← Book details Yan Matan Zamani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 20

Sashe 16

Yan Matan Zamani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun fitoh daka lectures ne Zeemarh ta kalle Deeja tace" mai yahana Salma zuwa sch ney yau"Deejah tace Allah shine mafi sani"Nussy tace Allah sa dai lfya"Hawwee tace amin"yarinyan Farty ce tafara kuka dake hannun Hannah Zeemarh tamiko hannu Zata ansheta nan danan tamiko hannu nan Zeemarh tashiga yimata wasa *iman* sai dariya takeyi kallan Farty Zeemarh tayi tace" plx kibani baby nush mana"Farty tayi dariya tace nayi ya da babanta"?ke kinki sai sisi kawai kikeyi ko amarcin kikeyi har yanzo shine bansani bah,gasu Hanna dasu Salma duk sunkamu" takarasa maganan tana daria smiling Zeemarh tayi tace Allah ne dai bai kawo bah, amma time nayi ni twins ma Zan Haifa duk dariya sukayi Nussy "tace toh sisters ni zantafi coz zanbiya hospital" Deeja tace nima wlh wai baki zaiyi girki zanyi gashi babu matayi shiwai bayasan mai aiki"Zeemarh tace Allah samudace" nan duk sukai sallah ma kowa tashige motanta tayi gida .

Zeemarh gidansu tanufa Dan a anashirin bikin fiddause da Mahmud, nan ta tadda matar yaya Ahmad aunty Haleemah da 'yarta afra mai shegen wayo da suruto kamarsu daya da Zeemarh. Bayan taje duc tagaisa da mutan gidan nandai suka rubuta list din abubuwanda za'asiyo na biki nan dai sukadan yi hira Da aunty Haleemah sama sama Dan bawani shiri sukeyi bah cikin hiransu ne Zeemarh tace zatatafi da afra gidanta gobe ko jibi sai tadawo da ita sai Haleemah tace wai tak'ira babanta taji.cen Zeemarh "tace so nakema abani afran gaba 'daya”Haleemah tace Abuja xakibishi ko kijira yadawo sai kuyi magana Dan ta waya bazai yuwu bah(Ahmad yanzo a abuja yake aiki yasamu k'arin girma awajen aiki)
Zeemarh tak'irashi yakumace taje da ita ba damuwa Haleemah najin haka tamasu mama da Didi sallama tajaa motarta tayi gida.Zeemarh bata iso gida basai after 6 wanka tayi ita da afra gami da sallah Already *Salma 'yar mutan gombe* mai aikinta tagama dinner saukowa k'asa dukayi taxubama afra tanabata kadan taci tace bataci nan Zeemarh ta hadata da kayan zaki dama abinda takeso kenan

Saidatayi sallan Isha sanan tazauna cin abinci inda afra sai wasa takeyi *yar mutan Gombe* kuwa sai hira takema Zeemarh .

Bayan Zeemarh tagama cin abinci waya da dauka tashiga k'iran Salma, sai da tak'irata sau 4 Ana 5 tadauka Zeemarh "tace wai inakigashiga ta alhajj sai k'iranake babu ansa a maimakun Salma tabada ansa sai kuka tafeshemata dashi tashi tsaye Zeemarh tayi tace"lafiya,meyafaru,ko bakida lfyane"? Rage kukan tayi tace Friend Ashe Alhaji yanada Mata gaban Zeemarh ne yafadi dam tace inalillahi wanan maganan bazai yuwu ta wayaba zanshigo gobe insha Allah nan takatse k'iran tana mamaki irin wanan lamari ko da *Salma 'yar aiki*ketamata hira shuru kawai tayi

Sai 10:30 Zeemarh tadau afra ta kwantar da ita SALMA YAR AIKI ma taje ta kwanta wanka Zeemarh tasake gami da sakayan bicci mai kyaun gaske sai kamshi takeyi Palo takoma ta kwanta a 3 siter tanakalan wani film a zee world,bata dade da kwanciya a wajenba bacci yayi gaba da ita.

