← Book details Yar Waye Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 22

Sashe 10

Yar Waye Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bangaren Ammarah kuwa,ihu tasa ha'di da nuna matsanancin farin cikin ta dataji maganan Ammar da Afral 'din inda take cewa"yanxu xata kirah su teemah don ta shaida masu,su shiraya jiran biki nan da wata biyu...
Ihun da Ammarah keyi yasa umman ta da Anty zinah da suke gyafe tambayanta lafiya? Wannan murnan da farin cikin na mene?
Dariya Ammarah tayi ha'di da shaida masu komai nasa ranan Amrah da Afral 'din.cike da farin ciki umman Ammarah da Anty zinah sukayi masu fatan alkhairi...inda umman Ammarah tace"yakamata suyi ma mom zaituna murna,saranan 'ya'ya nasu haka...

Anyi haka da kwana biyu su daddy sukaje gidan su Ammarah ha'di da neman aurenta,don Afreed tuni ya fa'da masu,inda hajiya kaka tace"su daddy suje,don yanzu xaman jiran na Ammar da Afral sukeyi...
Tohhh Alhamdullilah xamuce don Abban Ammarah sun yi na'am da xancen su daddyn,inda suka tsaida bikin duka rana 'daya,watohh watanni biyu masu xuwa.

Haka rayuwansu ta cigaba cikin jin da'di da nisha'di...inda mom Rayhana ke mamakin yanda Afral 'din tasaki jiki haka.sai dai yanda Ammar ya sakine shima ana walwala da shi kaman bakomai yafi damunta,don tasan shi sarai irin halin nasa...yanu na kaman yamanta da abu amma kullum inka bincike zuciyanshi xakaga dashi yake kwana yake tashi.

A haka har ranan da hajiya kaka tasa ya xagayo.inda tace" duka su ha'du a gidan nata,don ta dawo Abujan dirshan.inda jikokin nata ke rashin marhaban da dawowan nata.
Xaune kamar kullum hajiya kaka ce zaune" ta ha'da rai,inda kowa ke aukin gaisheta.
A ciki² take amsawa don yau cike take da jikokin nata.
Maganan ta fara cike da muryan tsufah.
Kaman yanda kuka sani,nasa maku ranan nan,don inji ta bakin ku Ammar da Afreed wanda kukeso xaku aurah.tohh alhmdllh naji ta bakin Afreed kuma har munyi mgn da iyayen yarinyan wato nusaibatul Ammarah, kuma mun tsaida bikin rana 'daya da taku ne umar. Don haka saura kai Ammar inason jin ta bakin ka yanxu.kasamu wacce kakeson ne ko nasamarma duk wanda tayi mun.
Murmushi Ammar yayi wanda xuciyan Afral banda fa'duwa ba'abun da yakeyi.
Habawa hajiya kaka mai yayi xafi haka??? Ae ni tuni na fitar da matan da xan aura,yanxu kawai lokacin da xa'asa nake xaman jirah.
Cike da mamaki kowa yake kallon shi,inda umar da Afreed kecewa a zuciyan su,tohhh badai lubnah ba...
Hajiya kaka ne ta katse shi cike da sakin rai jin yace"yasamu wanda xai aura,nan tace tohh muna jinka,a'inah take ne?
Dariya Afreed yayi ha'di da cewa"da wuri haka hajiya?
Mom Rayhana ne cike da 'dan daka mai tsawa tace"kae bamuson shashanci,komu saoinka ne?
Murmushi yayi ha'di da shafa sajenshi,yace" a'a momy.
Tohhh munajin ka a'inah take yarinyan?
Cike da murmushi yace"momy 'yar ki nake so ae.da sauri duka suka kalleshi,cikin rashin fahimtan wacce 'yar ta ta.
Momy ne tace"ban gane 'ya ta ba,wacce 'yar tawa?
Dariya yayi ha'di da cewa' Afral hajiya kaka nakeso.
Bude baki hajiya kaka tayi wanda takasa cewa"uffun don Ammar din anata ganin yanaso yamaida ta abokinyan wasan ta ne.
Cike da mamaki momy tace"kar ka kawo mana xancen banxa anan.Afral kuma? afral 'din da take 'kanwan ka? Ko kaman ta ne in tuna maka Ammar.
Hajiya kaka ne tace"gaskiya ne Rayhana inba shashanci ba yaxa ae kace" Afral kakeso,wanda ka raina da hannun ka,wannan ae sakarci ne.
A hankali Ammar yace" tohhh ae ba momy ta haifeta ba,kuma ba itah ce ta shayar da itah ba hajiya kaka, don allah kubari in auri Afral,wlh ni ne ka'dae xan kula da itah kamar yanda kukeso fah.
Su daddy ne da tun da yake maganan suka kasa cewa uffunn,inda su umar ke sharara dariya don axabcen su yau an kashe bakin hajiya kaka.inda Amrah da Afral duka du'kar da kai sukayi,a zuciyansu suna addu"an allah yasa hajiya kaka ta amince masu da wannan babban maganan.
Daddyn farouq ne yace"gaskiya naji da'din wannan maganan taka Ammar, kuma allah yayimaka Albarka,kaman yanda kace kai ne kadai xaka kulamana da Afral yanda mukeso tabbas haka ne.don haka Alh muhammad yaka gani? wannan maganan abun dubawa ce.
Daddy ne yace"gsky ni kai na yayimun da'di wannan maganan, amma dai mufara jin ta bakin hajiya tukunnah.

