← Book details Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 17

Sashe 15

Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dubu goma ta kawo mata had'e da abubuwan da suka shirya duk ta zuba mata, Asabe sai godiya ta ke, har farfajiyar gidan ummi ta rakata sannan ta dawo ta k'ara k'awata gidan da freshener 'yar dubai "Jameelah" sai k'amshi ke tashi.

Tana jin k'arar horn tayi sauri ta k'ara feshe jikinta da turare "True love" sannan ta fito da gudu kan ta zo har yayi parking ya fito yana hango ta ya bud'e hannu shi ai ko ta fad'a suka k'ank'ame juna sai kuma ta fashe da kuka........

*Jiddah Samusa✍🏻*
[12/20, 7:00 PM] ‪+234 806 161 2054‬: [8/12, 11:51 AM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*6⃣9⃣

Zaune yake a office yana duba patients amma rabin hankalin shi yana gida, Allah Allah yake ya gama duba su ya tafi gida ya ga Ummi.

Sai da ya d'auki a k'alla hour d'aya da rabi sannan ya gama dasu, ya fara tattare kayakinsa, yana shirin fitowa Dr. Dangana ya sako kai office d'in, yace, "a'ah badai har ka tashi ba naga ko k'arfe hud'u bai yi ba".

Dr. Nusayb yace, "k'warai kuwa kasan abunka da ba gwauro ba dole na je matata" ya fad'a yana mishi gwalo, dariya yayi sosai Sannan yace, "sha kuriminka ka yanzu ma albishir na zo maka da dashi eheee".

Fad'i naji toh in da gaske kake dan nasanka da tsilla-tsilla, Dr. Dangana yace, "an bani mata fa acan birnin kebbi yanzu maganan dana ke maka nan da wata biyu biki" karka gayamin cewar Nusayb.

Wallahi kuwa abokina bari nayi sai komai ya kankama ai sannan na fad'a maka.

Dr. Nusayb yace, "toh a ina ka had'u da 'yar kebbi kai da ba zuwa kake ba?"a wajen bikin ka ranar dinner na had'u da ita sunanta *FEENAH*,gaskia na tayaka murna sosai ai gara ka shigo kaima kaji yadda abun yake lokaci tafiya yake,cewar Nusayb.

Hakane abokina Allah dai ya mana jagora, muje na taka ma kafin ka fara k'orafin na rik'e ka.

Hahhhhhh kamar sani kuwa wallahi, suna tafiya suna hira har suka kai parking lot sannan sukayi sallama ya shiga mota tun yana hanya ya k'ira wayar Ummi tana ringing amma ba a d'auka nan ta ke hankalin shi ta tashi ya fara gudu cikin k'ankani lokaci ya iso gwarinpa, horn yayi maigadi ya bud'e masa gate ya cinna motar shiga ko wurin parking bai isa ba ya bawa nasiru mai bawa fulawa ruwa d'an mukullin motar akan ya gyara masa parking.

Da sauri ya isa k'ofar falon ya murd'a ya shiga ido yayi da ita tana kwance bisa carpet tana sharar baccin ta, ajiyar zuciya yayi mai k'arfi sannan ya isa d'aki ya ajiye briefcase d'in shi ya fito ya d'auke ta cak ya kai kan gado ya shimfid'e ta zai tashi ta kamo hannun shi duk a cikin bacci ta fara suratai dariya yayi yana shafa kanta sannan a hankali ya zame hannun shi............

*Jiddah Samusa✍🏻*
[8/12, 2:45 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*7⃣0⃣

D'akin ta ya nufa ya tarar da Zareefa na bacci, duka ya d'aka mata baya ba shiri ta bud'e ido tana sosa bayanta, yace wato shine kula da matata d'in da kike ko, kin zo kina bacci akan laushi kin barta yashe a k'asa a falo.

Zareefa ta turo baki tace, "kai Uncle irin wannan dukan da zafi fa kuma ita tace tafi son k'asan ai" bai ce mata komai ba ya fice.

Yana zuwa kayan jikinsa ya cire ya fad'a bathroom ya sakar ma kansa shower bayan ya fito a gurguje ya shirya yasa jallabiya ash color sannan ya isa ga teburin cin abinci nan ya zuba ya fara ci sai zuba loma yake saboda yunwa dake cinsa dan tun safe coffee kawai yasha ya fita dan ya makara.

Yana cikin ci Ummi ta fito tana had'a hanya, da sauri ya dire cokalin hannunsa ya isa gareta ya rik'o ta ya zaunar da ita bisa kujerun dake falo yace, "meke damunki Ummi" tace, "jiri kawai nake ji sannan na rasa abinda yake damuna" tana gama fad'i tasa kuka tare da k'ank'ame shi, cikin kuka tace, "please ya Nusayb a cire min cikin nan haka nagaji wallahi ko ina nasa kaina bana jin d'adi".

Hakuri ya rink'a bata har tayi shiru sannan yace ina zuwa, nan yazo ya mata gwaje-gwaje ya ga komai normal baby ma na cikin lafiya, sai dai har yanzu BP yaki sauk'a, damuwa k'arasa a fuskan shi yace karki damu sauran kad'an insha Allah.

Abincin ya deb'o ya zo ya fara bata taci ta k'oshi sannan ya k'arasa cin nasa.

**** **** ****

Anyi bikin Falaq cikin lafiya inda ta tare a gidan mijinta khalid dake zaria, sai dai fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a masu Albarka, duk wasu hotunan events da akayi ta watsap ta tura wa Ummi, Ummi haushi kamar ya kasheta ganin ba ita, amma ba yadda ta iya.

Wayarta dake bisa dining ya d'auki k'ugi yana neman agaji, ta dubi Zareefa tace, 'yar Albarka mik'o min wayata cikin sauri ta tashi ta d'auko tace laaaaaaa grandpa ne ashe.........

