← Book details Yar Waye Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 22

Sashe 3

Yar Waye Part 2 Complete Hausa Novel · about 11 min read

More typing...
More comment

Maman teddy ce...
[12/29, 9:55 AM] mmn tedy: Page 28 - 29

'Yar waye

_Written by: maman teddy.._

Da ido momy ta bi umar har ya fita, a ranta ko addu'a take allah yasa lafiya, don bata ta'ba ganin fushin shi haka ba.. Don haka take ta allah allah su talatu sugama mata lallen.
Anty don allah bari naje na dawo, don inaso nayi mawa Amrah siyayya kin san gobe birthday 'din tah,Ammara tace"hadi da kokarin barin falon. Anty zinah ne tace"ok gobe ne birthday 'din ko? Toh gashi wannan kyamata siyayya.ok Anty na gode, ammara tasa hannu ta amsa rafan 'yan dari biyar²guda biyu ha'di da nufan compound.da futan ta tarar da mai gadi na kokarin tare wata mata kar tashigo gidan.da axama tanufi mai gadin hadi da dakatarda shi,ammara ne ta bude baki ha'di da cewa"sannu baiwar allah, wa kike nema? Maganan take ha"di da shigowa da matan tsakiyan gidan.kallon ta matan tayi ha'di da cewa"kece nusaiba Ammara? Kuma nan ne gidan Alh.salisu mai gwal buzu? Ammarah ne tayi saurin 'daga mata kai hadi da cewa"ehh hajiya nan ne.wannan hajiyan ne tace"toh kice ma babanki binta na son ganin shi, daga waje.ok Ammarah tace'hadi da nufan cikin falon daddy, don bai cika fita a week end ba.har ta shiga falon tunani take a zuciyan ta wannan ba,matan da abban ta ya nuna mata a hoto bane, yace itah ce mahaifiyan ta, kuma ta rasu? Wata xuciyan ne tace mata kai ammarah ba'ita bace, wannan ai tafi umman ki kyau da jiki da kiba, gata wannan hajiya ce fah.da haka ta shiga falon, Abba wata ce ke son ganin ka a farfajiyan gida, wai tace"sunan ta binta.firgigit abba ya mike hadi da cewa"mai kk ce Ammarah? Ammarah ne ta maimai ta mai, ae nan Abba ya mike hadi da cewa"Ammara muje wajen ta nagan ta.Anty zinah ne dake gyafe tace"ahh nima dai bari na biyoku... Haka suka nufa barandan gidan,inda hajiya binta take.Abbah ne yaja yatsaya ha'di da mamakin ganin binta ayau. Cike da natsuwa ha'di da dattijan taka yace'Ammarah jeki gareta itah ce mahaifiyan ki. Cike da ru'du Ammara tace"Abba waye ummu na? Bakace ummu ta rasu ba?Abba ne cike da tausayin 'yar nashi, yace"ita ce mahaifiyanki Ammarah, wanda ta cireki a nono bakifi shekara 'daya da rabi a duniya ba, ta xa'bi duniya fiye da ibadar aure, saboda lokacin inah cikin 'kangin talauci... Yau gashi ta sama duniyan yanda takeso, ta auri kalan wanda takeso mai ku'din da take buri ba talaka ba.haj. binta da tuni hawaye ya rufe fuskanta tafara cewa"don allah Abban Ammarah kayi hakuri, wlh bana rabu da Ammarah don bansan ta ba ne, haka kaima, sai dan ina ganin kaman xamana da kai, ba, abun da nake saka ciki sai fitina, yau ka nemo mana bashin wannan gobe wannan, don musamu muci abunci.kuka ne yaci karfin ta, wanda sai da tayi mai isar ta, sannan ta cigaba da cewa"shiyasa na taho najeriya don inai mi aiki ko da wanke²ne, don insamo abun da xamu rika ci ni daku.naxo nigeria daga nijer da wata uku nasamu aikin wata ma'aikata inda xan rinka yin shara da goge². Nan na rokesu, a kan inaso asamin ma miji na, inda suka baka aiki a wannan masana,anta. Da farin ciki na dawo nijer ko xan ganku amma sai akace"kadauki