← Book details Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 17

Sashe 7

Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaban Ummi ya bada ras! Tace, "oh ni ummi ba dai laifi nayi wa wannan mutumin ba? Koma dai menene bari naje naji".

Ta same shi a inda ta barshi yana danna waya, ta samu k'asar "carpet" ta rakub'e sannan tace, "gani ya Nusayb ".

Sai da ya mula sannan ya d'ago kanshi had'e da ajiye wayar shi, ya tsura mata ido ba tare da k'iftawa ba har sai da ta tsargu tace, " ya Nusayb mai kake gani? "

Dr. Nusayb cikin hargowa yace, " da Allah can gafara mai za'a gani a jikinki *kwaila* dake, sannan uban wa yace ki fita daga gidannan? "

Ummi tace, "kamar ya uban waye ya Nusayb? Naga dai ba ni kad'ai na fita ba" tana gama fad'a ta ji sauk'ar rank'washi a kanta.

Yace, bani wayarki dan ban yadda dake ba, ba musu ta mik'a mishi ya karb'a yasa a aljihu, sannan yace, "kika kuskura kika k'ara fita ba da sanina ba sai nayi mugun b'ata miki rai, kuma karki manta da sharad'ina ban amince kiyi soyayya da kowa ba ni nan ya nuna kansa da yatsa ni zan zab'a miki mijin da zaki aura dan haka be careful".

Tashi ki bani waje in kin shiga kice wa Aunty fatima na wuce.

Tace, "ya Nusayb wayar ta wa fa?".

Yace, "zo ki k'wata mara kunya" yasa kai ya fice ya shiga motar shi ya tafi gidansa..........

*Jiddah Samusa ✍🏻*
[12/20, 6:57 PM] ‪+234 806 161 2054‬: [8/3, 5:33 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*3⃣7⃣

Bayan ya isa gida sai daya gama komai na al'adunsa duk daren duniya sannan ya bi lafiyar gado, ya kashe "bedside lamp", nan ya tuna da wayar Ummi, kai tsaye ya tashi ya d'auko sannan ya fara latsa wayar.

Contacts ya shiga ya gama bincikensa bai ci karo da wani bak'on number ba, ya wuce messages nan ma bakomai sai sak'onni da yake turo mata, shi kad'ai ya rink'a murmushi yana mai hamdala a ranshi ganin ba wanda take huld'a dashi daga haka bacci mai dad'i yayi awon gaba dashi.

**** **** ****

B'angaren Ummi ko gabad'aya hankalinta ba a kwance ba ganin wayar ta na hannun Dr. Nusayb, tsoron ta d'aya kar ya duba sak'onnin da ake turo mata dan ya hanata kula maza.

Sai juyi take a gado ganin hakan bazai fissheta ba ta sauk'o k'asa ta kunna kallo, wani American film mai suna "Arrow", ba ita ta kwanta ba sai wajajen k'arfe sha biyu cike da tunanin bawan Allah mai turo sak'onni.

<<<<<>>>>>

Washe gari da rana Ummi da Sabir zaune suna buga "Game", zareefa na "Homework", yayin da Aunty Fatima ke zaune mimi na mak'ale da ita tana kukan banza.

Yayi sallama ya shigo, yana sanye cikin shadda wagambari "dark blue" ta sha zubi da "light blue" d'in zare yayi kyau Sosai gabad'aya falon ya d'auki kamshin turaren sa "Hug" mai dad'in k'amshi.

Da gudu yaran suka tashi suna fad'in Uncle oyoyo, ya d'aga su d'ad'd'aya sannan ya iso ya zauna rik'e da Mimi a hannunsa.

Aunty Fatima ta dubeshi fusk'arta d'auke da murmushi tace, "Autan Mummy irin wannan gayu haka? Ko dai daga wajen budurwarka kake?"

Dr. Nusayb ya murmusa yace, "Aunty kenan kin cika zolaya , ni yunwa nake ji sosai wallahi a bani abinci".........

