← Book details Yan Matan Zamani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 20

Sashe 13

Yan Matan Zamani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fida wajen gidan nasu ta manna space a fuskanta sai tayi kaman wata celebrity...lol k'iran shi tayi a waya babu bata lokaci ya iso nan zuka bazama bayan subar NNDC moll chicken republic sukaje take away sukayi suka nufi garden dinshi nan suka ta hiransu da Dan tabe_tabensu(Allah shirya)bata dawo gida bah sai Ana k'iran magrib, sai da tayi wanka tayi sallah sanan taje tama su mama sannu da gida tana dawowa d'aki phone dinta dauko tashiga wayan Nata na fama.
*********************Ahmad yasamu wata yarinya haleemah sister'n wani friend dinshi ce, tana respecting dinshi sosai haka shima batada San abin dunia sam duk abinda kadauko kabata sai dai tayi godia da addua Ahmad najin da'din halinta babu ruwanta very simple girl
Haka sukai ta gudar da soyyarsu da Haleema cin kwanciyan hankali.

Babu Wanda yasan zancen daka shi sai mama Amina.Dan ko k'adan bai chanzama Zeemarh bah suna hira wasa da daria sometimes har assignment yana Mata Dan ko ba komai jini ba wasa bane

********************

Haka rayuwarsu tai ta tafiya inbaka da cash baka da wani sauran mutinci wajensu ko kanadashima in baiyi masuba sai dai su lashe ka Tass subarka sudai mutincinka ku'di ney.

K'awaye kuwa sai abinda yayi gaba yaran manya da yara irinsu barasa godiyan Allah . biki kuwa indai da maiko suna hanyan zuwa
Sunsan mutane sai kace wasu 'yan siyasa.

Suna fitowa daka lectures Deeja ne ta kalle Zeemarh tace" wai zamuje kuwa"?Salma tace mai zai Hana ai kodan na k'ara Baku labarinan"Hannah tace wai da gske Rahma Aliyu aure zatayi"?Salma tace ai shiyasa nakeso muje wani wajen da ba hayani ya na Baku labarin mijin ta, Abubakar na malali friend Dina ya sanshi"
Hauwee "tace yanada kudi ne"?
Deeja tace" irin na rage zafi bah" tashi duk matsawa wajen da ba hayani ya sukayi sai gumar bikin Rahma Aliyu sukeyi

Ko da bikin yazo basuyi wani rawar hai bah a cewar su sunfi k'arfin duk abokanan angon. Ita dai Rahma anyi biki lfiya ankuma gama lfya komai yayi kyau dai dai ba k'arya

Haka rayuwar su tai ta tafiya kulin burinsu gaba yakeyi ba baya bah har suka shiga 200lvl inda Fiddaudee itama tasamu KASU tana ka'ranta political science.

Ranan da Ahmad yakawo Haleema gida Dan ta gai da su Didi da su mama hauka ne kadai Zeemarh batayi bah Dan bata dauka zaiyi aure haka da wuri bah....

Biebie deee ce
🍁🍁🍁'YANMATAN ZAMANI🍁🍁🍁

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*STORY & WRITTEN BY*
~BIEBIE DEE BUKHARI~

_this page is for you sweetheart Ummie Garkuwa, thank you so much for d du'a.I love you so much sweetheart stay blessed_❣❣❣❣

9⃣3⃣

"""""" D'aki ta shige Dan ko face din Haleemah baza ta iya kallo bah, sabida haushen ta datakejii.

Ahmad ne yashigo d'akin da sallama a kwance ya ganta, zama yayi a bakin gadon sanan yace"sisi gafa antynku na kawo maku bakifitoh kun gaishe ba" yatsina fuska tayi sanan tace wlhy kaina keciwa please ace inagaisheta" Ahmad yace eyyah sorry sis, Allah sawake" yafita Zeemarh ta bishi da wani dogun tsaki mtswwwww.

Ahmad ko a ranshi sai yaji kaman bai kyautama tama da yamata zancen Haleemah, duk yaji baiji da'di bah

Haleemah ko ta yaba sosai da halin mutincin family'n Ahmad, Dan ko wannensu sai da yabata abin arziki babu abinda yafi birgeta kaman yanda sukai tasaka Mata Albarka taji da'di sosai takuma jii sansu harcikin ranta.

