← Book details Yar Waye Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 22

Sashe 9

Yar Waye Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Xaune duka suka mom,daddy Ammar da Amrah.dukan su xaune suna fira ne suna dariya...inda Amrah ke tsokanan Ammar akan maganan hajiya,nacewa"kafitomun da wanda kakeso,ko nikuma na fitomaka da duk wacce ta mun.dariya duka suka sa,inda daddy ke cewa"auuu yanxu hajiyan tawa kuke kwaikwayon maganan ta,lallai wuya n ku tayi kauri.
Dariya suka kuma sawa wanda dai² momy zatayi mgn sai jin sallaman Afral sukayi,cike da farin ciki, suka amsamata,inda kallon su batayi ba,har ta Amrah dake kwa'da oyoooyoooo my Afral bata kalleta ba,tayi up stairs.don ranta 6ace ta dawo.
A hankali momy tace"daddy wai ya xamuyi ne hajiya kaka ta janye maganan nan,na Afral?
Shiru daddy yayi kan daga bisani yace"ok kije ki lallasota,xamuyi maganan daga baya.
Cikin xaro ido momy tace"wane ni😳 kana sane yau har dani take fushinta don ko naje baxata lallasumun ba,sai dai Ammar don dama shi ya kunna wutan ae.
Amrah ne tace"tohhh ya Ammar don allah kaje ka lallasota mana. Ta fa'da kaman xatayi kuka,don gaba 'daya batajin da'din halin da Afral 'din take ciki.
Murmushi yayi ganin momy na hararanshi,don acewanta duk shi yaja masu wannan rigiman na Afral.
A hankali ya mi'ke ha'di da shiga room 'din Afral.wanda take kwance tayi rub da ciki akan gadon ta.idon nan nata ban fitan hawaye ba'abun sa sikeyi.zama Ammar yayi a gyafen ta ha'di da kiran sunan ta.
Jiyo muryan Ammar 'din yasata bu'de idon ta a hankali.
Ae ha'da idon da sukayi nan ta fashe mai da kuka.lallashin ta ya hau yi hadi da bata ha'kurin tun da bataso baxa'ayi mata dole ba..ganin irin kukan da takeyi ne yasa shi cewa"plz Afral kiyi shiru don allah komai yake damun ki ne.
Da kyar tasamu daman daina kukan,wanda ta hau cewa"ya Ammar ya xanyi da rayuwa ta ne? Na tsani duniyan nan yah Ammar,ni dama xan mutu in huta da komai wlh.
Cikin 'dan 6acin rai Ammar yace'kar na 'kara jin wannan maganan daga bakin ki Afral.mai yasa kikace hakan?
Goge hawaye tayi ha"di da fara cewa"da fari na taso cikin gata ban san 'kunci ba,balle da muwa ko talauci,inason momy na fiye da yanda nakeson kaina,amma na dauki komai a kaddaran cewa*momy ba mahaifiyata va ne,tohhh mai yasa hajiya kaka keson rabani da momy na.ni abanni tare da momy na muyi rayuwan mu tare kawai ya Ammar.ta fa'di cikin matsanan cin kuka,mai cike da damuwa,ha'di da tsantsan yarinta,wanda taba ma Ammar mugun tausayi,don yasan still she is smalll girl.
Cike da tausayinta Ammar yace"tohhh kina nufin ba kyason a rabaku da momy ne?
Cikin sauri Afral tace*ehhhh ya Ammar.
Murmushi yayi ha'di da cewa"ok tohhh xakiyi abu 'daya indai kinason kixauna tare da momyn ki...
Cikin sauri Afral tace " mai ye ya Ammar?
Kafeta da ido yayi na en da'ki'ku kan yace"Afral i really love you,zaki aure ni?
Cikin matsanan cin ru'du Afral ta fixge hannun ta daga nashi,sannan tafara nuna shi da yatsa,ya Ammar nifah 'kanwanka ce.wanda momy koda baitah ta haifeni ba, ae ta shayarda ni,kuma a musulunci ba aure tsakanin mu,noo Afral kin manta cewa " momy bata shayar dake ba,ko kin manta ta lokacin haihuwarku ne ta kamu da breast cansa.wanda likitoci sukace "karda ta shayarda ke ko sau " daya..cike da rashin sanin maganan shi Afral tace"no ya Ammar plz kabar wannan maganan wanda ni banta6a sani ba,just forget about the matter ya Ammar,banason jin wannan magana don allah.
A sanyaye Ammar yace"shikenan Afral,kisani xanbar wannan maganan amma bawai na barshi bane har abada,cox inso naga nayi taking responsisibility naki,inga na inganta rayuwarki kaman yanda kullum momy take burin gani,inga kinsamu miji nagari,wanda xai kulamun dake,kamar yanda Amrah tasamu umar wanda bani da haufi akanshi har bayan rai nasan xai kulamun da itah.tohhhh kefah? Nace kefah Afral?plz Afral ki amince in aure ki,momy tayi alfahari dake,kuma ki kasance 'ya wurin ta har abada...idon shi ne ya rufe wanda da ya bude su sai da Afral ta tsorata ganin irin yanda suka koma daga fari xuwa jahhh...
Da kyar ya bude baki ha'di da cewa*na barki Afral kije kiyi tunani plz...
Yana kaiwa nan ya mi'ke ha'di da barin dakin ya rufo mata 'kofah.da fitanshi Afral tasa kuka ha'di da fadawa kan gadonta ta kwanta,kuka take sosae ha'di da cewa" yah xatayi yau?
Dai² Amrah na shigowa 'dakin don koda tashiga "dakin ta,takasa sukunin ganin halin da Afral ke ci.