*Jiddah Samusa✍🏻*
[8/3, 5:33 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*3⃣8⃣

Aunty Fatima ta waiwaya b'angaren Ummi ta ga wayam, tace, "a'ah ina Ummi kuma tayi?" Sabir dubo Auntynku ko tana d'aki.

Ta fito sai a sannan tace, "ina wuni ya Nusayb" ya dubeta ya watsar sannan yace, "lafiya".

Aunty Fatima ta dubeta tace, "yi maza ki had'o masa abinci da abun sha ko", kai tsaye ta wuce kitchen ta had'o masa duk abinda ya dace bisa babban tire ta zo ta dire a gabansa, ta yi serving d'inshi yadda ya kamata, ya dubeta yace, "Sannu da kokari yau anyi abun kirki".

Ummi ta b'ata fuska tace, "Aunty kin ganshi ko"

Ta k'yalk'yale da dariya tace, "ai kun saba fad'anku ni 'yar kallo ce" ummi ta fara gunaguni tare da barin falon.

**************

1 WEEK LATER.......

Ummi na gani an turo bisa gadon d'aukan mara lafiya a sume take, Aunty Fatima duk hankalinta ya tashi, da sauri ta k'ira Nusayb a waya ta shaida masa gasunan fa Ummi ba lafiya.

A sukwane ya shigo cikin asibitin kai tsaye ya isa inda suke ya samu Dr. Dangana yana dubata, nan ya tsaya har ya kammala daga k'arshe ya d'aura mata k'arin ruwa.

Nan Suka fito tare da jawo k'ofar, Nusayb yayi wa Aunty Fatima nuni da ta shiga d'akin yana zuwa.

Zaune suke a office d'in Dr. Nusayb suna tattauna matsalan Ummi, Dr. Dangana ya dubi Nusayb yace, "a gaskiya abokina situation na yarinyar nan ya girmama, ciwon gaba gaba yake bazaiyu wu ko yaushe tana kan magani ba, kai Dr. ne kasan illolin wasu daga cikin drugs d'in nan wanda zai iya kawo matsala a mahaifa dan haka aure shine kad'ai maganin matsalan ta"........

*Jiddah Samusa ✍🏻*
[8/3, 5:33 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*3⃣9⃣

Dr. Nusayb ya ja gwaron numfashi daga bisani yace, "duk nasani amma kasan tayi k'ank'anuwa da aure ko makarantar gaba da firamare bata gama ba".

Kai kake ganin haka, meye ne bazata iya ba na d'aga cikin rayuwar aure? Cewar Dr. Dangana.

Toh ba matsala zanyi musu bayani.

Dr. Nusayb ya iske Aunty Fatima tana waya da Mummy tana shaida mata abinda ke faruwa, ganin shi yasa ta tsinke wayar tare da tambayansa ya ake ciki? nan ya mata bayanin komai, da mamakin sa sai yaji tace ai wannan ba abun damuwa ba ne tunda ta kusa kammala wa ai komai yazo da sauk'i, ka bar komai a hannuna zanyi wa Daddy bayani insha Allah zai fahimta tunda lafiyan ta ake nema.

Shikenan Aunty.

Yanzu ka zauna a wurinta bari naje gida na d'auko abubuwan da zamu buk'ata.

************

Kwana su biyu a asibitin ta samu sauk'i daidai gwargwado Nusayb ya bata kulawa duk abinda ta nuna tana so nan da nan ya sayo ya kawo mata, har ita kanta tana cewa, "ashe dai ya Nusayb akwai tausayi".

A gefe kuma Dr. Dangana ya nuna yana son Ummi amsar da ta bashi shine bata fara soyayya ba, shi kuma ya dage kai da fata sai ta fara soyayya a kanshi.
Duk wannan bidirin Nusayb bai sani ba dan a gefen Dr. Dangana yafi son sai sun had'e kansu kafin ya yi surprise wa Nusayb, a halin yanzu sunyi musayar numbern waya da shike Nusayb ya mayar mata da wayar ta.........

