Sashe 5
Yar Waye Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Hawaye ne ya hau wanke fuskan Amrah, tuni da gudu ta nufi ummu,wanda da sauri ummu ta nufo ta,rungume ummu Amrah tayi haɗi da rushewa da wani irin kuka mai ban tausayi,haɗi da tsuma zuciya...momy Rayhana kuwa kuka take sosai,don tausayin ummu maryam da ɗiyan nata yagama cika ta,kowa a wurin tausayin Amrah yagama cika su.inda a zuciyan umar,Ammar, Afreed suke cikin tsananin mamaki.dama ummu maryam itace mahaifiyan Amrah,wanda suka daɗe suna nema.wannan shi akecema ikon allah🤔
Hajiya kaka ne tafara magana cike da rashin sanin komai,hajiya maryam wai wannan wace ce ne? Dama kina da ƴa ne? Momy ne taja hannun Amrah don taraba ta da ummu maryam,amma sai Amrah ta ƙara shige ma ummu,wanda har shi kanshi umar sai dayaji tausayin ta,uwa kenan... Hajiya kaka ne takuma cewa"a'a hajiya Rayhana ƙyaleta da mahaifiyan ta, ae maraba ta yau da uwan ta kuma sai allah.duda inason ƙarin bayanin ita ɗin wace ce ne?
Gyaran murya Alh Abdullahi yayi haɗi da masu umarnin xama, bayan sun xauna ne, nan Alh.Abdullahi yafara bada labarin ummu maryam tun daga farko har xuwan doctor najwa da yanda wannan Alhaxan suka karɓa Amrah da ƙarfin tsiya haɗi da lokacin daya kaɗe ummu maryam.
Bayan Alh.Abdullahi ya ɗauki ummu maryam cike da ruɗu ya nufi wani asibiti dake cikin garin gombe.koda likitoci suka karɓesu, Alh.Abdullahi yakasa sukuni, banda safah da marwa ba'abun da yakeyi, hankalin shi bai kwanta ba sai da akasanar mai da farfaɗowan ummu maryam.
Cike da farin ciki yanufi ɗakin da aka kwantar da ummu maryam, da sallama ya shiga ɗakin, inda ya cidda wata nurse na daura mata drief a hannu.
Xama yayi a bedside drower haɗi da fara mawa ummu ya jiki.amsa mai tayi haɗi da mai da kallon ta ga nurse ɗin, don a ranta ko mamaki take, ya'akayi ta xonan.bayan fitan nurse ɗin ne Alh.Abdullahi yafara tambayan ummu a wani gari take ne? Kuma mai yasa ta shiga kan titi tana irin wannan gudu...don shi aran shi ya ɗauka mahaukaciya ne, sai yanxu da ta farfaɗo ya fahimta lafiyayyiya ne. Kwallah ummu maryam ta shere, inda tafara bama Alh.Abdulllahi labarin ta komai²... Sosai Alhj.Abdullah yah tausaya mata, inda yakisima abubuwa dayawa aranshi.kwana ɗaya ummu maryam tayi aka sallameta, inda Alh.Abdullahi ya ɗauketa haɗi da nufahn kauyen su da itah.can kuwa kauyen karau² hankalin kowa ya tashi, don kowa yasan ummu maryam da kirkin ta, ga uwa uba Amaratu.daga mai kuka sai mai jajen su da rashin su a garin.kawo ummu maryam da Alh Abdullahi yayi nan kauyen ne, nan gaba ɗaya a kayo gidan su ummu maryam don nan aka kai ta dama...Alhaji Abdullahi yasha godiya matuƙa wurin iyayen ummu maryam,inda suka koma bince ke akan inda xasuga Amrah.sune har cikin garin gombe don a nemo Amrahn.amma tsawon shekaru shiru ba Amrah ba labarinta.tun daga nan ummu maryam takoma ba magana kullum shiru, daga ibada sai ibada.wanda duk bayan sati Alh. Abdullahi yake dawowa ganin ummu maryam, ganin yanda takoma yasa shi tausaya mata sosai a arayuwan ta.inda yayi mata maganan yana so ya aure ta, firrr ummu maryam taƙi. Ganin haka yasa Alh.Abdullahi yin mata shiru da maganan.har kusan shekara guda, bayan wannan lokacin ne yasamu iyayen ummu da maganan. Inda da farin ciki suka amshi maganan.rufe ma ummu sukayi har sai da iyayen shi suka kawo komai na aure sannan aka sanar mata,bayanda xatayi don iyayen ta sun na'am da maganan auran, kuma itama gaba ɗaya taji bata kaunar xaman garin.ba a ɗauki wani lokaci mai tsawo ba akayi biki, haɗi da nufo da ummu maryam garin abuja,inda taxama cikakiyar ƴar kasuwa.kuma hajiya kaka ta nuna mata so, duda bata san meye lbrn ummun ba, kuma bata nuna mata han tara ba kasancewan ta na ƴar kauye... Don tun daga kan mahaifiyar umar da tsangwaman da ta nuna mata yasata dai na damun kowata irin surukan ta, koko ya take. Sai dai kishin da haj.kubrah ta dingayi, haɗi da mawa ummu maryam habaici iri², kallonta ummu batayi sai ma bata girman ta.tun da ummu taxo gidan umar yaxama ɗan ɗakin ta,saboda ibadan ummu, ga son mutanen ta.don haka kauna sosae ya shiga tsakanin su da umar.
Dakatawa Alh.Abdullahi yayi da maganan haɗi da cewa"tun daga wannan lokaci haj.maryam ke addu'an allah ya haɗasu da Amrah ko don ta haɗa ta da iyayen ta....
Godiya duka sukayi ma allah, inda hajiya kaka tafara jan Amrah da firan jika da kaka anata dariya.umar ko ko mawa yayi ya kwanta akan bed,don yau yarasa mai yakeji farin ciki ne, kome ne ohoooo?
Haj.kaka ko ganin umar ya kwanta ne ya sata cewa"oohhhh toh ae daka tashi ne, tun da dai wanda kake ciwon akanta ance, anbar maka. Kana wani isan mutane da miskilanci da kasaita.... Dariya duka ɗakin akayi wanda umar tsaban jin haushi da kunyan maganan hajiya kaka, yasa shi rufe ido.a ranshi kuwa cewa"yake shikenan Amrah ta riga da tagama rai nani daga yau... Dai² wata doctor ta shigo ɗakin bayanta wata mata ne kaman almajira ke tafe.wannan likitan ne tace"don alllah hajiya wannan baiwan allahn ne ke bukatan taimako, kowa nata tarasa sanadin haɗari da sukayi a mota,ƴaƴa da mijin ta,dukiyan ta gaba ɗaya duk ta rasa, don haka likita ce ƴar uwan mu ataimaka mata don allah, koda da na abun daxata ci ne...
Dagowa dukansu sukayi haɗi da kallon matan,cikin sauri Amrah, mom Rayhana,ummu maryam duka suka miƙe cike da mamaki da ruɗu Arch. Rayhana tace" doctor NAJWA???.......
More typing.....
More comment.
Maman teddy ce...
[12/29, 9:55 AM] mmn tedy: Typing...
MANAZARTA WRITTERS ASSOCOATION
_ƳAR WAYE_🤔
Written by : Ayshatou maman teddy.
Episode 34 - 35
____________________________________