← Book details Yan Matan Zamani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 20

Sashe 11

Yan Matan Zamani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Awaje ta tadda Didi tana tsince wake, musmushi Zeemarh tayi"tace kakus mai kuma zakiyi da wake"?kallanta Didi tayi da kyau kafin "tace wlhy marmarin fatan wake nakeyi su Amina basa San irin girkinan shine yau nakeson nayi"Zeemarh na daria tace ki k'ira yaya daddy(Musa) yazo maki da plantain sai muhada dashii, kinga yau zai dawo daka sch"Didi tace a'a y'an biyu Zan k'ira"Zeemarh tace ashe bazaki ci ba kuwa indai wayananne"Didi tace duk su Zan k'ira nabasu sak'o sai naga nawa yafi yawa"Zeemarh tace Bari naje na gaida su mama"Didi tace da kyau.

Side mama murja tayi,ta shiga d'akin da sallama bayan mama murjan ta ansa, samun waje tayi ta zauna sanan tafara gaisheta,ansamata tayi cikin sakin fuska Zeemarh "tace mam baba fa"?mama tace bai d'ade da shiga wanka ba y'ar gidan baba"Zeemarh tayi murmushi tace inya fitoh agaidashi,Bari naje nagaida mama"mama murja tace ki gaidamin ita"Zeemarh tace insha Allah"

Da sallama ta fa'da d'akin mama, Ahmad ne yayi saurin juyowa, murmushi ta sakarmai shima ya maidamata sai da ta zauna ta gaida mama da baba sanan Ahmad duk suka ansa fuskasu sake. Daki ta wuce wajen fiddausee, duka ta kaimata bashiri fiddause ta tashi "Zeemarh tace wlhy yunwa nakeji plx ki dafamin indomin ki mai masifar d'di"Fiddausee tace inkina so jirani nayi wanka na shirya nima"Zeemarh tace indai zakiyi ai mai sauki ne"

Batawani d'ade sosai a toilet din bah ta fitoh, Shiryawa tayi cikin gown na atanpa d'ikin yayi kyau sosa Zeemarh tace"beautiful muje "fiddausee tayi daria tace ai kinfini kyau"haka dai suna wasa da daria suka wace kitchen nan fiddausee ta hadda indomie bayan sun gamane suka dawo Parlor man suka zauna sunaci suna hira da sai k'arfe 12:00pm su baba suka tafin sallan juma'a

Shara sukayi da mopping "Zeemarh tace sis muyi girki yau"fiddausee tace mai zAmudafa "Zeemarh tace muyi jolof rice da coslow"nan suka shiga kitchen suka Fara aiki,kamshin girkinne yafitoh da mama Dana cikin d'aki kitchen tashiga nan taga Zeemarh sai yanka cabbage takeyi murmushi tayi sanan tace Allah muku Albarka suka ansa ta amin mamanmu"

1:30 sungama komai,coslow nan na Zeemarh yasha style sai daukanshi pix akeyi, abincin ta diba kadan a plate da coslow tayi side Didi bayan tagama cine tayi sallah "tace ma Didi zata gidansu Salma anso wani paper"Didi tace adawo lfya"

Fadawa d'akin tayi bako sallama" baby kina ina?"SAlma tace ina fa zaki ganni kishigo a harkitse"Zeemarh tace bawani kawai nak'osa na baki labari ney"Salma tace yauwa ya kukayi"?Nan Zeemarh ta shiga bata labari suna daria sai da sukayi mai isarsu sanan "Zeemarh tace wai ina Ummie ne"?Salma tace taje u/sarki biki wata y'ar group dinsu kee aura'r da y'arta "Zeemarh tace hala bikin na manya ne"?Salma tace yakike Abu kaman bakisan Ummie ba,tafini San kud'i fa"Zeemarh tace kedai bakida mutinci wlhy"Salma tace ai gskiya ne"
"Zeemarh tace ba wajen zuwa ne?"Salma tace akwai wlhy Deeja nake jira sai gak"i *daraja super market*nakesan shiga kinsan nayi wani sugar daddy Hannah cee ta hadani da shii"
"Zeemarh ta harare ta sanan tace da banzo ba bazaki k'irani ba kenan"?
"Salma tace naga ai kina ma su baba tuggu ne nashi bazaki fitoh ba sai kin gama amma sorry besty" harara ta bata sanan tace"ance fa sugar daddies b'ata yara sukeyi"
"Salma tace indai baza'a level 3 ba ai da sauki,ke nidai inzai sake hannu muje zuwa kawai"
Sallaman Deejay ne ya katse ta,Deeja na zama tace"ta Ahmed yakukayi ne"
"Zeemarhtayi musmushi tace hadda girki nayi yau Dan yaudara" duk sukayi daria k'iran Didi tayi a waya "tace Ummie ta aikesu kar ajita shuru"Didi tace adawo lfya.