Da sauri tayo wajenta ha'di da 'dago tace" Afarl mai yasame ki ? Don allah ki smdaina kukan nan manah,kifadamun.
Dago rinannun idon ta tayi ha'di da cewa " yaya na,kumah mijina??? Nan takuma rushewa da kuka,wanda cike da rashin fahimran ta Amrah tace"kaman yah,bangane ba Afral.
Ciki n matsanan cin kuka ta hau cewa"yahhh Ammar...ban da nanata sunan ba abunda takeyi.
Wanda nan take Amrah ta tuno maganan ta na ba farko,yayana...kumah mijina..wani ihu Amrah tasa ha'di da 'dago Afral tace" don allah Afral da gaske,cike da matsannan cin farin ciki take maganan,wanda yasa Afral sakin baki tana kallon ta cike da mamakin farin cikin nata.
Dariya ta hauyi ha'di da 'daga hannu tana mawa Allah gidiya,kai Afral muyi ma allah godiya.wayyyooo ni allah ya nunamun ranan,don ma naki xamu farayi wlh,naga bikin yaya na.

A sanyaye Afral tace " kin manta cewa a musulunci ba aure tsakani na da ya Ammar! Momy fah ta shayarda ni.
Cike da sanyin jiki Amrah tace" haka ne,Afral amma ae ya Ammar yafimu sani,kuma tun da yace" yana sonki,tohh yana da hujjansa ne...
Don haka kawai kishare wannan xancen.

Murmushi Afral tayi don tasan wannan lamarin ba mai yuwuba ce,nan tanisa ha'di da cewa" ae yace wai ma momy na ba itace ta shayarda ni,kiji fahh wani bahagon xance.

Shiru Amrah tayi na kusan minti 'daya sannan tace"hmmm toh 'kila da gaskiyansa,don kinga yafimu sanin komai,amma bari naje na tambayi momy ta cikin siyasa yanda baxata fahimci xancen ba.
Tohhhh shikenan.
Afral tace hadi da bin Amrah da kallo.
Murmushi Amrah tayi ha'di da cewa " kai allah kanuna mana lokacin nan,ya Ammar da Afral,hmmn
Saurin rufe ido Afral tayi wanda wannan d first time da ta ta6a jin kunyan wani abu a rayuwan ta na duniya.
Dariya Amrah takeyi har ta bar dakin ta rufo mata 'kofah...

