← Book details Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 17

Sashe 8

Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yasa d'an makulli ya bud'e k'ofar parlourn suka kutsa ciki, bai ce mata uffan ba ya haye upstairs, ganin haka ta nemi kujera ta zauna.

Yana shiga d'akin shi ya cire kaya ya shiga wanka bayan ya fito ya shirya kansa cikin kananan kaya sun amshi jikinsa sosai.

Tafe yake yana waya da Aunty Fatima yana shaida mata sun iso amma suna gidan shi tukun a haka ya iso cikin parlourn, ummi ta dube shi daga sama har k'asa tace,

"Amma dai ya Nusayb kasan ba nan gidan muka yi zanzo ba, kawai zaka wani tashi ka kawo ni gidanka gashi yunwa nake ji" .

Ya kafe ta da ido yana kallon bakin ta yadda take magana gwanin sha'awa, ji yake kamar ya cafko ya tsotsa, ya lumshe ido sannan ya bud'e yace toh uwar azarbabi, nan d'in cinye ki za ayi?

"Ni bance ba"

Toh in kina son na kaiki, maza ki tashi ki je ki sama mana abinda zamu ci a kitchen.

Da sauri ta ajiye gyalen ta, ya nuna mata kitchen ta wuce a gurguje ta dafa musu indomie da kwai ta kawo ta ajiye mishi ta kawo ruwa sannan ita ta zauna ta ta ci.

Suna kammala wa ya d'auke ta ya kaita gidan Aunty Fatima dake Asokoro.

Yana parking da gudu ta shige cikin parlourn ai ko tana arba da aunty fati ta fad'a kanta, Nusayb da shigo yace a ranshi ke dai Amina bansan yaushe zaki girma ba ki daina guje-guje.

Aunty Fatima ta dubesa a'a autan Mummy ya ka ja ka tsaya kuma, yace ai shareni kika yi dan kin samu wannan uwar rawan kai d'in, ni kinga tafiya na ma ya ajiye trolleyn.

Haba autan Mummy yi hakuri shigo kaji, a'a ki bari "hospital" zan wuce yanzu, zanzo gobe muyi magana.

Toh shikenan ba matsala.

Yasa kai ya fice...........

*Jiddah Samusa✍🏻*
[12/20, 6:57 PM] ‪+234 806 161 2054‬: [8/5, 8:06 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*4⃣9⃣

Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya ta ji kunya, yau Asabar ta ke k'ofar gidan Alhaji Umar Bashir da kewayenta cike take da jama'a daga sassa daban-daban na nijeriya da k'asashen ketare, taro ne na manya-manyan k'usoshin nijeriya abun ba a cewa komai.

Da misalin k'arfe goma na safe dubban jama'a suka shaida d'aurin auren *Nusayb Umar Bashir* tare da *Amina Abubakar Bashir* akan sadaki dubu d'ari.

Fusk'ar kowa in ka duba zaka ga yana cikin farin ciki bare uwa uba Dr. Nusayb abun ba cewa komai, sanye yake cikin farar shadda d'inkin babban riga yayi kyau har ya gaji, bakin shi kamar gonar auduga, kyauta ya rink'a yi wa jama'a kamar bai san zafin naira ba haka b'angaren mahaifinsu ta kasance.

A cikin gida Ummi ba abinda take sai aikin kuka tun Falaq da sauran k'wayenta suna zolayar ta har jikin su yayi sanyi da lamarin ganin yadda ta ke kuka gwanin tausayi dakyar a ka samu tayi wanka wannan ma da taimakon Aunty lubna ne, a ka shirya ta cikin leshi riga da siket "red color" da ratsin fari tasha zubi gaban rigan ga stones "multicolor" da aka jera su rasss, tayi kyau na k'arshe ni kaina Jiddah sakin baki nayi ina kallonta ta.