Waigawa duka sukayi ha'di da sauraron jin mai hajiya xata ce...
Wanda cike da murna da farin ciki hajiya ta dingi sama Ammar albarka,don acewan ta samm ta manta Rayhana ba'itah ce ta shayarda Afral ba.
Murna gaba 'daya falon a keyi,inda hajiyan tace"toh ae yaka mata muji na bakin Afral 'din ko???
Nan ummu maryam tace"ae hajiya kyaleta kawai basai mun bi nata ba.
Hajiya ne tace"a'a muji dae na bakin nata xaifi,kafin muje dangin mahaifin ta neman auren.
Afral mai kika gani kina son yayan naki kuwa,xaki aureshi ki xauna da shi da wannan fitinann halin nasa?
Sunkuyar da kai Afral tayi ha'di da jin kunyan maganan hajiyan,wanda inda dane,ita dakanta Afral din xata tsiwace ta.amma yau takasa mgn saboda kunyah.
Wasa da yatsunta ta hauyi inda suna ha'da ido da Amrah tasaki murmushi, don Amrah n ma dariya take mata.dai² kunnenta Amrah tace" ooo" yau wace rana su Afral ansan kunya,ashe dama kin san kunya Afral?
Kauda kai Afral tayi tana murmushi. Inda daddyn farouq yace"ae hajiya basae ta fa"da ba,don ko yanxu mun samu tabbaci,sai dai muce kawai allah ya nunamana lokaci.
Nan gaba 'daya aka ha'da baki tare da cewa"Ameen ya Allah.
Haka suka dinga fira a falon inda Afral da Amrah sukayi bedroom 'din hajiya kaka.
Ba kunya su Afreed suka mi'ke xasu bi bayansu,nan ummu maryam ta ce"kufita kubamu wuri.
Mom zaituna kuwa cewa"tayi bassu sukawo mana rashin kunya mana.
Sosa suman kansu suka hau yi ha'di da barin falon hajiya kakan.
Haka su daddy keta kisima yanda bikin 'ya'yan nasu xai kasance,cike da walwala da jin da'din rayuwan nasu..

________________________________

A washe gari akayo kiran su hamma umar,Afreed da Ammar,inda ko samun su Amrah basuyi ba.don fitan a suba sukayi,abun ka da sojoji...Ammar sai da yayo kiran wayan Afral ko sun tashi,amma nan yaji ta a kashe,don haka sukayi ma su daddy da momy sallama ha'di da nufah barrack wanda daga can xasu wuce farance...

Koda su Amrah suka tashi da safe,suna break ne momy ke shaida masu tafiyan su umar.inda duka sukayi masu fatan dawowa lafiya...a haka har suka gama break fast,inda momy da daddy sukayi masu sae sun dawo,don yau duka suna da fita aeki.
Xama sukayi suna ta firansu tare,don yanzu soyayya ne sosae Amrah da Afral ke nuna mawa junan su.

