← Book details Yan Matan Zamani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 20

Sashe 3

Yan Matan Zamani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahmad ney yayi sallama dakin didi bayan sun ansa yanema waje ya zauna ya gaida didi,didi ta ansa tana murmushi,haka sukaita hira har sai da sukaji kiran sallahn magrib suka tashi dan gabatar da sallah shikuma ahmad yayi masallaci.koda yadawo dakin didin yadawo bayan ya zauna zeemarh ta kalleshi tace nifa wunwa nakejii yaya sai da ya kalleta da kyau yace mekikesan cii saida ta juya idanu sanan tace shawarma da suyan 111 yayi murmushi yace bakin kanwata da San dadi jita kaman suya murmushi tayi tace eh mana,waye baisan dadi didi tayi charaf tace babu wlhy yace shikenan innafita sallan isha Zan wuce dakanan zeemarh ta marairaice fuska kaman zatayi kuka tace yaya please zanje yace ba saikinyi kuka ba shikenan ki shirya kafin nadawo daka masjid.

Didi tace kanwanka kasani ko nifa mai zaka siyomin yayi murmushi yace duk abinda kikeso kakus dariya sukasa duka.

A bangaran mama kuwa wanan hali na uwar mijin ta na damunta ace Mata batasan gaskia Sam,amma dai zata tayasu da addua Allah ya shiryesu yakuma ganan dasu dan taga lamarin yariyantata da kakarta na da munta kuma yana bata mamaki( *nidai nace Allah kyw ta*) tashi mama tayi dan bata so tata tunani dakin su tashiga,ta shiga da sallama Firdausee tagani kan sallaya tana karatun Qur'ani zamun waje tayi ta zauna bayan Firdausee ta kar aya tajuwo da fara'anta tace mama kinji ni shiru wlhy ina dan karatune mama tayi murmushi tace ba komai Allah bada lada Firdausee taca amin mamanmu wai ina sis tanda nadawo islamiyya ban ganta ba mama ta tabe baki tace kinsan yayar taki sai addua tana dakin didi Firdausee tace Bari na idar da sallah naje aiyi hiran da ni.