Toh masu karatu muje zuwa dan jin yadda zata kaya

*Jiddah Samusa ✍🏻*
[12/20, 6:57 PM] ‪+234 806 161 2054‬: [7/31, 8:33 AM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*3⃣1⃣

Mummy da k'awarta Hajiya Asiya suka tarar a parlour, Ummi ta gaisheta ta wuce d'aki yayin da Nusayb ya zauna bisa kujera suka gaisa tare da tambayarsa wajen aikin sa, daga haka ya tashi ya wuce d'akin sa.

Hajiya Asiya ta dubi Mummy tace, "nikam Hajiya Maryam yaron nan kun mishi mata ne?"

A'a, mai ya faru ne?

Hajiya Asiya tace, Wallahi nayi sha'awar sa ne wa Aisha, mai zai hana yaje ya ganta in har ta masa kin ga sai a k'ulla zumunci.

"Hakane Hajiya Asiya, bari zan tuntub'e sa dan ji ta bakin sa, kinsan halin d'an yau ba a iya musu cewar Mummy kenan".

Bayan tafiyar Hajiya Asiya, Mummy har d'aki ta iske Nusayb, yana zaune yana aiki a "laptop".

Ta zauna kusa dashi sannan tace, "babana wajenka na zo" haba Mummy Shine baki k'irani ba har sai kin taso da kanki, karka damu autana, dama wata magana ba ce mai tsaho, ni har yanzu baka samu yarinyar da ta kwanta ma a rai bane?

Nusayb yayi shiru daga bisani yace ban samu ba Mummy, kinsan ni ba ko wani tarkace nake so ba.

Nasani babana, amma kasan dai lokaci yayi da ya kamata ka aje iyali, dan haka ga shawara mai zai hana kaje ka duba d'iyar Hajiya Asiya, ta gama karatunta gashi har ta fara aiki kaga sai ku daidai ta ko.

Kai tsaye Nusayb yace, Mummy gaskia bata min ba.

Shikenan tunda haka kace bazan maka dole ba, tana gama fad'in haka ta tashi ta fice.

A fili ya furta, kaji Mummy da kwashe-kwashe, wato har na ishe ta ko me? Ni mace d'aya nake so a rayuwata wanda zuciyata da gangar jikina suke muradinta............

*Jiddah Samusa*✍🏻
[7/31, 9:03 AM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*3⃣2⃣

2 DAYS LATER....

Janye da trolley ta fito, Nusayb ya karb'a yasa a booth sannan ta bud'e gambun motar ta shiga, shi ma ya shiga mazaunin direba ya zauna, Mummy da Asabe na d'aga musu hannu daga haka maigadi ya wangale mishi ya gate ya cinna motar shi.

Bacci take sosai a hanya bini-bini ya dubata , ba ita farka ba sai da suka iso cikin garin Abuja.

Ta dube shi tace, a'a ya Nusayb har mun iso ashe, yace mai zai hana tunda ke tsabar wauta kin saki baki da hanci kina bacci har da minshari.

Yoo Allah na tuba meye a ciki dan nayi bacci ni ba direba ba, kai da kake direba ai baka ga ta bacci ba.

Keeeeee! Dan rainin hankali ni zaki duba ki cemin direba ko? Zanyi maganinki kuwa yayi k'wafa.

Tace haba likita bokan turai, wasa nake maka fa wallahi dan Allah kayi hakuri.

Nusayb yace daya ke ni abokin wasanki ko? Ko shiga taitayinki duk randa kika kuskura kika shigo hannuna bazan miki da kyau ba.

Daga haka kowa yayi shiru, kai tsaye gidan shi dake Gwarinpa ya nufa, yayi horn maigadi ya bud'e mishi ya shiga ya wuce "parking space" yayi parking sannan suka fito.

Ummi tace amma ya Nusayb kamar nan ba gidan Aunty Fatima ba ko sun canza gida ne?

Oho! In kin shiga kya gani da idonki, yana gama fad'in haka ya wuce gaba, bata da zab'i illah ta bishi a baya..........

*Jiddah Samusa✍🏻*
[7/31, 9:29 AM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*3⃣3⃣
Chapter 7 · 0% Book details