Wanda kwanci tashi ba wuya a wurin allah,yau gashi satin su umar kusan biyu da tafiya.inda bai ta6a kiran Amrah ba,tun da yakira ta ranan da suka tafi...inda Afral kullum ana manne da waya ana xuba soyayya.don wata xubin har mamaki Amrah keyi,kaman da ba yayan ta ba ne hmmm.
Yau kwana uku kenan basuyi waya da Afreed ba,inda Afral ke tayima Amrah magiya akan in hamma umar ya kira ta ta tambayeshi lafiyan Ammar 'din.
Da tohh Amrah ta bita,a zuciyanta kuwa cewa"take hmm baki san ni ko waya da shi bamayi ba,ko kuma ya rika yin mun mgn yana wani miskilanci²,hmmm ni inah xan iyah wannan?gaskiya naga takaina,hamma umar fah??? Nima nayi da gangar wlh.
Haka suka shirya ha'di da nufahn wani shoping mall,inda suke ta siyayyan kayan su ta kyale²n mu na mata....

Lubnah ce wanda tun daga shigowansu ta hangosu ha'di da gane su,don ko batasan Amrah ba,toh tasan Afral farin sani kuwa.
Cire shadow space 'din ta tayi,wanda ya mamaye mata rabin fuska.cike da takun ta na 'kosassun mata ta nufesu....don yanxu tasan komai na maganan Afral da Ammar 'din.

Kehhhhh...sunan da takirah Afral kenan da shi.
"Afral wanda tayi kaman batajita ba,ta cigaba da duban kayan da xata siya abun ta,haka ma Amrah...
'Kara nanata kehhhh lubnah tayi.inda cike da masifah ha'di da tsiwa Afral ta 'dago ha'di da ajiye wani neckless dake hannun ta xuwa ma'ajin shi.....

Banyi maku posting da wuri ba,pls kuyi ha'kuri bana da chaji ne,but manage with dis...

#share and
Comment...

Maman teddy ce....
[12/29, 9:55 AM] mmn tedy: Typing...

MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION.

'YAR WAYE???
Pure love and symphaty story📒📚

Story and written by Ayshatou maman teddy...

Episode 42 - 43

________________________________

Da ajiyewan ta ta juyo ha'di da mawa lubnah kallon banxah,wanda cike da mamaki ha'di da jin haushi kuma da tsanar Afral 'din lubnah tace" kehhh ni sa'ar wasan ki ne da kikemun wannan iri kallon???
Tohh in fa'da maki ko Ammar bai isheni kallo ba,balle ke.
Saurin katse ta Afral tayi ha'di da cewa" tohhh naji hajiyata sai kuma me ne? Naga ni ba Ammar bane ae,inkuma kinga nayi maki kama da Ammar to go ahead...
Juyawa tayi ha'di da cigaba da dube² n ta,inda cike dajin haushi da kuma mamakin wula'kancin da Afral 'din tayi mata tace"kehhh bari nagaya maki don bani da lokacin 6ata tashi akanki,wani xance naji,don kuwa sai dai ince xance, kokuma ta tsuniya,wanda take taxo muji ta,jinayi wae Ammar zai aureki,tohhh wlh karki kuskura don ko kin auri Ammar baxaki ta6a jin da'din rayuwanki ba,banxa ',yar 'kauye 'yar matsiyata,no wonder naga yanda akeyi ma arxi'ki ashe 'yar hayece...tohhh daki aureshi gomma ma ki koma 'kauyenku kisamu dai² ke.
Kasa magana Afral tayi wanda lokaci 'daya idonta ya ciko da kwalla wanda suke gab da xubowa.saurin kama mata hannu Amrah tayi ha'di da girgixa mata kai alaman kar tayi kukan.
Wanda cike ta takun ta Amrah na isah ta 'karasa gaban lubnah. Budan bakin Amrah kuwa cewa"tayi munji 'yar mala'u.a hakan dai tafi karuwa daraja,kuma a hakan mai haiba ha'di da kamala yace"bawanda yakeso sai er anwansa er mutunci, ba karuwa mai bin maza ba,mara asali da tushe,don gunda damu ansan asalinmu wasu ko asalin nasu ba'a sani ba,daga 'kauyen ne da uban ma ko babu ohooo.

Wani wawan mari lubnah takai ma Amrah,inda Amrah cikin xamman ta rike hannun ha'di da cewa" da kinyi kuskuren marina,tohhh dana ce sae kinyi nadama a rayuwanki wlh,don sai kare yafiki daraja,banxa kawai karyan maxa.
Sauke hannun lubnah tayi da 'karfi inda sae lokacin ta dawo duniyan tunanin da ta fa'da.
Kwashe kayan da suka siya sukayi ha'di da nufan wurin daxasu bayar da ku'din kayan.sannan suka kama hanyar gida,inda driver yajasu har gida.
Chapter 10 · 0% Book details