← Book details Yar Waye Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 22

Sashe 12

Yar Waye Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya ne tace"ehhh haka nake nufi,gomma ma ku tattara ku 'kara gaba,don nasan ba don allah kukaxo gidana ba.
Tana fadin haka ta mi'ke ha'di da nufah 'dakin ta.wanda cikin hanxari Ammar yayi saman benen,a tunanin shi a bu'de 'kofan take.amma cikin rashin sa'a sai yajita a garma'ke...taski ya jahhh ha'di da dawowa ya sanarma su umar da suke xaune,don maganan hajiya ba 'karamun 6ata mai rai yayi ba.

Nan Ammar yake sanar masu komae,wanda dariya Afreed yayi ha'di da cewa",kunga banu yau.ae hajiyan tasan halinku ne shiyasa.
Saurin kallon shi umar yayi ha'di da cewa"kaman yahhh mai kake nufi?

Dariya Afreed yayi ha'di da cewa" tasan ku da shegen son mata,musamman kai umar da shegen jaraba.
Kallon shi umar yayi cike da 6acin rai yace" kai dallah karka kawo mana maganan banxa anan. Wato xanso??? Amrahn ne xanyi wani abu da itah? Dududu nawa take??

Dariya sosae Afreed yayi ha'di dacewa"kaman da gaske, dama wani ba kai ba.kallon shi Ammar yayi wanda sae a lokacin yace" tohhh 'kila in ankae mai itahhh ba'abun da xaiyi da itahh sae shangiyan da yasa bayi in yana bu'kata....

Dariya Afreed yayi ha'di da cewa"hmmm mutum yasha bear wlh asirin shi ya tonu.
Kallon su umar bai yiba inda ya mi'ke ha'di da basu waje...
Dariya duka sukasa inda Ammar yace"kofah yanxu ka bincika a bu'kace yake,don gomma kowa da shi ae,donmu namu ya fitohh sarari...

Haka suka dinga shakiyan cinsu,inda a ranan haka suka dinga damun hajiya da magiya, amma samm ta'ki barinsu ganin su Amrahn.

Ganin haka yasa Ammar da Afreed tattara yanasu² ha'di da barin gidan,suka nufi gidan su daddy.
Inda umar yakasa binsu don shi bai da sukuni kwata².burin shi kawae yaga Amrah n shi,shi ne ka'dai hankalinsa zai kwanta...a haka sae da ya kwana uku a gidan amma wul'kawan Amrah bai gani balle maganan ta.
Inda wata rana yana xaune sai ga hajiya kaka ta sauko daga saman,bin ta yayi da kallo ha'di da keys din dake hannun ta,har tashige dakin ta,da alama bacci xatayi.

'Karamun tsaki yajahhh wanda a ranshi yace"wae ace yau biki saura kwana 3 amma an hanaka sa'kat da matanka.wannan wani irin bala'i ne?
A ranshi ne yace" ae inkin san wata bakisan wata ba hajiya, bari ki gani.

Mi'kewa yayi ha'di da bun bayan hajiya kaka inda tun daga bakin 'kofah yakejin munsharinta...a hankali kuma cike da san'da ya nufeta,inda yaga keys 'din ya nufahh ha'di da dauka ya fitoohhh...

Cike da axama ya haura sama ha'di da fara gorgoda keys 'din,wanda cikin sa'a ya bu'de kofan...
Shiga falon yayi ha'di da rufewa da key,nan yakuma nufan bedroom din ta,inda su Amrah ke xaune suna firahhh,sallaman shi yasa cike da mamaki suka kalleshi,inda Afral da gudu ta nufeshi inda yaware mata hannu ta fa'da jikin shi...nan ya mai da kallonshi ga Amrah wanda ta cigaba da kallonsu,murmushi yayi mata wanda ya bayyana wushiryan shi,ha'di da fito da kwarjinin shi,alama yayi mata da taxo,wanda a hankali ta mi'ke ha'di da 'karasowa gareshi,tsayawa tayi batare da tayi hugging 'din shi ba,cike da mamaki yake kallonta don yasa dah bahaka take mai ba,don har fa'da mayake mata akan hakan.
Murmushi yakumayi mata ha'di da jawota gare shi.a hankali ta yayi hugging 'din ta,inda Afral da sauri ta bar 'dakin don a xuciyanta cewa take" hmm masoyan asali,bari na barku yahh umar kabama flawan ka ruwa yanda yaka mata.