Yana dawowa yatadda zeemarh a bakin kofanshi har tashiya tana jiranshi saida ya kalleta yace minti 1 ina zuwa bajimawa yafitoh, bagaran mama yayi dan Mata sallama zeemarh ko tsayawa tayi bakin kofa dan ita wai batasan jaraban maman.sun fitoh tare da Firdausee, Firdauseen ne tamatsa kusa da zeemarh tana cewa I miss you sisi zeemarh tayi murmushi tace I miss you too sis kije kijirani dakin didi zamudan fita da yaya ahmad Firdausee tace no pee adawo lfya...
tace allah yasa'. nan ahmad ya karaso gurin zeemerh yace sis muje ?. tace muje toh nan suka fita. suna fita yadauko motanshi dayake waje. yace muje tabude gidan gaba ta shuga tareda gir-gizanta. suna shiga tace yaya kasamin waka mana da AC . yace toh yanda kikeso haka zanyi'. suna tafiya tanabin wakan don ita duk wakar daya shigo ta iyashi'. har suka iso wani restaurant'. suna zuwa tace kai brother daga ganin gunnan za'ayi chilled. shide Ahmad murmushi yayi. Suka fito daga motan suna fita tafara taku dai dai'. irin na yayan manya har suka fito gun zamansu. suka zauna suna zama tafara kallon yanda kowa yake zuwa da fiancee insa. aranta tace kai inama nima inada hot booty. chan yace zeemerh nan tayi fir ta dawo daga duniyar tunaninta tace. emm yace me kike tunani tace bakomai yace akawo miki me dame. tace burger hot pizza da shawarma . ba tareda musuba yace drink fa? tace exotic tace toh. nan ya tashi yaje ya hado mata "yana zuwa yace kin gaji ko tace habade ban gajiba'. Yayi murmushi suka fara cin abinsu. kamar ance daga kanki tana daga ido taga wani guy. shida budurwarsa sunzo. sunnata chilling sukazo dede gun ice cream taga sun siya . tareda siyan kayanci iri iri suka samuguri suka zauna. kusada desk nasu guy in yakecewa fiancee nasa'. baby nayi feeding naso zeemerh kam se kallonsu take totally speecless. haka harsun wuce tana kallonsu. can daya lura da haka ahmad yace zeemerh me kike kallo? nan tayi tsaki mchsw nan tafara kora masa bayani. yace kai kanwata yanzu menene tace kaga ni wlh sun burgeni wlh. gashi daga ganinsu yan gayune'. yace kema ai yar' gayu ce tace bazaka ganeba. nan yace muzo mu tafi dare nayi tace toh. bangaren didi kuwa ita da firdausee se hira suketa yi. inda firdausee take gayawa didi saura izu 20 haddarta ya hadu. didi tace masha allah haka akeso .chan didi tace yawwa firdausee zakiji bikin kawarsu zeemerh da za'ayi na *YAR' GATANNAN* firdausee tace didi biki fa kikace ni wlh banda lokacin biki. ba gwara nazauna ina tilawa naba. didi ta bude baki tace kuttisi lalle firdausee nidan allah yaushe zaki waye. "tace ga zeemerh kullum tauraruwarta se haskawa take amma yarinya ance kanki a buhu. toh wlh ki gyara nide nagaya miki. se kace ba jinina a jikinki toh kigyara. itade firdausee ta kasama magana kasa' kasa tace dan allah kiyi hakuri. kafin didi tace wani abu taji kamar karar horn in mota. a sukwane ta tashi tana cewa firdausee sun dawo fa. aikam tana rufe baki sega zeemerh tazo tana ran gwada tace hi didi's didi tace oho miki ya hanyar kice kinci dadi. tace sosai ma. daga gefe taga firdausee ta zuba mata ido'. zeemerh tace babe how far'. didi tayi caraf tace wlh yarinyarnan nada matsala. ta kwashe labarin hirar da sukayi ta bata. zeemerh tahau dariya tace wlh kema bakinki be gajia. wannan yarinyar nan ce zatazo bikin zee lallema. salan guys in gun su rainani. suka kwashe da dariya se didi tace ke ina tsarabana. tace ni kaza zan iya mantawa dakene nanta mika mata yogurt da meat pie. ta karba hadda godiya ta ciire ice cream dayaa ta mikama firddausee tana ansa. tace nagode.....

© ~biebie dee~
07039732859
© ~samrah~
09062056022
*💓YAN'MATAN ZAMANI.💓* NA. biebie dee bukharii
da
Samrah

*edited by*hajja ce ❤

*this page is for you Rabiatu Sk msh thank you so much for d du'a we really appreciate*

2⃣1⃣ _ 2⃣5⃣

"haka rayuwa ta cigaba da kasan cewa kullum"
'zeemerh tana abinda take so, in ance za'ayi mata fad'a didi tayi kyamas ta hana.
'Rana bata kar'ya, saidai uwar diya taji kunya, ana saura k'wana hudu afara bik'in zee, don haka tun ran talata suka fara shirye shirye.
Kasan cewar a ran talatan deejah tak'ira idris akan ya kawo mata kayan nan haka daya kawo mata ta yabi kayan sosai saboda d'inki yayi matukar kyau sosai.
tace kai idris nagode allah ya biya zanga shegiyar da zatayi dink'in dayafi namu!" nan ta cewa mamanta mom please zanje gidansu zeemerh yanxu. mom tace adawo lafiya sbd mom irin matan nanne da basa takurama yaronsu.

