← Book details Yar Waye Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 22

Sashe 8

Yar Waye Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da fargaba Amrah suka nufah sasan mom zaituna ha'di da shiga da sallaman su.inda farouq sai da yadau kusan minti goma sannan ya shigo.
Don ko ajikin sa fa'dan da hajiya kaka keyi.samun wuri yayi ya xauna.
Inda hajiya kaka tafara magana a gajirce,ba komai ne yasani tara ku anan ba illah kawai insanar maku cewa"na yanke shawaran auren umar da Amrah watanni buyu masu xuwa.sannan kuma ku su Afreed nabaku nan da sati biyu ku fito mun da matan da xaku aura,ke kuma Afral jiya iyayen wannan yaron muhammad sukaxo akan maganan aure n ku,don haka duka tare xamu ha'da sai kukuma iyaye kufah shiri....cike da murna umar ya hau xubama hajiya godiya inda wurin gaba 'daya suke mamakin rashin kunya irin na umar lokaci guda.suko su Afreed da basuga komai ba,sai dariyansu sukeyi.
Don komai yaxo masu dai² don xasuje training na wata guda,don duka xa'a 'kara masu matsayin da suke kai na captin xuwa na gaba da captin 'din.
Murna ne yakoma mawa Ammar ciki, sakamakom jin wai iyayen mohammad sun turo maganan auren Afral.nan take yace"a'a hajiya kaka ni baxa'a aurad da Afral yanxu ba,don ban son aurenta da wannan yaron.
Cike da mamaki hajiya kaka tace"tohhh mai kk nufi kenan?
Budan bakin Ammar cewa yayi nifah Afral baxatayi aure yanxu ba,dudu du nawa take? Shekaranta fah 18 ne.gsky ba yanxu ba.
Cike da masifah hajiya kaka tace" tohh baka isa ba Ammar,kai inah ruwanka,bakaso tayi aure kai xakayi?
Ok nima nafasa baxanyi ba hajiya,shikenan.
Yana kaiwa nan ya mi'ke ha'di da barin falon.

Wanda gaba daya aka bisa da kallo,itahma Afral da baso takeyi ba,ta mike ha'di da fita falon.

Hajiya kaka ne tabisu da bambami, tohhh ko kunaso ko bakwaso sai kunyi aure a wata biyun nan da nasa,ba 'dage ba jirge wlh, inkuma kun'ki na ha'daku da kowa cece.....

#share and
Comment

Maman teddy ce...
[12/29, 9:55 AM] mmn tedy: Typing...

*MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*

*'YAR WAYE???*

Written by: maman teddy.

~Garga'di~
Banyarda wani ko wata suyi amfani warun juyamun labari,kuma labari na 'ki'kirarrene ba fasahan wani acikin ta,kuma banyi shi don cin xarafin wani/wata ba,inkin ga labarin ya yi shige da rayuwanki tohhh akasi akasamu...

Dedicated to you my dear fans,naji Comment 'dinku.kuma inajin da'di sosae da yanda kuke bani ha'din kai a novel 'din gdy mara adadi🥰😘

Episode 38 - 39

___________________________________

Haka hajiya kaka ke binsu da bambami wanda 'ya'yan nata ban da bata ha'kuri ba'abun da sukeyi.
Suko su umar da Afreed banda dariyan su ba'abun da sukeyi.ganin dariyan da sukeyi ne yasa mom zaituna daka masu tsawa ha'di da cewa"sufita su basu wuri,ba musu suka mi'ke ha'di da barin 'dakin,inda dama Amrah duk ta 'kosa ace su tashi,don nauyin su mom da takeji a yau 'din.
Nufan sasan ummu maryam tayi,inda da shiganta,ta tadda Afral na masifah ha'di da ha'da kayanta,ala dole xata bar gidan ummu maryam,don acewan ta babu mai mata auren da bata so.

