← Book details Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 17

Sashe 1

Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[12/20, 6:55 PM] ‪+234 806 161 2054‬: [7/14, 8:06 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page* 1⃣

A guje ta shigo cikin parlourn sai ji tayi ta bangaje mutum, bata ankara ba ta ji sauk'ar mari lafiyayyu a fuskanta, wani uban ihu ta saka had'e cewa "wayyo mummy zai kasheni" burgima ta ke tsakanin ta da Allah ta rik'e cikin ta,
Mummy step bibbiyu ta ke had'a wa ta sauk'o da saurinta ta nufi wajen ta d'ago ta, tace meya faru ne ummilolo? Tace na shigo kaina a k'asa ban lura da wancan k'aton sangamin ba, sai na buge shi, shine fa ya mareni guda biyu sannan ya fara k'wallo dani yanzu haka kayan cikina juyawa suke, ta k'ara sakin razanannen ihu, Mummy ta dawo da dubanta wajen Nusayb ta fara masifa haba Son, daga dawowanka zaka jawo min magana ko? Yarinya da bata tab'uwa shine zaka zo ka mata wannan d'anyen aikin toh nikam ba ruwana kai da ubanka in ya dawo

Nusayb dake gefe tun zuwan mummy ya saki baki da hanci galala yana kallon Ummilolo da tsananin mamakin ta na sharrin da ta k'ulla masa, daga bisani ya bud'e baki yace haba mummy akan wannan kuchaka 'yar k'auyen kike min fad'a

Kaci ubanka nace fad'ar Mummy kenan, yarinyar nan d'in ce kuchaka, k'anwar ka ce toh 'yar gidan baffan ka Abubakar

Nusayb ya k'walalo ido waje had'e da rik'e baki yace......

*Jiddah Samusa ✍🏻*
[7/14, 8:07 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page* 2⃣

Nusayb yace, Mummy kina nufin kice wannan Amina ce? K'warai kuwa Son ita ce, yanzu k'imanin watanta uku da dawowa wajen mu kenan, ya tab'e baki had'e da d'aga kafad'unsa, Mummy ta cigaba da cewa yarinyar nan tun jiya take d'aukin dawowar ka amma daga zuwanka zaka illata ta ko, wallahi baka dawo ba, in ka kuskura ka tak'ura wa yarinyar nan kasan sauran
Nan ta kamo hannun Ummilolo tace zo mu tafi baby na, Ummilolo ta tashi tana d'ingisa k'afa, ta faki idon Mummy ta masa gwalo sai kuma ta fashe da kuka, Da sauri Mummy tace menene kuma? Toh ba shine ba kuma yake harara ta

Mummy ta waigo ta balbale shi da masifa ta ja hannunta suka nufi d'aki,

Nusayb dake tsaye ya d'an murmusa dan shi dariya ma tafara bashi, daga bisani ya ja tsaki mtswwww! Sannan ya wuce d'akin shi

Mummy ta dubi Ummilolo tace maza kiyi wanka kiyi sallah sai kizo mu ci abinci, nan ta fara kiciniyar cire kaya tare da fad'in Mummy banason wannan mutumin ya cika kyau kamar aljani ga baya dariya, yaya sudais ya fishi fara'a, Mummy tace toh uwar iyayi zaki tsaya surutu ne ko kuwa zaki shiga wankan? Ta rik'e kunnenta yi hakuri yanzu zaki ga aiki da cikawa tayi bathroom da gudunta......

