Sashe 9
Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta gyad'a masa kanta a sanyaye ta koma ta jingina da kujera tana mamakin ya Nusayb a ranta yadda wai ita ce har yake bata hakuri duk da laifin da ta mishi d'azu.
Basu d'auki dogon lokaci ba suka iso cikin garin Kaduna saboda gudun da yake, kai tsaye gida suka nufa yana parking ta bud'e gambun motar ta fito tayi cikin gida da saurin ta, ta iske Daddy sai ya Sudais zaune a falo da gudu tayi kan Daddy ta rungume shi ya d'ago ta cikin farin ciki yace, "Mamana kune ke tafe haka da yamman nan".
Ummi tace, "Eh wallahi Daddy mun same ku lafiya" yace, "lafiya k'alau". Sai a sannan ta dubi Sudais tare da koma wa gefen shi ta zauna, sai ga Nusayb yayi sallama ya shigo ya hango Mummy da ke fitowa daga kitchen kai tsaye wajen ta ya nufa ya rungumeta tare da gaishe ta, tace, "sannu babana ya hanya?" a shagwab'e yace, "Lafiya lau Mummy na".
Ta rik'o hannunshi suka iso falo sai a sannan ya na dariya ya je kusa da Daddy ya gaishe shi, Daddy yace, "mhm Autan Mummy sai yanzu ka ganni ko bazan amsa ba toh"..........
*Jiddah Samusa ✍🏻*
[8/4, 3:26 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*
*Na*
*©Hauwa Esmaeel Musa*
*Page*4⃣3⃣
Dr. Nusayb ya zube a gaban Daddy yana dariya had'e da d'ora kansa bisa k'afafun shi yana tuba nake Daddy na kasan naka na musamman ne ai.
Ya Sudais yace, "Daddy kar ka yadda da d'adin bakin shi", Nusayb ya d'ago ya dubesa yace, "kai yayana Waya kasa da kai" duk a kasa dariya. Ya Sudais yace ka kyauta shine kuka had'e kai, kai da fatima kuka d'auke Ummi.
Yi hakuri yayanmu wani lokacin da kaina ma zan kai muku ita cewar Nusayb, ya sudais yace, "ai wa lubna zaku bawa dan tayi fushi daku tace"
Ummi tace, "Allah sarki aunty lubna".
**** ***** ****
Da misalin k'arfe goma na dare bayan kowa ya shiga d'aki, falon ya rage daga Daddy sai ya Sudais, Sudais ya dubi Daddy yace, "kace akwai abunda zamu tattauna Daddy da ya shafi Nusayb".
K'warai kuwa Sudais, dama zance aure ne kasan dai matsalar Ummi na duk wata toh yanzu a bisa bayanin likita abun yayi k'amari dan haka na yanke shawaran had'a Nusayb da Ummi, dan nasan ko bayan raina zai rik'e min ita Amana insha Allahu banason tayi maraici ita kenan nake gani a matsayin d'an uwana naji sanyi a raina "
Sudais yace, "Daddy hukuncin da ka yanke yayi fatan mu Allah ya tabbatar da alkhairi".
Ameen thumma Ameen cewar Daddy.
Daga haka suka yi sallama kowa ya tafi makwancinsa.
*Jiddah Samusa ✍🏻*
[8/4, 4:00 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*
*Na*
*©Hauwa Esmaeel Musa*
*Page*4⃣4⃣
Washe gari da misalin k'arfe goma sha d'aya na safe, sun kammala kalaci duk sun hallara a falo baka jin k'arar komai sai A.C da TV.
Daddy yayi gyaran murya sannan ya umurci Nusayb da ya bud'e taron da addu'a, bayan sun shafa, Daddy duk yabi su da kallo kowa ya sha jinin jikinsa in ka cire Sudais kad'ai da yasan makasudin zaman.
Daddy yace, "Nusayb, Ummi inason ku bani aron hankalinku ki ji abinda zan fad'a muku da kyau, ba shawaran ku nake nema ba ga dukkan abinda zaku ji face umurni nake baku".