A sukwane Dr. Nusayb ya shigo gidan yana ratsa mutane abokan wasan shi sai tsokalar sa suke amma ko a jikinsa, har sai daya dangana da inda Aunty Fatima take sannan ya ja birki ya rungumeta hawaye kawai ke ambaliya a fuskar shi duk ya tsorata ta.

Yace, "Aunty yau bansan wani irin farin ciki nake ciki ba, yau Allah ya mallaka min abinda na jima ina rainon shi ina begen sa wanda ba dabara na bane ya bani na rasa wani irin godia zanyi wa ubangiji na".

Aunty Fatima ta d'ago shi tare da goge masa hawayen shi tace, "haba autan Mummy be a man mana yau ba ranar kuka bane yau burin ka ya cika wanda na jima ina taya ka addu'a dan haka ba abinda zamu ce sai godiyan Allah"

Yayi murmushi yace, "nagode my sweet sis Allah ya barmu tare" ya bata peck sannan ya tashi ya fice...............

*Jiddah Samusa✍🏻*
[8/5, 9:13 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*5⃣0⃣

Da dare misalin k'arfe bakwai, Ummi sanye cikin "super exclusive" ruwan goro da yalo ta d'aura lifaya akai, zaune take cikin dangin mahaifiyar ta suna mata nasiha sai kuka ta ke daga k'arshe duk suma suka fashe da kuka saboda tuno 'yar uwarsu da suka yi yau ga d'iyarta har ta girma za'a kai gidan miji amma babu ita dakyar suka rarrashi kansu sannan suka sadata da d'akin Mummy daganan Mummy ta kamata zuwa sashen Daddy inda suka tarar da Nusayb ma ya iso.

Daddy ya musu fad'a sosai wanda yawanci wa Nusayb yayi ganin shine namji Mummy ma ta d'ora da nata Amarya Ummi dai sai kuka, Nusayb jin kukan nan yake har ranshi, ji yake kamar ya kamota ya rungume ta ya lallashi abarsa amma ba hali.

Mummy ta k'ira Aunty Fatima da wata babarsu suka fita da Ummi zuwa harabar gidan yayinda motoci ne a cike da wurin, Abdullah yana hangosu yayi maza ya bud'e gambun mota suka sanya ta sannan suka shiga, suma sauran jama'a duk suka nemi motoci suka shiga a ka wuce da amarya gidanta dake GRA, gida ne na gani na fad'a masu karatu na barku da wannan ku canka, dan in zan tsaya fad'ar tsaruwanta toh page ma yayi kad'an.

K'arfe takwas da rabi a ka shirya dan tafiya "Dinner", wayyo karku so ku ga Amarya tasha "wedding gown" mai kyan gaske an tsara mata kwalliya abun dai ba a cewa komai.

Falaq da sabreen ne suka sanya ta tsakiya har bakin mota suka rako ta, falaq ta bud'e mata ta shiga, wani k'amshi ta ji ya buge ta, ta kai duba gefen ta taga Nusayb ne, shima yayi kyau Sosai, Abdullah ne ke jan motar sai matar shi a gefen sa faiza da d'ansu haidar, Abdullah ya waiwayo yace, "amaryar mu kinsha k'amshi" ta harare shi yayi dariya yace, "a yi hakuri bani na kar zomon ba"...........

*Jiddah Samusa✍🏻*
[8/5, 9:57 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*5⃣1⃣

Kai tsaye "Hotel 17" suka nufa inda za a gudanar da dinner d'in sun samu wajen a cike dan duk an tafi amarya da ango ne kawai ake jira, bayan Abdullah yayi parking duk suka fito Nusayb ya rik'o hannunta yayin da abokan ango dana amarya suka jeru a bayansu a gaban su kuma Sabir ne da Zareefa a matsayin "flower boy da flower girl"

Daga bakin k'ofar an malala jan carpet har zuwa wajen da aka tanada dan zaman ango da amarya, tafe suke a hankali D.J ya saki kid'a mai taushi da ratsa zuciyar masoya yana tashi, yayinda flower boy da flower girl hannun su rik'e da container flowers ce a ciki suna watsa wa a hankali da haka har aka raka su mazaunin su.