'Kara manna ta da jikin shi yayi, inda yake sha'kan wani irin 'kamshin jikin ta,wanda lokaci guda yafara sakar mae da kasalahhh...

Niko maman teddy zarah ido nake ina addu'an allah ya kawo hajiya kaka,gudun kar ayi aika²...😆😜

Tun yana sauke numfashi a hankali yakoma saukarwa da sauri da sauri,inda lokaci guda yafara bin Amrah da kisss...ganin haka cikin 'dan ru'du Amrah tafara 'ko'karin raba jikinta dana hamman nata.
Wani ri'ko yayi mata wanda motsi kwakwkwara ta kasa yi.cigaba da kissing 'din ta yake,inda cikin rawar murya ta haucewa"hamma don allh kabari,nine fahh,ganin idon shi arufe da alama ma bajin ta ya cika ba yasata fara saka mai kuka...
Bugun 'kofan hajiya kaka ne ya dawo dashi hayyacin shi,inda take ta xage².itakuma Afral dake falo take mai da mata da mgn cike da tsiwa na kaka da jikahhh....

A hankali ya saketa inda da sauri tafara goge hawayen kan fuskan ta,hankchief ya ciro da ga aljihun shi yafara gige mata hawayen,dai² Afral na shigowa,batare da damuwan ganin su haka ba tace" yahh umar hajiya kaka fahhh.
Kallonta yayi ha'di da bata keys jeki vu'de mata.
Kar'ba tayi ha'di da nufan 'kofahhh.
A hankali ya sunkuyo dai² kunnen ta yace" my Amrah kina bu'katan wani abu ne,don yau xan tafi gidan daddy, tun da hajiya ta hanani ganin ki.a hankali ta bu'de idon ta ha'di da waresu akan fuskan shi,kwarjininsa ne hadi da kunyanshi ya saukan mata,don haka da sauri ta sun kuyar da kai 'kasa,don takasa ha'da ido dashi.
Murmushi yayi mata sannan yace"kin ganki kuwa Amrahn hamma? Kin 'kara kyau sosae kum...

Rufemun baki munafiki,maxa fita kabani waje,kar in 'kara ganin ka anan,na fa'da maka.
Dariya umar yayi wanda ya'kara mawa fuskan shi kyau da kwarjini sannan yace"kwantar da hankali n ki hajiya kaka, ae yau xan bar maki gidan,tunda naga Amrah ae shikenan basai kin koreni ba.
Tsaki hajiya kaka tayi" ha'di da Amsan mukulin hannun Afral tana mai 'Kara jan tsaki...

Haka umar ya bar 'dakin fuskan shi 'dauke da murmushi, don yau zuciyan shi wani sanyi take mai,tunda yaga Amrahn nasa...
Haka hajiya kaka ta raka shi har 'kasa tana bala'i hadi da cewa"zai kawo mata rashin kunyahhh,a haka xa'a kawo mata wankan...

Gaskiya Comment 'din ku na 'kasa,don haka mu 'ko'karta muringa yi plzzz,yanda najii Comment 'dinku haka xan rin'ka tayping...

#share and
Comment.

Maman teddy ce...
[12/29, 9:55 AM] mmn tedy: Typing...

MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION...

*'YAR WAYE???*

story and written by: Ayshatou maman teddy.

Episode 46 - 47

_________________________________

Haka dai su Amrah suka bie hajiya kaka da ido har ta fita...
Xama Afral tayi ha'di da kallon Amrah, wanda ta fa'da duniyan tunanin abun da hamman nata yayi mata.a ranta ko cewa tayi " gskiya hamma na ya chanja,ko dae ya manta ni ce Amrahn sa.
Dafata Afral tayi ha'di da cewa"hmm masoya kenan,ana nan ana tunanin ya umar ko? Kar kidamu kwana nawa ne yarage a kaiki,ku huta da fitinan hajiya kaka... Kinga kwaci soyayyan ku har ku gaji...
Duka Amrah ta kaimata wanda Afral tayi saurin kaucewa tana mata dariya...