Afral yanaga kina ha'da kaya lfy?
Amrah ta tambayeta ha'di da xama kusa da itah...
Cike da masifah Afral ta hau cewa" kaman yah lfy,bayan duk agavan ki akayi komai.
Toh don a gabana akayi komai yanzufah ha'da kaya naga kinayi.
A gajirce Afral tace"ok toh barin sasan ummu maryam xanyi,don komawa part 'din mom zaituna xanyi yau.don itace xata iyah dakatar mun da wannan tatsuniyan hajiya kakan.
Murmushi Amrah tayi mara sauti,wanda ya bayyana beuty point 'din ta wato dimple,ha'di da cewa"still now ban fahimceki ba,dama ba son muhammad kikeyi ba?
Ehhh bance bana son shi ba,amma ae bamuyi xan aure shi ba,kehhh intially van shirya yin aure yanxu ba,mai nayi a karatuna,dududu yaushe ma nashiga jami'ar?
Don haka dole dad su san yanda xasuyi su kauda xancen nan.tafa'da ha'di da xage zips "din akwatin ta...

Dijeeee.....dije" Afral tafara kiran wata maaikaciyan gidan,wanda batare da taji mai Amrah xata kuma ce mata ba.
Da hanxari dejeee ta shigo ha'di da 'dan rankafawa gani hajiya.
Nufan er ficiciyan jakarta tayi mai launin pink ha'di da 'dauka,da kuma cema dejeee maxa dauki kaya nan ki kaymun sasan mom,amma kibi da shi tabayan back yard ne,saboda banson wannan tsohuwan tagani,yaxama kuma abun magana.
Ok badamuwa hajiya..nan dejeee ta 'dauka ha'di da nufan part 'din mom,wanda xata shiga 'dakin ta baya.

Tashi Afral tayi ha'di da varin 'dakin ha'di da cemawa Amrah" escuse....
Bin ta Amrah tayi da ido har ta fita,wanda a zuciyanta tace"ohhh Afral har yanxu 'dabi'unta irin na turawa,ko yaushe xata chanja ohoo🤔

Da fitanta ta nufi part 'din mom wanda ba wanda yasan da shigowan ta.nufan bedroom 'din mom tayi ha'di da fadawa kan gadonta,don duniyan komai ya tsaya mata cakkk.
Bayan su mom sunyi sallama da hajiya kaka ne,don har su mom Rayhana sun nufi gidajensu,don mom Rayhana tace,baxata yarda ta ha'du da Afral ba,don tasan baxasu wanye lafiya ba,tun da ta nuna batason wannan auren.
Fiye da awanni mom zaituna na xaune a sitting room,inda bayan tagama komai ta nufi bedroom,damamaki ta 'kara inda Afral ke kwance,wanda sai sharara baccin ta takeyi.don tun tana xaman jiran mom amma bata shigo ba,har bacci ya dauke ta...
'Karasowa mom tayi ha'di da jan mawa Afral blanket.a zuciyanta tana tunanin abun da Afral 'din xata ce inta farka,don tasan da wata a 'kasa dole...
Niko maman teddy nace" a tashi lafiya Afral 'din momy,sauran kuma naji wani darun😜

Amrah maxa yau ha'da kayanki kibi mom Rayhana don yau a cann xakiyi mata week end.
Tohhh ummu."Amrah tace ha'di da 'ko'karin fara ha'da kayanta.
Mom Rayhana dake bayansu ne tace"a'ahhh basai ta dau kayanta ba,don olready daddy yasiya mata wasu kayan...don haka ta bar wannan anan.
Ok tohhh ae ko mun gode mawa dady,toh maxa shirya ki fito muna jiranki a falo,sai ku tafi...ummu maryam tace"ha'di da nufan falo.
Batare da Amrah tace wani abu ba,tafara ha'da kayanta,don itama ta damu da halin da Ammar yashiga,don haka take son xuwa kodon tasan mai ke da munshi.

Bayan ta gama shiryawa ne ta fito wanda sanye take cikin shigarta na atampa super,wanda takw kalon green da fari,sai mayafinta 'dan dai² mai launin green shi ma.simple makeup ne akan fuskanta,wanda tayi 'daurin tobannn,wanda daga "kasa ta kame gashinta da ba'kin riboms.sai daurin toban 'din yayi sama,gashin kuma yasauko har gadon baya.wanda ni kaina sai da nace" masha'allah...don fa'din kyaun da tayi ma baxai fa'du ba...