Koda takoma gida haka taitabama su amminta labari Suma sai San barka sukeyi da k'ara sa Albarka.

Zeemarh yinin ranan bata fita bah, haka kuma batayi picking din call din kowa ba Dan batajin da'di Sam kowa da komai haushi yakebata

Hakadai tagama weekend d'inanan cikin rashin walwala har Monday. Koda suka fitoh lectures da friends dinta ke tanbayenta nan duk tabasu labari, Hannah tajee tsaki sanan tace"kisan kina sanshi wayahanaki auranshi"?Deejah tace shidai nagani" Salma tace ai sai ki dage da addu'a"Hauwee tace shedanne kawai, kinada kaman Al_mansur yaro da ku'di ga kyau abinda kike nema, mai zakiyi da wani Ahmad? Tsakanunku sai zuminci ai" Nussy tace gara ki natsu da kyau kikuma dawo daidai"Salma da Hannah sukace da yafi kam"Farty ce ta'karasu wajen su kallan su tayi dukka sanan tace" babies wats wrong"?Nussy ce ta Mata bayani
Kallan Zeemarh tayi tace" kar kibani kunya mana mai naki a ciki Allah sama ya aura Mata 4 a Rana d'aya dat he's problem"Zeemarh tace hakane insha Allah ya wuce" Salma tace good"
Farty ce tayi magana" babies kutashi muje gidan wata cousin Dina Feenah amaryace daka abuja aka kawuta nan u/Rimi nan" Hanna tace Amira fa"? Farty tace wai bazata bah, shiyasa na anso car key d'inta sai Hanna ta jaa nata"
Nan duk suka tashi suka nufa inda sukai parking motan.Faty tashiga Zeemarh a gefenta sai Hauwee a baya.motan Amira kuma Hannah ce ke driving sai Salma a side dinta sai Nussy a baya haka suka dau hanya sai gidan cousin Farty, watou gidan feenah

Tinda ka bakin gate Salma da Hanna suka rude sai sanbatu sukeyi Dan gidan ya hadu ni Kai na sai da na Lora horn sukayi mai gadi ya bude ai sai anan Zeemarh taga fasalin gidan Dan tinda suka Fara tafiya chrttin takeyi kallan Farty tayi tace" naso naga mai gidanan" Farty yayi daria tace kuma wlhy age mate din muce bah" Zeemarh tace Masha Allah Allah samu adanshinsu" Farty tace nima soon zanzo nayi auran tayi magana tana daria

Kulle motan sujayi duk suka nufa 'kofan da zai kaisu cikin polon tsayawa duk sukayi Farty ta k'irata tace" kibude 'kofa batajira taji abinda zatace ba ta kashe k'iran, suna Kama wayan akabude 'kofan saide ba Feenah bace watace Wanda ita kanta Farty bata wani ganeta bah, farace sosai duguwa tanada kyanta dai dai ita dakaninta kunga yar gayu kuma Wanda sukeji da naira, itama dai baza tawuce mate dinsu bah. matsamasu tayi sukashige tana masu murmushi basukai da zama sai ga feenarh ta fitoh daka kitchen da tray a hannun ta
K'ara sawa wanan buduruwar tayi ta ansheta, a gabansu ta aje drinks ne da kayan motsa baki Zeemarh ce tace thank you murmushi kawai ta Mata

Bayan sun gama gaisawa Farty tama Feenah introducing friends dinta ita kuma Feenarh tamasu introducing sister'n mijinta wato *Ramalurv* nan sukai ta hira Ramalurv da Zeemarh Dan har jininsu ya hadu k'iran Amira ne ya tsaye masu hira Zeemarh ta k'ira cemata suna ina gatanan k'araso wa" Farty ce ta ansa phone din tama kwatancen gidan ba a jima ba sai gata ta iso nan dai suka baje akai ta hira Ramalurv sai basu labarin samarinta takeyi da yanda take garasu dai 5pm suka fitoh sai da Zeemarh da Ramalurv sukai ansa number juna