Bayan an natsa ne M.C ya fara k'iran 'yan "high table" hatta yaya babba sudais ba a barshi a baya ba shima yaje, daganan kuma a buk'aci babban abokin ango ya fito dan ba da takaitaccen tarihin ango, Abdullah ya fito ya bada cikin k'warewa, bayan ya gama sai a ka nemi ta Amarya ma, Falaq bata yi sanyi a gwiwa ba ta fito ta bada tarihin amarya had'e da d'abi'unta.

Nan aka saki kid'a a buk'aci ango da amarya su fito sannu a hankali suka iso filin nan suka fara rausaya wa zo ku ga yadda ake b'arin dollers ni jidda har na tsorata zan gudu kamar an ce ki waiwaya kawai sai na hango d'aukacin mutanen Jiddah Samusa's novels a gefe kuma ga na billy giro novels da maman uthman novels sannan ga 'yan Haucy's kitchen wanda su suka d'auki nauyi dukkan abubuwan ci da na sha, sai a sannan nayi hamdala na k'arasa wajen su.

Biki tayi biki can na hango cardypinky, daughter Amna, feenan mu, babien baba, ummul Islam, laina, binta Musa, a tsakiyar fili suna tik'ar rawa sai lik'i a ke musu.

Bayan an gama raye - raye aka buk'aci kowa ya je ya d'ebi abinda yakeso yaci, tashin farko wasu daga cikin mutanen mu ne suka tashi kamar su momman farhana, ummin ustaz, janan, faty makarfi, jidda kauji, aunty yana, mrs bawale ummu hilal da dai sauran su sai ciko plates suke har da k'ara komawa na dubi kawata dake gefe na nace ayusher mohd kin ga wad'annan mutane zasu samu jin kunya gashi dai gayyar sod'i su ka yo amma duk sun zage, tayi dariya tace, "rabu dasu su yagi rabon su irin wannan didima haka" 😜

Ba a tashi a wannan dinner ba sai misalin k'arfe 2 na dare sannan aka kwashe jama'a a ka mayar............

*Jiddah Samusa✍🏻*
[12/20, 6:57 PM] ‪+234 806 161 2054‬: [8/4, 3:01 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*4⃣2⃣

Dukkansu suka fito dan yi mata rakiya, Sabir na rik'e da trolley yayin da Zareefa na mak'ale da Ummi tana kuka sai ta bi su.

Kawar da kai yayi kamar baisan da zaman su ba, ya bud'e boot yayi alama da hannu wa Sabir yasa trolley d'in aciki da sauran kayyayakin tsarabar ta ya zaga ya shiga ya zauna ganin hakan Ummi ma ta bud'e gefen mai zaman banza ta zauna.

Aunty Fatima ta lek'o kanta ta cikin motar tana dariya k'asa-k'asa tace, "toh Autan Mummy Allah ya tsare sai mun zo jibi da Abban Sabir", ko uffan bai ce da ita ba ya fisgi motar da k'arfin gaske sai da goshin Ummi ya bugi gaban motar ta tsanyara ihu dan zafi.

Da sauri maigadi ya bud'e gate suka fice, suka d'au hanya, ganin kukan ta bai tsaya ba yasa ya gangara gefen hanya yayi parking had'e da janyo ta jikinshi da k'arfi har sai da ta tsorata ya matse ta sosai a tare suka sauk'e ajiyar zuciya mai k'arfi daga bisani yasa hannu ya mulmula mata goshinta da ya soma tashi ya rad'a mata a kunnen ta "kiyi shiru haka ya isa ban yi da niyyan cutar da ke ba kinji Amina".
Chapter 8 · 0% Book details