Bugun 'kofa tafaraji kaman amafarki, buga 'kofan akeyi bana wasabah nan da nan ta tashi tayi wajen 'kofan Dan tabude,tana budewa wazatagani Almansur ne a bige yashawo giya tsayawa tayi abakin 'kofan taki matsamai cikin zafin nama ya bangaje ta tafad'i har yayi hanyan sama sai kuma yadawo janta yashiga yi yanacewa wlhy sai kunbiyani kudina,yama za'ayi kuce kuncinyeni impossible wlhy janta yashiga yi tana tirgewa bata ankaraba taji ya dauketa da Mari gami dacewa muje sai kunbiyani kud'ina ai bashiri tashiga binshi bai ajeta a ko inabah sai cikin bedroom dinda suke kwana daa(Dan banace yanzo ba)hannu yami'ka Mata gami da "cewa give me all my money nafasa game din"nan tashiga dakko duk wani kudi datasan ta ajiye yana ri'ke da ita sai da tami'kamai dukku dadan sanan yasaketa yafita

D'akinda ta kwantar da Afra takoma sai da ta babbatar ta saka key sanan tazube a kan gadon gami da sauke wani kuka mai tsuma zuciya,kuka takeyi bana wasa ba chan ta tanbaye kanta dama Almansur nashan giya,yana chacha?? Wai ya'akayi banga ko alamaba wata zuciyan tace ku'di yarufe maki ido"haka taita tunana tana kuka har bacci barawo yayi gaba da ita.

K'arfe 4 daidai ta tashi da matsanancin ciwan Kai(Allah sarki Zeemarh)tanan kwance har akayi k'iran sallan asba nan ta rarrafa tashiga toilet tayu Alwala tafitoh window ta leka nan ta hangeshi xai tafi masallaci a zuciyan ta tace"akwai Sallah amma babu hali" wata zuciyanne takuma cewa toh inkana sallan ai anasamaka ran shiryiwa wata rana " hawayene ya zubu Mata tasa bayan hannunta tashare sallaya ta shinfida tashiga sallah ta 'Dade sosai tana addua(abinda batayi da) kafin ta 'dago daka sujadan koda ta idarma sai datayi azkar,tadade sosai tana addu'a sai da gari tafara gske ta kwanta nan da nan bacci yayi gaba da ita

Bata k'ara tashiga sai 9:43am shima Dan Afrah ta tashi ne,kallan Afrah tayi Tamata smilliig itama Afran smillig take Mata toilet tayi da ita direct brush tayimata gami da wanka sanan suka fitoh shiryata tayi cikin wani shot gown baby Afff tayin kyau sosai chocolate tabata sasan itama tashiga wanka bata jima sosai bah ta fitoh, shiryawa tayi cikin gown na atanpa 'dinkin A Shep, kayan yazauba ajikinta sosai ko powder bata saka ba ta dauki Afra sukai k'asa Dan yin breakfast, tana da lectures 12pm kum

Bata yi tsamanin yanan ba kitchen ta wuce ta dauko Dan k'aramin cup wan da zata hadana babyAff tea, zamatayi a 'daya daka cikin kujerun sanan ta aje Afra kan 'daya tea tahada Mata sai tosted bread nan tashiga bata k'adan Tasha wai batasha kuma kallanta Zeemarh tayi "tace zan maki bulala fa" maimakon Tasha sai daria kawai take Mata itama Zeemarh daria tayi" tace zakisani Afra ce tayi magana tace"mami shiweet Zeemarh tayi dariya tace" see your moth like shiweet,sweet not shiweet" tashi tayi da niyar daukoma Afra sweet daji ance "where ar u going"rudewa tayi nan da Da nan jikinta yafara rawa duk tarasama mai zatace mai phone dinshi yadauka yana dannawa tanan a tsaye Afra ko tanacin pala wasanta taketayi kallanta yayi yace "samin abinci"nan tashiga zuba mai bayan ta gama tawuce sama da sauri

Koda taje bedroom bayan ta daukarma afra kayan tsakinta abinda zata bukata ta dauka sanan car key tafita. Yaban inda ta barshi kitchen tashiga tama SALMA 'YAR AIKI sallama tafitoh nesa da shi kadan ta tsaya tace "Zan tafi sch" banxa da ita yayi sai tapping phone dinsa ya'ayi zatakuma magana kenan yace" what d u want"tace banida mai a mota kuma motan nadan bani problem 2days" bai kalleta bah sai cemata yayi kisiiya ai kina da ku'di bai tsaya jin abinda zatace ba yayi gaba.