Ita kanta mom Rayhana sai da ta yaba da kyaun Amrahn...
Dai² xasu fita ne suka ci karo da umar a hanya yana 'ko'karin shigowa falon.turus yajah ya tsaya,don ganin irin kyaun da Amrahn tayi, murmushi yayi ha'di da cewa"momy inah xakuje?
Dariya momy tayi ha'di da cewa" xamuje gidane acan xatayi mun weekend.murmushi tayi ha'di da shafa kan umar 'din ta wuce.
Dai² Amrah xata wuce shi ne,a dai² kunnen ta yace"you look soo,sooo beutiful,duk da ke'din dama kyakykyawane ko Amrahn hamma, but ill really miss u.
Ba tare da tace"mai komai ba ta ra6a shi ta wuce ha'di da yin mun murmushi, don kunyan hamman nata takeji sosae.kuma tana mamakin yanda shi koka'dan bai nuna yanajin nata kunyan...

A haka suka nufah gidan mom Rayhana, inda tayi mamaki matu'ku da girman gidan,da kuma tsarin shi,don komai irin na gidan su hamma umar ne.
Banbancin su daya,gidan su hamma sunfi scurities da kuma yawan sojoji...

Da shigansu daddy dake xaune a sittingroom yayi saurin cewa"wlcm home dear... Ha"di da ware hannayen shi gareta.
Dariya Amrah tayi ha'di da nufan daddy tayi hugging 'din shi...daddy ka dawo lafiya?
Bude baki daddy yayi ha'di da cewa"lafiya Amrah ya kike? Yau xakiyi mana weekend ko?
Ehhh daddy,Amarh tace"ha'di da kallon daddy tana murmushi.
Momy ne tace"yaka mata daddy kabarta ta shirya kafin kufara maganan na ku na fama.
Murmushi daddy yayi ha'di da cewa"tohh baby jeki kimtsa sai kifito muyi fira,kiban labari.
Dariya Amrah tayi ha'di da nufan dakin da mom tayi mata jagorah.

Cike dajin da'di Amrah tace"momy na wannan 'dakina ne?
Dariya momy tayi ha'di da cewa"naki ne baby,duba inda akwai abun da bai maki ba,ko kikeson a kawo maki kimun magana...
Woww momy yayi kyau sosai wlh,bari na shirya sai na fito muje wurin daddy.
Momy ne tace, ok toh ina jiranki daga 'kasa.
Bayan mom ta sauka 'kasa ne,ta cidda Ammar nata cika yana batsewa,gyafe kuma daddy ne lallashin shi...
Kallon su momy batayi ba,don tasan Ammar da kafiya...in yace baison abu toh bamai sashi yaso abun.
Nufan kitchen tayi ha'di da sanarma ma'aikatan ranan su duba food time table,don su fara shirin ha'da dinner.

A hankali Afral ta bu'de ido ha'di da mi'kewa,direct nufan privacyn mom zaituna tayi ha'di da 'dauro alwala don time ya wuce sosae.
Bayan ta idar da sallah ne mom ta shigo ha'di da cewa" afral kin tashi?
Waigowa tayi ha'di da kallon mom,nan take idon ta ya ciko da kwalla,wanda cike da rawar murya tafara cewa " mom kinji me haj kaka tace ko?
A sanyaye mom ta karako ha'di da xama kama Afral suka nufi wani super suka xauna. Mom ne ta fara cewa"kiyi ha'kuri Afral,kin san hajiya in tace,ehhh toh abi mata shixaifi xaman lafiya.don haka kiyi ha'kuri ki amince kawai..kinji my Afral.
Amemakon Afral taba mom Amsa sai kawai tajuya ha'di da kwanciya kan super,ta rufw idon ta,don ko kallon mom bata sonyi a yanxu.
Ganin haka yasa mom zaituna kamo hannun ta ha'di da cewa"ok shikenan xan san yanda xanyi hajiya ta janye maganan shikenan?
'Dagowa Afral tayi ha'di da cewa"ok kifara hanata tukunnnah.
Sannan takoma ta kuma rufe idon ta.
A hankali mom zaituna ta mike ha'di da barin bedroom din,a ranta ko tana kisifah abubuwa da dama,da xatayi akan maganan Afral 'din.
Itako Afral tun da mom zaituna tace mata haka,xatasan yanda xatayi,sai taji dan sanyi a ranta.don haka ta saki ba laifi,don har fira suka xauna sukayi da mom.
Washe garin ranan da yamma ta tattara ha'di da nufo gidan Arch.Rayhana.
Chapter 8 · 0% Book details