba tabbas ke 'yar Umar dinace "ya karasa maganar yana kallon Addah da hankalinta yayi mugun tashi ba zato taji kuka yazo mata cikin damuwa tace"koma menene kaine silar batan Umar ai da halin daya tsinci kansa a ciki mai yasa ka kasa masa hakuri ka fahimce shi tun a wancan lokacin akan laifin da baikai ya kawo ba ka iya cewa yabar maka masarauta shekara talatin kenan babu ko alamarsa yanzu da yarsa tazo maka har gida ai ka nemeshi "ta karasa maganar dakyar sbd yadda muryarta ke shakewa zainab kallonsu kawai take inda taji zuciyarta ta girgiza lokacin da Addah ta ambaci Umar shine ya tsorata ta.

Moddibo hakuri kawai yake bawa Addah don yasan bai kyauta ba mai martaba dake kallon su dukda maganar ta cikin gida ce amma tunda abin ya hado da Zainab dole ne suma suyi mgn dan haka yace suna neman karin bayani shiru palon yayi ana sauraron moddibo ganin kowa shi yake kallo yasa ya sauke numfashi yana cewa "gaskiya da na rike sirrin a zuciya ta amma yanzun dole na fada kowa yaji dalilin dayasa umar yabar cikin ahlinsa nine sila shiru moddibo yayi ya kasa magana gabadaya kansa ya dau caji ji yake kamar kada ya fada amma kodan ya wanke laifinsa a gurin yarsa ya fada musu.

*Mrs Al'ameen Ahmad ce*🌹
Chapter 17 · 0% Book details