A hankali take sakkowa da stairs inda a 'kasa tana shirin nufan part 'din momy suka ci karo da Ammar yana fitowa daga nashi 6arayin,abunka da mara gaskiya nan take Amrah ta fara sinne kai 'kasa tana dariya.
Ae nan take ya gano ta,ganin ya nufota yasa ta nufan 6arayin momy da gudu,ae shima nan yavi bayan ta,wanda tako biyu yayi ya kamota.
Dariya tasa ha'di da cewa"plz ya Ammar ka sakeni,wlh ni banma komai ba fahh.

Murmushi yayi ha'di da cewa"ae bance kinmun komae ba,amma ya Afral ta sauka ta daina kukan?.maganan yayimata direct don yasan tasan komai na avun da ke tsakanin sa da Afral 'din.
Murmushi tayi sannan tace"baka da matsala ya Ammar,amma matsala 'daya shine momy fah itace ta raini Afral kuma ta shayarda itah,tohh ta yaya xakuyi aure don ko a musulunci ba aure a tsakanin ku.

Murmushi Ammar yayi sannan yace"na fa'da mata ba momy ne ta shayarda ita ba,tun kafin momy ta haifeki Amrah ta kamu da breast cansa,wanda koda ta haihu sai likitocin suka ce kar tashayarda 'yan da ta haifah,kuma haka akayi samm momy bata shayer da Afral ba,don ni da umar muka raini Afral ta hanyan bata madara da sauran avuncin su na jarirai,har tayi wayo.
Inda tana da shekara daya daddy yace"xasu tafi abroad don anan momy da itah xasufi samun kulawan likitoci.wanda haka suka koma America da xama,kuma tun da suka tafi basu dawo ba sai shekaran nan da ta wuce.
Don haka plz Amrah don mind your self about that matter,just forget kawai kisan yanda xakisa Afral ta amince don allah my little...ya fa'di ha'di da kashe mata ido 'daya.

Dariya Amrah tayi ha'di dacewa"ai ya Ammar ka kwantar da hankalinka,yanxu dai karmu fitar da wannan maganan har sai ranan da hajiya kaka tace" tasa maku date line.
Dariya Ammar yayi tuno da hajiya kakan.wanda a ranshi yace"tsuhuwan mata amma sai shegen fitina.bakin ae xai mutu ne.
Hmmm ya Ammar bari naje nakira Ammara don nayi mata wannan albishir 'din.
Dariya Ammar yayi ha'di dacewa" ahhhh ba tana kasansu ba?
Ehhh ae sun dawo daga mallie,kasan buxayen mallie ne.
Ok yace"hadi da barin falon.cike da murna da farin ciki Amrah ta haura sama don tayi ma Afral Albishir 'din itahhh ta yaya Ammar ne....
Inda shikuma da fitan shi wayansa ta hau ruri,dubawa yayi ha'di da kallon sunan mai kiran,wani dogon tsaki yajahhh gani sunan lubnahhhh akan screen 'din wayan.

#share and
Comment...

Maman teddy ce...
08081202932
[12/29, 9:55 AM] mmn tedy: Typing...

MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION.

*'YAR WAYE???*
Pure love and symphaty story📒📚

Story and written by: Ayshatou maman teddy.

Episode 40 - 41

________________________________

Tunda Ammar yaga mai kiran ya mai da wayan a aljihu batare da ya 'dauka ba,ya nufi motan sa ha'di da nufan gidan daddyn farouq.

Cike da murna Amrah ta nufi 'dakin Afral,inda ta barta ta sameta,ae nan da gudu da nufeta ha'di da fa'dawa jikinta tana dariya.
"Dagota Afral tayi sannan tace" mai ya faru Amrah mai yace maki? Kin gan shine?
Dagowa Amrah tayi ha'di dacewa " Kwarae da gaske Amarya a wajen ya Ammar.nan ta kuma kwashewa da dariya, ha'di da kwanciya kan filo.
Afral da bata gane inda Amrah ta dosa ba tace"pls Amrah ki tashi kimun bayani yanda xan gane,ni ban fahimce ki ba.
A hankali Amrah ta mi'ke ha'di da korama Afral duk yanda sukayi da Ammar,wanda daga 'karshe ta 'dauki waya ha'di da kiran Ammarah.

Binta da ido Afral tayi ha'di da tunanin abubuwa da yawa a zuciyanta.
Chapter 9 · 0% Book details