"tana fita tak'ira salmah" hello babe salma tace' how far?" deejah tace ke d'inki ya iso, da karfi tace dan allah kice yayi kyau, deejah "tace ink'in zo kin gani" kizo gidan su zeemerh ina chan. tace toh ai ko gaba da china kike je zanzo".
__"tana kashe layin tacewa umma zan fita. umma tace salamatu sai ina?" tace umma angama mana d'inkin mu wlh' irin d'inkin ya'yan 'manya biki ga dink'in ba, wlh kuma kyauta fa.umma tace dan girman allah ke dan allah.
salmah tace au biki yadda ba?" tace a'a na yadda"!. tace kinga umma bara naje nagani kada suyi bani'. haka itama ta kwashi kafa ta tafi.
"koda deejah ta isa, gidan su zeemerh tayi sallama direct part in didi ta wuce" saboda zeemerh ta sabama kawayenta da zuwa part na didi, tana shiga ta ganta akan gado tana shan wankan, da gudu ta taso tana my deejar o'yoyo' tace ke dallah kada ki karyani d'in kunanmu aka kawo mana zeemarh' ta daka tsalle tace kai bestie kice zamu fice! da wankanmu' suka tafa tareda dariya".
chan didi ta shigo deejar tace didin'mu ya kike?" tace yam'mata adon gari' ya k'inzo klau"? tace wlh lafiya lau, didi tace madallah se chan zeemerh tace wai' ke ina yar iskancan shiru. kaf'in tayi shiru sega salmah tayi sallama'
"yeeeh babe mun gaji da jira" tace eyyah wlh a'a baza ku gane ba. saboda wallahi ina' tafiya ina gudu" don kawai nazo ayi dani'. nan suka tuntsire da dariya" suka hau gwada kayansu ko' kunyar didi basujiba". nan didi tahau fasa musu kai" kai
*YAM'MATA* in baku babu gari!!! tace kai zeemerh duk ke aka cuta, bayan bangan shi kamar nasuba, "yama kuke cemai hipt" ko nan suka kwashe da dariya sukace allah bar mana ke didin'mu.
"haka dai sukai ta hiransu da iya shegen su,su salma bazu bar gidan su zeemarh ba sai bayan sallan magrib.

A bangaran mama kuwa ba abinda ke shiga tsakaninta da zeemarh sai gaisuwa ita ko zeemarh hakan yamata dadi dan acewanta duk cikin friends d'inta anfi samata ido.

Mama kulin tana b'inta da addua dan taga kwana biyunan kanta Kara rawa ya keyi, kamar kulin yau ma zeemarh tace ta shigo dak'in mama da sallah Dame da gaisuwa Bata t'saya jin ko maman ta ansa ba tayi hanyan dakinsu mamace ta da katar da ita da dawowa tayi ta zauna mama ta kalleta da kyau tace ke a ganinki abubuwan da kikeyi kin kyau ta kenan yaushe rabon ki da islamiyyah ita dai zeemarh tayi shuru dan jikinta yayi sanyi mama nacikin mata nasihane baba ya shigo bayan duk sunmai sunnu da zuwa ya ansa yaneme waje ya zauna sanan ya kalle zeemarh yace naji duk abinda mamanku ke cewa kuma zanyi maganin abun nan ba da dadewaba didi ce ta shigo Baku sallah cewa take matakin kenan kace zakamata aure ko toh wlhy karma kafara shi Ahmad yaushe yafara aikin da har zai riketa Sam ba Zan yadda ba kaji nafada maka in bakin Ku bazai fada alkharee ba yai shuru kuma daka yau azeema tadawo hannuna da zama kar naji kar nagani zuwa tayi ta daga zeemarh sukai gaba shiko baba tinda didi tafara magana salati kawai yakeyi yarasa wace kalan U'wa Allah ya bashi marasan gskia mama tace hakuri zamucigaba da musu Allah ya shiryar da su.

ASALIN LABARI....

© ~biebie dee~
07039732859
© ~samrah~
09062056022

_Please ina rokon kusani a ddu'a ina fama da ciwan kai_

*Biebie Dee*_thanks_
3/29/2017 2:49:18 PM: Biebiedee: 💓*YAN'MATAN ZAMANI*💓
NA
biebie Dee bukharii Da
Samrah
*mungode sosai da gudumawar da kuke bamu Anty aina'u (ummu_abdulnaseer)& Anty hajja ce Allah saka da alhkharii ya kuma shiryamaku zuri'a Ameen*

2⃣6⃣_3⃣0⃣
Chapter 3 · 0% Book details