*Jiddah Samusa✍*
[12/20, 7:01 PM] ‪+234 806 161 2054‬: [8/12, 10:17 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*7⃣3⃣

Washe gari da misalin k'arfe shida na safe, Aunty Fatima na zaune bisa kujera yayin da Ummi ke kwance tana bacci ita da jaririn dake kwance kusa da k'afarta, k'arnin jini ta fara ji nan ta duba kasan ummi jini kawai tagani kwance male-male kamar an bud'e famfo sosai ta tsorata.

Waya ta bugawa Nusayb cewar akwai matsala fa, cikin lokaci k'alilan ya shigo da wasu doctors biyu, dama a asibitin ya kwana nan ya duba ya ga jinin da aka sa mata ne yake ta zuba a rikice a ka mayar da ita "theatre room" Dr. Nusayb ya kasa tab'uka komai duk jikinsa ya sauk'a yayi sanyi dan matsalar ba k'arami ba ne.

Awa d'aya biyu shiru ba wani labari time d'in har su Daddy sun iso sai safa da marwa suke, can Dr. Izge ya fito yace da Nusayb yazo jiki a sanyaye ya shiga d'akin nan suka shaida mishi sun yi iya yin su jinin nan yak'i tsayuwa fa, kai tsaye Dr. Nusayb yace, "dole sai an cire mahaifar" nan aka hau sabon aiki bayan sun gama a ka fito da ita duk ta ji jiki.

Nan Nusayb yayi wa su Mummy bayanin komai sun tausaya mata matuk'a

*****
Kwanan ta biyar a ka sallamesu suka dawo gida ganin tunda mijinta likita ne duk abinda ya dace zai mata a gida, Mummy ce ke zaune da ita.

D'akin ya shigo ya tarar tana ba wa yaron nono, ya zauna gefen ta yana mata sannu yace ina Mummy fa? Tana kitchen, bayan ta shayar da yaron ya karb'a ya kwantar sannan ya duba ciwon ta ya bata maganin ta tasha.

Ya k'ura mata ido tace, "yadai?" yace wani suna kike sha'awar a sawa yaron nan, tace inason a sa masa sunan Daddy, yace kiyi hakuri na riga da na masa hud'uba da sunan mahaifin ki, meyasa? Bakomai kawai haka nayi niyya, amma da kabi ta nawa da sunan Daddyn dai muka sa.

Karki damu hakan ma yayi, a sanyaye toh shikenan Allah ya raya mana, yace Ameen ya rabbi.

Ranar suna yaro ya ci suna Abubakar suna kiran shi da Khalifa, ba ayi wani shagali sosai ba sakamakon maijegon lafiya bai ishe ta ba, sun samu kaya kam sosai ta ko ina sai son barka yaro yayi goshi.

Kullum Dr. Nusayb yana mak'ale da yaron shi ba k'aramin so ya ke masa ba kacokan zai kashe lokacin shi saboda d'an kamar tsoka d'aya a miya...........

*Jiddah Samusa✍🏻*
[8/12, 10:18 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*7⃣4⃣

TWO WEEKS LATER.......

Kwance yake bisa gado rungume da d'an shi yayin da Ummi ke zaune a gefen shi, ta dubesa tace, "kace akwai maganan da zamu yi ina saurarenka" a hankali ya kwantar da Khalifa, sannan ya rik'o hannunta ya murza a hankali.

Can ya nisa yace, "inason duk abinda zan fad'a miki ki d'auke shi a matsayin kaddara inaso kiyi duba da irin ni'imar da Allah ubangiji yayi mana ba abinda muka nema muka rasa sannan ya azurta mu da yaro wanda wani ma yana nema mai bai samu ba dan haka Allah yana hana wani abun wa bayinsa dan yaga ko cinye wannan jarrabawan da ya mishi dan haka ina so ki sa wa ranki nutsuwa Allah ne ke yin komai, kiyi hakuri a halin yanzu mahaifar ki an cire sakamakon matsala da kika samu".

K'wace hannunta tayi ta tashi dafe da k'irji tana hawaye, cikin rawan murya tace, "kanason kace min bani da mahaifa yanzu sannan kana nufin bazan k'ara haihuwa ba innalillahi wa inna ilaihir raji'un".

Rik'o ta yayi ya zaunar da ita yace, "kiyi hakuri Amina haka Allah Ya tsara mana Khalifa ne kad'ai yaron mu a duniya", cikin zafin rai tace, "yaronka ko nawa? kai ko yau kaso zaka k'ara aure ka haihu kai baka da damuwa ta fashe da matsanancin kuka".

Rungume ta yayi yana shafa bayanta har ta nutsu sannan ya d'ago ta ya share mata hawayenta yace, "inaso ki sani ummi komai da kika gani nufin Allah ne zancen zan k'ara aure ko bazan k'ara ba duk wannan na Allah ne Shine masani kawai dai mu 'yan adam kowa na da irin tsarin shi na rayuwa wani ya tafi daidai ko kuma a samu akasin haka, saboda haka sanin kanki ne bani da ra'ayin auren mace sama da d'aya duk yadda na kai da son yara da burin ki cika min gida da yara ba yadda zanyi dole na rungumi kaddarar da Allah ya d'ora mana, yawan yara ba shine ba, albarkar su a ke nema sai ki ga yara dayawa amma duk ciki ba ya wuce mutum biyu ne na k'warai da haka kisa a ranki ina tare da ke cikin ko wani hali Khalifa ya isheni rayuwa har karshen rayuwata wallahi, in kin ga nayi aure toh dama haka Allah ya tsara a rubuce ta ke.
Chapter 15 · 0% Book details