*Jiddah Samusa✍🏻*
[12/20, 6:55 PM] ‪+234 806 161 2054‬: [7/15, 9:44 AM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page* 3⃣

Bayan ta fito a wanka, kai tsaye sallah tayi sannan ta isa gaban dress mirror wanda yananan shak'e da kayan shafe-shafe, tayi wajen minti arba'in tana kwalliya, fuskar nan ta sha fente-fente a dole sai tayi kwalliyan zamani,,

Sannan ta nufi wardrobe ta zak'ulo wata 'yar kanti riga da skirt "milk color" mai ratsin "coffee color " an mata ado da stones golden, ta saka, sai kuma ta d'auko wata d'ankwalin kayanta na atamfa ta kashe d'auri dashi

Ta k'ara duban kanta a mirror tana juye-juye ita a dole tayi kyau sannan ta kama hanya don fita daga d'akin tana wak'e wak'en ta, har ta isa ta murd'a handle d'in kofar sai ta tuna bata shafa turare ba, da sauri ta dawo ta feshe jikinta da turare mai kamshi gaske sannan ta fito tana rangwad'a kwankwason nan kamar zai karye

Kai tsaye "dinning area" ta nufa, sai washe baki take, ta iske Mummy da Nusayb bisa dinning table suna cin abinci,

Nusayb kallonta yayi daga sama har k'asa a ranshi yace, wannan tana tunanin har yanzu a k'auye take ne da take irin wannan kwalliya? ya k'ara duban fuskanta yaga sai wani fari da ido take, bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba.......

*Jiddah Samusa ✍🏻*
[7/15, 9:49 AM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*4⃣

Dariya yake sosai har da har da rik'e ciki, Ummilolo dake tsaye ta cika tayi fam ai sai ta sa kuka tana bubbuga k'afafunta, Mummy ta gimtse dariyar ta tace, haba "Nusayb meye haka zaka tasa yarinya a gaba kana dariya", yi hakuri Mummy na daina, ya rufe bakin shi yana cigaba da dariya k'asa-k'asa, Ummilolo da ta lura dashi tuni ta fasa ihu, wanda yasa dukkansu tsorata,

Nusayb ya daka mata tsawa, a take annurin fuskar shi ta gushe ba shiri ta nutsu ta fara mitsike ido, ya balbale ta da fad'a, Mummy tace a ranta "maganinki ma sai shi da ni ce yanzu ai da bakiyi shiru ba" daga bisani tace rabu dashi zo ki zauna ki ci abincin ki

Ta zumb'uro baki ni na k'oshi, sauk'ar rank'washi ta ji a kanta, Nusayb yace wuce yanzun nan ki ci abincin kafin na b'ab'ballaki, da sauri ta ja kujeran ta zauna, Mummy tayi serving nata ta d'ebo abincin a cokali ta nufi bakin ta dashi

Nusayb yace, Mummy "mai nake shirin gani abincin ne sai a baki za a bata" Eh mana kasan haka hajiya ta sabar mata, yace toh tunda ba tsohuwar ai sai ki zage kici da kanki, oya k'arbi cokalin

Ummilolo tasa hannu ta k'arba tana tsiyayar hawaye, ci take tana yatsina fuska kamar mai cin magani, tanayi tana zubarwa bisa table, Nusayb duk yana kallon ta yace a ranshi "dole na gyara miki zama Amina"

Ya ture plate d'in gabanshi ya tashi ya nufi parlour....

*Jiddah Samusa ✍🏻*
[12/20, 6:55 PM] ‪+234 806 161 2054‬: [7/15, 8:20 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*5⃣

ASALIN SU.....

Mallam Basheer Babariko yana da macen aure guda d'aya mai suna Amina, asalinsu 'yan wani k'auye ne watinani dake k'aramar hukumar Nangere ta jihar yobe, sun kasance yarensu karai-karai, sunyi auren soyayya tun saurayi da budurwa, inda Allah ya albarkace su da samun yara biyu duk maza tsakanin su ya kai shekara takwas daganan haihuwan ta tsaya

Babban sunan shi Umar k'aramin kuma Abubakar amma ana kiransa da bukar, sun samu tarbiya daidai gwargwado daga iyayensu, Umar ya kasance ma'abocin son karatun boko sab'anin Bukar da ya tsani boko,,