Ammarah kabar nijer wanda ba'asan inda kake ba.nayi kuka sosai da rashin ku, haka nace bani ba nijeriya, saboda na rasa mijina mai nuna mun so kulawa, da 'ya ta 'daya tilo.. Tsanan da kowa ke nuna mun a garin nijer yasa ni barin nijer don dole badon ina so ba. Haka naxo nijeri, inda nacigaba da aikina a wannan masana,antan. A haka na soma kasuwanci, inda nine sayar da takalma jakunkuna, sarkoki da sauran su.a haka arziki ya fara bunkasa har nafara safarar xinarai, a kulum addu"a na shine allah ya hadamu don inroki gafarar ka,sai gashi sanadiyan kasuwan ci naxo har cikin gidan ka ban sani ba, sai danaga ammarah wanda kulum nake mafarkin gani, wanda kaman ka dana gani a fuskanta, yasa ni gane Ammarah jini nah ne, waigawa inda Ammarah take tayi wanda hawaye yayi mata kace² a fuska, cewa don allah ammarah kiyi hakuri da cutar dake danayi a rayuwa... Ammara kuwa nufan haj. Binta tayi ha'di da rungume ta, tana wani irin kuka kaman ranta xai fita. Rungume ta itah ma haj.binta tayi hadi da sa wani kukan... Sai a lokacin Alh.salisu yaji tausayin iyalan nashi.Anty zinah kuwa hawaye ta share ha'di da jan hannun haj.binta sukayi cikin falon gidan... Bayan komai ya matasa masu ne, suka dinga jajan ta mawa haj.binta hadi da tausaya mata.wanda suka yanke shawaran nan da kwana biyu xasu tafi garin nijer da haj.binta, haka suka dinga jajanta lamarin ummu Ammarah.
Amrah.... Amrah... Kalla wannan hoton tayi maki? Afreed ke magana hadi da mikama wa Amrah hoton, wata budurwan shi.yatsina fuska tayi ha"di da cewa"uhummm ni ya Afreed batayi mun ba,jubi fah yanda take"daga nin ta bata da tarbiya,ni dai gaskiya batayi mun ba. Mom zaituna ne tace"afff ae a haka xaku 'kare kullum busuyi ba.ni kuxo muyi soper don har yanxu umar bai shigo ba.dariya duka sukayi ha'di da nufan dirning don suyi soper. Anan ne mom ke cewa"Amrah ni nagaji da wannan kushen naki, kulum kice basuyi ba, ko dai kina da wanda kikeson ba yayan naki ne? Mom tace"ha'di da sakin mata murmushi... Afreed ne ya amshe maganan ha'di da cewa"plz my Amrah nabaki wuka da nama kixa'ba mun duk wanda tayi maki. Hmm nan Amrah ta gyara xama don dama wannan daman takeso.da farin ciki kwance a fuskan tace"why not ya afreed kaso Ammarah wlh ina ganin kundace sosai. Dajin haka nan mom ta hau dariya, don amrah ma dariya ta bata, shiko Afreed tsaki yayi hadi da cewa"wata Ammarahn? Wannan yarinyan, toh ni bama xan aura yarinya ba.kukan shagwa'ba Amrah tasa ha'di da cewa"yanxu ya Afreed kawan nawa ne bakaso, wlh toh ni baxan 'kara maka magana ba, sai ranan da ka amince.kuma baxan 'kara cin abinci ba, sai kace ka amince. Mi'kewa tayi ha'di dayin kaman xata bar wurin.saurin riko hannun ta Afreed yayi hadi dacewa"no karki fushi waya ce maki bana son ta?na yarda na amince shikenan.kissing 'din shi tayi ha'di da cewa"yah Afreed i reallly luv you soooo much.yanda tayi maganan yasa su mom da Afreed kwashewa da dariya. Don lamarin amrahn sai tabaka dariyah...hmmm ya Afreed goben ranace ta daban kenan? Afreed ne yace"a wurin wah? A wurin ki ko?dariya tayi cike da xolaya tace"ya Afreed a wurin ka dai.nan take Afreed ya fara tunanin kodai Amrah tagono shi ne, yana son ammarahn.mikewa yayi xai kamata,xiliyewa tayi hadi da nufan 'daki da gudu,itako mom zaituna ba'abun da takeyi banda dariya, ha'di da 'kara jin son 'ya'yan nata...