Alhaji ya Kai su super market suyi shopping hadda na banza sanan yabama KO wannesu 10k tasaka crdt sai d'adi sukeji
Gidan su salma ta aje kayan sanan tanufo gida.

Vail dinta a ajee kawai ta fa'da toilet wanka da alwala tayi gown tasa Mara nauyi sanan ta tafara sallah, bata bar wajen ba sai da tayi isha'i.

Waje takoma wajen Didi bayan Didi ta idar da sallah "Zeemarh tace abinci na"Didi tace su y'an biyu sunciye"Zeemarh tace aidama nasan sai su, ba'a wuce tayi"Didi tace insunjiki keda su ni ba ruwana"

K'arfe 9 dadai duk sukazoma Didi hira Zeemarh na zaune nacin indomie bayan duk ta gaidasu ta maida hankalinta kan abincinta "a *zuciyanta*tace wai nan duk sunzo meeting ne faa Zan Baku mamaki gobe, za'ayi komai ta k'are ne"
Kallan Ahmad tayi ta sakarmai murmushi shima murmushin ya Mata "a ranta takuma cewa dakanada ku'di da na yarda amma innaa badani baa....

*inayimuku fatan Alkhari a duc inda kuke masoyana*❤❤❤❤

_Biebie Dee_🌸
07039732859
🍁🍁🍁'YANMATAN ZAMANI🍁🍁🍁

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*STORY&WRITTEN BY*
~BIEBIE DEE BUKHARI~🌸

8⃣6⃣_9⃣0⃣

""""""Haka dai akai ta hira har zuwa k'arfe 11mp kowa yama Didi sai da safe ya tafi Dan kwanciya.

Zeemarh bata kwanta ba sai da tagama wayanta da Samari da kuma chatn sanan ta kwanta da niyyan anjima ka'adan zata bama Didi tsoro.

Hanan ne kuwa yafaru k'iran sallan farko Zearmah ta tashi sai shure_shure takeyi da sambatu da yaree Wanda ita kadai tasan metake cewa

Haka Didi ta tashi sai addua takeyi Mata dataga abin bah mai k'arewa bane shine taje tak'ira su Ahmad, suma haka sukai tamata addu'a.

Zeemarh bata bar subah sai da tajii antada sallah sanan ta gyra ta kwantaa,nan da nan duk sukayi Alwala sukatafi *masjid*

Koda suka dawo daka *masjid* din d'akin Didi suka shugo nan sukaga Zeemarh sai sharar baccin ta takeyi hankali a kwance.

Zeemarh ba ta tashi ba sai 7:30 toilet ta wuce direct ta 'dauro Alwala, bayan ta idar da sallah phone dinta ta 'dauko, data ta bude ta shiga group din su
"Babies yau akwai bala'i faa, bakuga yanda na basu tsoro da asbahi ba"jinsu shuru datayi tasan va su tashi ba, Snapchat tashiga tana ta haukanta tana cikin yin video ne tasa wak'an *sweetdrms* sai ga Didi ta shigo, tsayawa tayi kawai tana kallon ikon Allah Zeemarh KO sai music din takebi nata blushing

Sai da ta gama Didi tace" Anya Azeemarh kina ganin fa baki da lafiya amma da safiyar Allah kin kamajin wa'ka"Zeemarh tace kudai gidanan komai sa ido kai, dakayin good morning shine wani wa'ka ni gskia banasan haka" fita tayi fuuuuu tabar d'akin Didi ta bita da Ido

Side mama Murja tayi a parlor ta tarar da su, ta gai dasu tana murmushi duk suka ansa cikin sakin fuska "baba Aminu yace 'yar gidan baba mamanku tace kinzo nemana jiya ko"? Zeemarh tace ehh dama gaisheka kawai zanyi" baba yayi daria yace madallah sai da Zeemarh tashi tea sanan ta bar d'akin tanufi side mahaifiyarta,