Hajiya kaka kuwa da saukanta,ta yada zango a falon ta ha'di da cigaba da mawa umar fa'da,wanda kallonta bai yiba,ya wuce 'dakin shi ha'di da shirye² n nufan gidan daddy,don tun dayaga Amrah komae na shi taji ya natsu sosae...

Hajiya kaka ne tabi shi da ido,ganin ya fitoh da alama barin gidan xaiyi da gaske.
Bu'dan bakinta cewa"tayi afff ae dama nasani,tohh tun da kwanyan ka ya fa'da,kar ka kara dawo mun gida.
Murmushi yayi batare da ya cemata komai ba,ya fice ya barmata gidan.

Haka taketa masifah wanda a ranta tace" sae ta ha'du da su Amrahn da har suka tsaya suka saurareshi...

Tun ana sauran kwana biyu su teemah suka xohhh gidan hajiya kaka, inda suke ta ro'kon ta akan ta barsu suyi event din da suka shirya yi, amma samm haj kaka ta'ki amin cewa masu.haka suka ha'kura wanda sae ana gobe daurin aure ta amince akan suyi priders shower.
Akan suyi a cikin gidan,inda suka nufi garden na gidan...'kawayen su da yawa sun halirta wannan brider showern,inda su Ammar basu san anyi,don da sae sun xohhh koda kaka xata tsine masu ne.
Anci ansha,kuma anyi rawa,inda Amrah tayi rawa iyahh rawa,don kowa a wurin dan kallo ya xama mata...don itah kanta Afral bawani rawa takeyi ba,batta dae da iyahh soyayya, dakuma ba so mahimmanci...amma rawa takan taka,amma bawata gwana ce ba.

Basu tashi ba sae wuraren magriba,inda hajiya kaka, tafara yohhh masu kirahhh,don haka duka suka tattara sukayi part din hajiya kaka.
Daran ranan samm basuyi macci ba,inda suke firansu tsawon dare,har kusan asuba,sannan suka kwanta...

A rananr Asabar ce,wanda yake shekara ta dubu biyu da Ashirin,inda dubbab mutane,manyan gommnati,'yan kasuwa,'yan siya duka suka shaida 'daurin auren Umar farouq Abdullah shida Amrah muh'd,sai kuma Afreed tare da Ammarahh salis,tareda Ammar aka daura da Afral. Duban mutane sun shaida kuma sunyi masu fatan xama lafiya.
Wanda hajiya kaka samm ta hana 'yan jikokin nata sunufi gidan iyayen nasu,inda tace"sae dai suje gidan iyayen nasu in xa'akaesu gidan maxajennasu...

Inda su abba suka ware masu wani tan'kamemen estate,dukansu,don tare xasu xauna a estate 'dayah...
Sunan estate daya ne,amma tafiyan da xakayi kafin kaje na wani estate din sai ka axa kabar gidan ne gaba 'daya saboda nisahn su...
Haka kowanne a ka cika mata daki da kayahhh.don gaba daya kayan da aka xuba masu bana 'kasan bane.kuma komae iri 'daya akayi masu.su ukun,don ko da baban Ammarah yace" xai mata kayan daki,wani gidan Afreed aka warw masu na partcout inda yake aeki acan.wanda gidane ya shiryu wanda da kaganshi kace aljannan duniya ne...don abbah yayi ma Ammarah kaya nagani na fa'da..niko nace tohhhh 'yar daya tilloooo..

Daddy ne da kansu suka kayi mawa su Ammarah komae iri daya na estate din.don ko su Ammarah basu sani ba samm.

Umar farouq na hago cikin dumbin mutane yana ratsawa da kyar,saboda yawansu.
Sanye yake cikin fararen shadda,wanda akai mae babban riga,mai adon dark blue disign.hulan kansa blue,kwarjinin sa,kamalansa duka sun bayyana, inda wurin gabadaya jami'an tsaro sun cika shi,sojoji kuwa ba"a magana.don tuni nigeria ta dauka en jarida,masu aikin gidan tv.kowa nason dauka don ya watsahhh...kafin a wanni tuni daurin aurensu ya xagaya koinah,na nijeria,inda har da 'kasashen waje.don 'kawayen Afral sae kira suka suna tayata murna.
Gidan tv.kuwa ba'abun da suka yadawa inba cewa suke the cople of the year..
Haka xakaji ana kwadawa.
Chapter 12 · 0% Book details