Da shigan Amrah 'dakin ta,ta 'daga waya ha'di da kiran Ammarahn.daga wan ta, ta fara xaiyane mata komai yanda sukayi da Afreed, ha'di da cewa"shiyasa nace ki bari mubi komai a hankali,don na lurah Afeed 'din ma yana sonki, ba kyece kike son shi ke daya ba.don haka jan kunnenki xanyi, bawai daga yace"yana sonki ki wani amshe masa nan da nan ba,at list kija mai ajin mu na mata,bakiyi saurin amincewa ba, inkuma ya gano mu shi kenan.dariya Ammarah tayi cike da farin ciki tace"wlh Amrah yau ina cikin farin ciki,na farko wanda nakeso,kin mun busharan yace"yana sona,kuma har ki kara dacewa"kina hasashen dama da soyaya ta atare da shi,na biyu kuma umma na da ta dawo gareni, wanda da nake tunanin ta mutu ashe bata mutu ba. Cike da son jin karin bayani Amrah tace"kaman yahh bangane me kike nufi ba.murmushi Ammarah tayi ha'di da bata labarin komai na umman nata da kuma ta gayamata asalin kasan su nijer.cike da farin ciki Amrah tasa ihun murna ha'di da cewa"yaushe ne xamu xo muga ummah,ae yanxu ko xan sanar mawa sweat mom don ta tayamu farin ciki.difff ta kashe wayan ha'di da nufan mom zaituna don tayi mata albishirin ganin umman Ammarah.
Bayan su Afral da Ammar sun fito gidan hajiya kaka ne,a motan xuwan su gidan su Amrah Ammar kece ma Afral, Afral kinga yanda kikayi kyau kuwa?plz kirin'ka yin irin wannan shigan yafi maki kyau wlh.cike da farin cikin yabawan da ammar yayi mata tace"toh ya Ammar daga yau xan fara irin wannan shigan tunda baka son wancan.damamki yakalle ta, a ranshi kuwa cewa"yake meyasa Afral ta canja haka? Komai aka cemata bata gadda ma, a haka su ka isah har estate 'din umar inda ake taron acan.tun daga nesa xaka juyo karan disko,da speaker,horn sukayi inda mai gadi yayi saurin bu'de masu.a natse suka fito daga motan,inda tuni idon m.c ya karkato garesu...ba tare da yasan ko su waye ba,ya hau fara xuba masu kirari.wanda Amrah dake tsakiyan fili saurin mai da hankalin ta garesu.bata gane Afral ba, don bata saba ganin ta da irin wannan kayan ba.sanye Afral take cikin wani dakakken swisss less,mai ruwan dark blue wanda akayi mai kwalliya da flowers pink a jikin ta.fuskan nan kuwa yasha makeup,sai daurin ture kaga tsiya datayi,ha'di da xubo gashi gadon baya, abun ka ga.... Bari dai inyi shiru.Ammar kuwa shigan suit yayi,wanda abunka ga segxy guy sai yayi wani mugun kyau,haka ido gaba 'daya ya dawo garesu,don ba rana ke kashe masu ido ba, sune suke kashe ma rana ido🤪
A dan hanxarce Amrah ta fito cikin taron mutanen wanda duk kawayen ta ne,ta nufo su Ammar cike da kulawa fuskanta 'dauke da murmushi.wanda sanye take cikin wani irin fitinan nan gown colon golden da stones cofee wanda yakara bayyana tsadan gown 'din ha'di da kyawun shi.kafan ta cikin wani hill shoe,mai ruwan golden kalan kayan ta,sai daurin head da akayi mata da coffee head, wanda yayi step² kai kalan fasalta maku irin kyaun da tayi baxai yiwu ba, don sai inbata a wanni ban gama ba.ba tare da takalla Afral ba tayi saurin hugging din ta hadi da cewa"you are welcome dear.dagowa Amrah tayi ha'di da kallon Afral, kallon kallo aka tsaya yi.dai² Su Ammarah, teemah na xuwa.ammarah ne data gane Afral tayi saurin cewa"sannu da