Dukkansu gaban su dukan tara-tara yake ba uku ba kowa da tunanin da yake sak'awa a ranshi, can suka tsinka yi muryar Daddy yana cewa, "zan had'aku aure da zarar Ummi ta kammala makaranta nan da uku masu zuwa insha Allahu".
Gaban Ummi ya bada rassss! hawaye kawai ke ambaliya bisa fuskanta.
B'angaren Nusayb wani irin dad'i yaji ya ziyarci zuciyar shi tsaban murna ya kasa rufe bakin sa.
Daddy duk yana nazarce dasu ganin Nusayb yana murna yasa hankalin shi ya kwanta, ya dubi ummi yace, "mamana inason ki kwantar da hankalinki ki rungumi zab'in dana miki insha Allahu nan gaba zaki ga alfanun da yake ciki wannan aure kiyi hakuri kinji".
Ta gyad'a kanta tare da fad'in "insha Allahu Daddy zan kasance mai yi ma biyayya cikin ko wani hali muddin bai sab'a ma shari'a ka mun abunda ko iyayena iyakacinsa abinda zasu min kenan koma k'asa da haka ko kare ka kawo min kace na aura zan aura bare d'an cikinka dan haka ba abinda zan saka ma dashi da wuce na ma biyayya sai ko addu'a"
Daddy yace, "Allah ya muku albarka" duk suka ce "Ameen".
Mummyn yara baki ce komai ba, ai ba abinda zance Alhaji duk k'ark'ashin ka muke duk abinda ka zartar muna maraba dashi fatan mu Allah ya tabbatar mana da alkhairi.
"Ameen"..............
*Jiddah Samusa ✍🏻*
[12/20, 6:57 PM] +234 806 161 2054: [8/5, 8:50 AM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*
*Na*
*©Hauwa Esmaeel Musa*
*Page*4⃣5⃣
Wunin ranar Dr. Nusayb ya kasance cikin walwala da annushuwa, takanas ya tafi gidan abokinsa Abdullah dan a ganin shi wannan magana tafi k'arfin a sanar da ita ta waya.
A b'angaren Ummi ta rasa a cikin wani yanayi ta ke, ita dai tasan bata son Nusayb ko kad'an a ranta, Falaq ce ke bata baki akan ta rungumi wannan k'addara insha Allahu zata ga akhairin wannan had'in sannan ta k'ara da cewa, "Ummi na jima ina miki sha'awar ya Nusayb dan kunyi matuk'ar dacewa wallahi kuma naga sonki a k'wayar idanunshi tun ba yau ba".
Ummi ta dubi Falaq duban kina da hankali kuwa, sannan tayi tsuka mtswwww! Tace, "Amma ko hasashen ki ya baki k'arya wannan d'an ji da kai d'in da manyan 'yan mata ma suna bibiyarsa amma basu isheshi kallo ba sai ni zaki ce, wanda kullum maganan shi ni kwaila ce".
Falaq tace, "yanzu bazaki yadda da magana ba ta nasani amma nan gaba kad'an zaki gani da idonki", ke kika sani dai cewar ummi, Falaq ta k'yalk'yale da dariya had'e da tashi tace, "kinga tafiya ta".
**** **** ****
2 DAYS LATER.......
Zaune suke bisa teburin cin abinci suna kalaci , Daddy ya ga shiru Nusayb bai fito ba, ya dubi Ummi yace, "mamana dubo yayanki ko lafiya shiru bai fito ba".
Murd'a k'ofar d'akin da tayi yayi daidai da fitowar shi daga "bathroom", yana d'aure da "towel" iya k'ugunsa kirjinsa gashi ne kwance luf-luf.
Ta rufe idanunta ta juya zata gudu da sauri yayi azamar damk'o tsintsinyar hannunta had'e da jawo ta zuwa jikinshi har suna jin hucin junansu, jikinta sai b'ari yake ta rufe idanunta.
Dr. Nusayb yace, "wato tsabar kin girma kina son susa tun ba ayi auren ba har kin fara biyo ni d'aki ko? toh bari na baki abinda kike buk'ata" da sauri ta ware idanunta ganin yana kokarin kunce towel yasa ta saki k'ara.........