Ansa bikin Haleemah da Ahmad zukuga farin ciki wajen mama Amina kamar me, Ahmad yayi kokari sosai komai yasama Haleema dai dai Dan da Zeemarh taga kayan auran tayi mamaki komai na cikin a kwanin unique ne mai kyau.haka dai akai ta shiri har biki yazo *kamu* a Arewa house, kuma yayi kyau sosai Amarya da ango sunsha kyau har sungaji

Zeemarh tayi kyau sosai dan Al_mansur yasakar mata ku'di banda kudadrn da wasu samarin nata suka bata, friends dinta duk sunzo su Salma duk sunsha kyau ganan gansu kaga manyan yara Ramalurv ma tazo gidan brother'n ta tasauka kwana friends din Zeemarh kawai abin kallo ne Dan sunhadu sunyiya dressing ba k'arya
Fiddause ma tayi kyau Abu dai yayi kyau sai San barka

Ankai amarya gidanta mai kyau anan kabala cstain, gida yayi kyau ko wa sai sa Albarka yakeyi.

Haka rayuwa yaita tafita Zeemarh Al_mansur na sakar Mata kudu tinda ya Lura abinda takeso kenan.

Salma ma tasamu wani alj.Yahya maikaci ne babba a NNPC

Haka su Nussy, da Hauwee, ko wannesu akai Wanda ta ajee amma basubar cikin kudin Samari ba.

Ansa bikin Farty, suna gama exams dinsu za'ayi *yanmatan* sai shiri sukeyi Dan a cewar su wanan bikin babba ne...

Zeemarh tace da sunshiga 300lvl zata tura Am_mansur gida Dan ayi maganan Aure Dan taga fiddause so take ta tura muhmud gida ita ko baza ta yadda da haka ba, gara taga yadda ake sauke akwatuna da yanda Mata ke baza kwalliya.

Cikin ikon Allah sungama exams lfya shirye_shiyen biki aka fara babu Kama hannu yaro Zeemarh kuln tana busy Dan sune *Amara 'kirjin biki* Ramalurv ma tazo da wata friend dinta *memxy* itama 'yar gayuce ta k'arshe

Salma alhj.Yahya ya sake cash Dan Ummie ma tace itama zata biki acewarta Farty ma ai 'yartace tinda k'awar Salma ce
Anko Salma tasiya Mata na iyaye 25k lace ne sanan Salman ta Kai Mata d'inki a ka zuba Mata stone work mai lfya( abin nema yasanu..lol)

Friends *laiyajey* ce zata masu makeup each dinsu 12k. bride kuma *I.Laurah*ce zata yimata tindaka garin abuja a ka dauko ta, kowani event 150k ne, event 3 kawai za'ayi sai yinin biki Dan mijin Farty bayasan hayaniya sosai

*bridal shower* suka Fara inda sukai masifar kyau kada ma Farty taji labari *l.Laura* ta fitoh da ita ba kadan bah, kyau d'inda Farty tayi yasa Zeemarh kudira a ranta itama *l.Laura*ce zata Mata .
Next day akai kamu ranan ma sunyi kyau sunsha pictures kaman babu gobe, Snapchat yayi kuka haka Instagram da duk wani social network datakeyi sun San friend din Zeemarh na aure. Zee ma tazo da yaronta Fahad very cute boy dashi

Ran Friday aka daura aure, simple yinin biki sukayi sai dare suka wuce dinner nan ma sunsha kyau ba ka Dan ba Zeemarh, Ramalurv, memxy, Salma,Nussy,Hauwee, Hannah da Amira kaita sai kashe salfie Duke da Amarya
🍁🍁🍁'YANMATAN ZAMANI🍁🍁🍁

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*STORY & WRITTEN BY*
~Biebie deee bukhari~

_thank you so much for d love n care Zee zee I really appreciate,stay blessed_💞💞💞💞

9⃣4⃣

""""""Angama komai lfya ankai Amarya gidan ta mai masifar kyau dake u/Rimi,gida yayi kyau haka kayan ciki ma komai dai Masha Allah.
Chapter 13 · 0% Book details