Kafin sufitoh har yawuce a ranta tace da dane fa shi zai kaini har sch amma ji yanzo gaba daya ya chanza,Afra tasa a mota itama tashiga suka tafi sai databiya ta bank ta cire kud'i sanan tayo sch.

Yau ko su 3 Kai sukazo Ita,Deejah sai Farty abin yabata mamaki bayan sunfitoh ne Zeemarh tace zataje taduba Salma nan Deeja tace zata farty kuma tace zatakai baby iman hospital batajin dad'i amma su gaisheta sukace zataji Allah ba babymush lafya" Farty ta ansa da anin

Motan Zeemarh suka shiga kasancewan Deeja batazo da natabah,tana zaune a gefe sai babyAff a ba tana surutanta gidan Salma sukayi direct a u/dosa, suna isa mai gadi yabude masu gate suka shiga bayan sunyi parking ne duk sukafitoh
A palo suka taddata dagani Tasha kuka kamar ba Salma yar gayu bah, tana gansu taje tayi hugging dinsu bayan takawo masu juice da cake ne Zeemarh" tace duk kingama wata kalla" Sakma tace ba dole bah Alhaji yahya dai Ashe matan shi biyu nice ta uku gashi yahanani xuwa sch ku duk yanda kukasan shidai bah haka yakema bah zan iya cewa hutun wata shida kawai nayi a gidanan nafara fuskantar bakaken halinshi, ga ruwa ga bakar mako da mugun hali, yaki daukarmin mai aiki ga cikinan nabani wahala" Zeemarh tayi shuru tace mukuma tamu kaddan kenan" Deeja tace wlhy koni hakane rowa yakemin ba nawasa ba da nayi magana yace ai da naci, dai dai da man mota ninakesiya dana yau ba sarki sai Allah nace nahakura" Zeemarh tace naku da sauki nifa Almansur masayi ne sai tafashe da kuka nan duk dukai ta bata hakuri bayan nan Zeenarh tace kilallabashi yabarki kicigaba da zuwa sch kibah komai zaki temaki kanki dakuma ummie"Zeemarh tace kifadama Ummie sai tarokeshi" Salmatace nanawa kuma ya raina Nata ai sai yagadama"Deejah tace insha Allah zai yadda"
"Salmatace Allah sa motanama ko mai babu kuma nasan babani zaiyi bah" Zeemarh ta zuge jaka tabasu 5k dukkansu tace"gashi kowa tayi manage nima cikin kud'inane da su baba suka bani nakayan d'aki sai Wanda Almansur yabani da,nasan yanzo abubuwa xasu chanza Dan yau ko ku'din manmota yak'ibani"Deeja tace ai mungode wlh, wai ace mutane duk sunchaza kuma bawai Dan basudashi ba"Salma tace rabon mumukacinye tin a waje"Zeemarh tace mudage da addu'a insha Allah,Allah xai yayemana"duk suka ansa da Allah sa" nan suka ma Salma sallama suka tafi,
Suna tafiya Salma tak'ira Ummie tana bata labarin kyautan da Zeemarh tamata sai godiya takeyi, nan tafadamata shawaranda suka bata Ummie" tace zatak'irashi taji,inyace ma bazai biyabah ai sai akarasa biya daku'din hayan gidanmu" Salma tace Allah sa mudace nansukai sallahma

*****************
Al'amari na Almansur gaba yakeyi ba bayaba kulin Zeemrh cikin kuka takeyi gashi sisin nairansh yadena bata ga sha'anan bikin Fiddause.
Tafadama Didi damuwanta Didi tayi mamaki matuka da wanan hali na Almansur dakucema Zeemarh ta Dage da Addu'a Allah yamata zabin alkhari *ni biebie* nace AMEEN FA

shirye_shiryen bikin fidaudee aketayi da Mahmud ko naira 'daya Almansur bai ba Zeemarh bah yaushema yake kwana a gidan bare har ta tanbyeshi saide cikin ku'din ta dauko 50k sai wani lace da tasiyarmawa k'awar 100k Almansur ne yakawo Mata lokacin suna zaman da'di shine tahada 150k tabada
Chapter 16 · 0% Book details