Ta shiga da sallama bayan sun ansa ta shita sauna kusa da baba, sanan tafara gaisheda 'yan d'akin tinda kan mama da baba gar Yusuf 'yan biyu ne kawai ba ta gaida ba Hussain yace" ni shiyasa nafi shiri da feedy a kanki bakisan na gaba da ke bah Sam" Zeemarh tayi daria sanan tace very soon Zan zama yayarku koo baba"? Hussain kasa ce Mata komai yayi su Fiddasee KO sai daria sukeyi
"Mama tace kedai Allah shiryeki"Zeemarh tayi musmushi kawai, haka dai akaita hira har zuwa 12:40 nan duk mazan sukayi Alwala suka tafi *masjid* sai da suka k'ara gyara parlor'n sanan suma suka shiga d'akinsu Dan yin nasu sallan.

Kafin su baba su dawo daka *masjid* su Zeemarh sungama zuzzuba a abincin a food flask mama "tace duk sukai side Din Didi"
Haka KO sukayi duk abinda za'a bukata sai da suka Kai suka ajee.

Koda su baba suka dawo side Didi sukayo direct already su mama na wajen
Bayan su zazzauna ne Zeemarh da Fiddause suka fara zuzzubawa sai da suka bama kowa sanan suma suka zuba nasu, nan Zeemarh ta fiddo phone dinta ta daukesu picture tana daria fiddausee tace" duk murnar ne haka"?
Zeemarh tayi murmushi kawai a ranta tace"zakuga murna kuwa"
Whatapp ta shiga ta ma group din friends dinta sanding pictures din da ta sauka su Didi na cin abinci
"Babies za'afara meeting faa"
Hannah tace ai sai kik'ara shuka tsiya, ayi komai a gama yau ba sai gobe bah"
"Deejah tace da yafii kam"
"Nussy tace kida murmushi ne ko da suntashi na k'aryan zasuce bayin kanki bane"
Zeemarh tace ke da kikasan komai ai murna naketayi"
"Salmah tace please baby na yau nafi na kulin"
"Zeemarh tace don't worry booboo na"
"Amira kaita tace nidai kiyi sauri Dan yau munada fitah,
Coz wani yaron friend daddy yazo daka kano, yace yanaso nakai yaga kd"
"Salmah tace inkuma bakiyi sauri bah mutafi"
"Zeemarh tace bye sai nazo"

Hankalinta ta maida kan abinda Didi ke cewa,"tin dai dai Azeemarh da yardanta ai sai ayi kawai, inyaso sai ta cigaba da karatun a d'akin Ahmad KO hakan baiyi ba"? Tagama maganan duk tana kallan su.

Baba aminu yayi gyran murya sanan" yace hakan yayi Allah tabbar mana da Alkhairi" duk Kansu suka ansa da Ameen

Baba Abubakar yace" ina ganin kawai ai anarana kawai inyaso sai ajee afadama yan manni kawai" Didi tace babu laifi"

Zeemarh shuru tayi taji iya gudun ruwansu ashe abin da gskene haka, Ai bata tsaya jin mai za'akuma cewa ba ta yanka uban k'ara Wanda yasasu rudewa gaba dayansu.

Magana tafara cin wani irin muryan Wanda ni kaina bangane ganshi bah " baza muyadda ba wlhy, bamu yadda ba wlhy, Kai Ahmad bamunce kafita har kanta bah? Zaburatayi data mike su baba suka riketa, cigaba tayi da cewa ai tinda baku janye ba muma bazamu FASA ba dauketa zamuyi bazaku k'ara ganinta ba"
"Didi tana kuka tace bayan Allah Dan Allah kuyi hakuri"
"Wani daria zeemarh tayi tace inbaku fasaba muma baza mufasa ba"su mama da su Ahmad dai addu'a kawai suke tofah Mata Dan basuda bakin magana sai dai addu'an kawai.

"Ahmad yace indai har zaku barta nima na hakura"Didi ta daura da cewa Ehh Allah huce zuciyar kuu"
Wani shu'umin karfi ne ya zo mata , tashi tayi da sauri tayi waje tana cewa sai munyi shawara"
Binta da ido duk sukayi suna kuma Addu'an Allah sa ta sawo.

Koda Zeemarh ta fita gidan su Salma ta wuce,ganinta kawai Salma tayi a gabanta Salma har Dan tsorata tayi Dan babu KO talalmi a k'afanta
Chapter 11 · 0% Book details