xuwa sister ha'di da jan hannun hannu sukayi wani falo da itah.inda suka bar Amrah da Ammar a tsaye.murmushi shi Ammar ya sakin mata hadi da yima ta murnan xagayowan Aihuwan ta.bayan sun 'dan fara fira ne, tayi sauri" cewa bari nakaika wurin su ya Afreed.ok yace"hadi da bin bayan ta.xaune su Afreed, umar da sauran Abokanen su suke,a wani rumfah wanda ko bi takan kwama calan su amrah basuyi ba.ya Afreed ga ya ammar yaxo, Amrah tace"ha'di da saurin juyawa don ta nufi 'dakin da suka kai Afral,ba tare da taga kallon² da umar da Ammar ke mawa juna ba.da shigan ta falon ta cidda Afral ta saki sosai da su Ammarah banda firah, ba abun da sukeyi. Da fara'a ta nufesu hadi da cewa"ashe kece Afral 'din.dariya Afral tayi ha'di da cewa"wlh nice Amrah ya kike? Da fatan anaba yaya na kulawa yanda yakama ta...dariya Amrah tayi wanda dai² xata bata amsa taji hayaniya ha'di da banko kofar falon,dagowa duka sukayi waxasu gani😳umar ne ya shigo yana wani haki, da huci, fixgo Amrah yayi ha'di da cewa"kehh waye wancan? Dai² Ammar, Afreed, mom zaituna na shigowa falon.bakin Amrah ne ya hau rawa inda tafara cewa"cike da ini nah... Ammm.. Amm shine saurayina da nake fa'da mawa ya Afreed.cike da ba'kin cikin maganan ta yace"kuma kina son shi? Daga mai kai tayi ha'di dacewa"ehhhh ya umar.wani wawan mari yasakin mata, kafin ta kuma yin wani abu yakuma kara mata wani marin.da axama a kuma xuciye Ammar ya hanka'de umar ha'di da shakeshi ya fara kaimai duka.ganin haka nan suka fara dukan juna,dambe sosai sukeyi na fitar rai, kaman basu ta'ba sanin juna ba.Afral wanda ta ri'ko Amrah suna wani irin kuka don ita gaba 'daya batasan inda lamarin nasu ta dosa ba.Afreed ne yayi saurin shiga tsakiyan su, ha'di da kokarin raba su, amma sunki rabuwa sai ma duka da suke kai mai...mom zaituna da take wani irin kuka wanda bata ta'ba yin irinsa ba tayi saurin shiga tsakanin su ha'di da cewa"tohhh ni ku dake ni nace.ganin mom a tsakanin su, yasa su dole dakatawa ha'di da sauke numfarfashi.kafin mom tayi wani magana tuni umar yabar falon... Wanda wajen ajiye motoci ya nufah ha'di da daukan motan sa ya dau hanya.wani irin gudu yake wanda ko wani mai mota bashi hanya yake, hadi da yimai addu"an allah yakai shi duk inda xaije lafiya.a haka da taimakon allah ya isah Abuja.wani mahaukacin horn yayi mawa mai gadi, wanda a guje yaxo ha"di da bude get din.ko da yashigo ko parcking bai gama yi ba, yafita ha'di da nufan part 'din ummu maryam.xaune take kan sallaya tana laximi.da shigowan shi ya fa'da jikin ta ha'di da rushewa da wani irin kuka, wanda tunda take bata taba ganin hawayen umar ba.cike da rudu ta tallabo shi ha'di da cewa"farouq lafiya? Mai yasa meka? Kuka yake ha'di da cewa"ummu na rasata. Na rasata ummu, na rasa Amrah na.yana kai wa nan numfashin shi ya dauke.wanda ummu ta hau girgixa shi hawaye na sitiri a kan fuskan ta,umar waye Amrah? Don allah katashi kafada mun inda take ba xaka rasata ba.haka take girgixa shi koxai tashi amma shiru ba numfashi.dai² Alh.Abdullahi na shigowa, ganin halin da suke cike ne yasa shi rudewa matuka, musamman halin da 'dan nashi tilo yake ciki.in yarasa shi yarasa komai a rayuwan shi.shine burin shi, gatan shi, abun tattalin shi,abun kaunar shi.....
Chapter 3 · 0% Book details