*Jiddah Samusa ✍🏻*
[8/5, 9:42 AM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*
*Na*
*©Hauwa Esmaeel Musa*
*Page*4⃣6⃣
Ya k'ura mata ido ganin yadda take magiya ya cika ta, sai ya ta burge shi, a hankali yaji wani abu na yawo cikin sassan jikinshi ya kai bakinsa da niyyan sumbatar ta nan take wani sashe na zuciyar sa tace, "mai kake shirin yi" nan take ya kori shaid'an tare da ture ta daga jikinsa, cikin tsawa yace, "fita ki bani wuri in kika kuskura kika k'ara shigo min d'aki ba tare da na baki izini ba jikin ki zai gaya miki".
Ta fashe da kuka cikin sauri ta fice ko wajen su Daddy bata koma ba ta wuce d'akin ta ta fad'a bisa gado.
Bayan fitar ta daga d'akin ya sauke numfashi mai k'arfin gaske, ya zauna bakin gado ya tallafi hab'arsa sai da yaji ya dawo daidai sannan ya tashi ya shirya a gurguje ya fito, ya iske duk an gama karyawa nan ya gaishe da iyayensa cikin ladabi, Mummy ta dubesa tace, "toh maza sai kaje kayi breakfast ko" ya amsa da "toh".
Ya zauna bisa tebur tare da k'walla ma Asabe k'ira, ta fito tace, "yallab'ai an tashi lafiya?" lafiya kawai yace, sannan yace k'iramin Ummi a d'aki.
Ta iso a sanyaye tare da fad'in "gani ya Nusayb" yace oyaa zuba min abinci, tace a ranta, "shege d'an iska mai tab'a mata" a fili kuma tace, "toh" nan ta zuzzuba mishi ta tura gabansa zata tafi ya tsai da ita yace zauna ban sallame ki ba ai.
Daddy dake zaune a falo yana hango su wani dad'i ya ziyarci zuciyar sa ganin Nusayb yaji maganarsa dan dama yace yayi kokari yana Jan ta a jiki ta haka ne zasu saba.
Yana cin abincin shi cikin kwanciyar hankali yana murmushi tare da fad'a mata bak'aken maganganu sai ka rantse hiran arziki suke, ya cigaba yace, "karki yi tunanin zan aure ki dan ina sonki ne a'ah zan aure ki ne dan biyayyar iyaye da kuma taimakon ki tunda jarabar maza ta miki yawa tun baki je ko ina ba zaki tafasa ki k'one".
Cikin k'unar rai tace, "toh nima ce maka nayi ina sonka? Biyayyar iyaye tasa zan aureka kuma bazan tab'a sonka ba" tayi tsoka mtswwww! Ta wuce d'aki...................
*Jiddah Samusa ✍🏻*
[12/20, 6:58 PM] +234 806 161 2054: [8/4, 8:43 AM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*
*Na*
*©Hauwa Esmaeel Musa*
*Page*4⃣0⃣
Kwanci tashi ba wuya hutun su Ummi ya k'are, yau suke shirin komawa, a d'an zaman da tayi a gidan Aunty Fatima ta koyi girke-girke nau'i - nau'i da sauran abubuwa.
Horn yayi maigadi ya bud'e masa gate ya cinno hancin motarshi cikin harabar gidan ya samu waje yayi parking sannan ya fito yana sanye cikin shadda ruwan toka d'inkin half jamfa yana shiga falon idonshi yayi katari da Dr. Dangana da Ummi suna zaune cikin k'ayatattun kujerun falon suna hira.
Lokaci d'aya annurin fusk'arshi ta gushe ya k'arasa zai wuce kamar bai gansu ba sai Dr. Dangana ya masa magana ya waiwayo fuska a had'e yace, "ya akayi?".
Dr. Dangana yace, "na zaka wuce ne ba tare da mun gaisa ba gashi neman iri ya kawo ni gidanku", Dr. Nusayb ya murmusa sannan yace, "ban lura bane kaina ke ciwo".
Ummi da tun shigowar shi hantar cikinta ya kad'a sai a yanzu ta d'ago ta dube shi cikin sa'a idanunsu ya sark'e da na juna, wani mugun kallo ya watsa mata ba shiri ta tashi tayi upstairs da gudu.