Ganin kwazon da umar yake dashi bayan ya gama "primary school " yasa dagacin garin su ya masa hanya ya samu gurbin karatu a "Government College" dake maiduguri, ba k'aramin farin ciki yayi ba haka ma iyayen sa,

B'angaren Bukar kuwa ya duk'ufa ne a karatun addini inda Allah ya taimaika mishi inda ya haddace Qur'ani maigirma da sauran littatafai. Sannu a hankali umar ya kammala karatun shi na gaba da primary cikin ikon Allah ya samu "scholarship" a k'asar "Ukraine" suka bashi "Business administration" bai dawo k'asar sa ta haihuwa ba sai da ya kammala har "masters" sannan ya dawo bayan ya fito da sakamako mai kyau.....

*Jiddah Samusa ✍🏻*
[7/15, 9:07 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*6⃣

Iyayen shi ba k'aramin farin ciki suka yi ba hatta d'aukacin mutanen k'auyen ya basu sha'awa kowa ya taya shi murna, kowa zuwa yake kallon shi abunka ga k'auye, ba a d'auki dogon lokaci ba ya samu aiki a "NBTI" a reshen su dake jihar kano

Ya fara aiki cikin sa'a cikin lokaci k'alilan ya had'u da 'yar ogansu mai suna maryam yarinya mai hankali da nutsuwa suka fara soyayya bai yi k'asa a gwiwa ba ya samu mahaifansa da zancen inda ya tarar dana Bukar ma har an nema masa auren wata yarinya mai suna Fase yar garin Buzu ce, sunan shi ya b'ata daga Bukar ya koma "Bukar na Fase"

Mahaifinsu yayi matu'kar farin ciki jin cewa ya samu matar aure dan kullum abun yana ranshi dashi yake kwana yake tashi toh abunka ga ba zamanin waya ba, bare yake nemansa da
zance

K'anin Mahaifinsu da dagacin garin da wasu dattijai biyu suka je neman masa auren ba b'ata lokaci aka basu har rana aka sa nan da wata d'aya saboda gari ba kusa ba

Anyi aure lafiya inda ya tare da matarsa a unguwar "sharad'a phase2", gida ne madaidaici sai shegen kyau da tsaruwa abunka ga 'yan boko, Bukar na Fase kuwa sunanan a can Watinani amarya ta tare a cikin gidan suna zaune tare da surukanta suna zaune lafiya, dake baaba Amina mace ce da ba ruwanta da harkokin yara....

*Jiddah Samusa ✍🏻*
[12/20, 6:55 PM] ‪+234 806 161 2054‬: [7/16, 9:38 AM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*7⃣

A kwana a tashi ba wuya Allah ya albarkaci Umar da Maryam da 'ya'ya uku Sudais, Fatima da Nusayb, B'angaren Bukar na Fase kuwa har yanzu Allah bai basu haihuwa ba, duk da hakan ba abinda ya canza a zaman su, sai ma wani sabon tattali da suke nuna ma junansu,

Kwatsam Mallam basheer ya tashi da ciwo wanda yazo da k'arar kwana ya cika, sun ji mutuwan sa ba kad'an ba hatta d'aukacin mutanen k'auyen sun girgiza saboda Babariko mutum ne mai halin dattako a duk inda yake dattijo mai wadatan zuci da hangen nesa, bayan anyi arba'in Umar ya buk'aci mahaifiyarsu da K'anin sa akan su koma kano wajen shi da zama, amma fir Baaba Amina tace batasan wannan zancen ba, a gidan mijinta zata zauna har ita ma lokacin ta ya risketa
Ganin hakan Bukar na Fase ma yace ba inda zai je ya bar ta, haka umar ya tattara da iyalanshi suka koma kano,

Ba ajima ba aka masa "transfer" zuwa kaduna inda suka tare a "malali" ya k'ara kud'i ya mallaki kamfani wajen biyar, ya zama babban Alhaji ya kai mahaifiyarsu da k'aninsa har da dagacin garin suka sauk'e farali

Cikin ikon Allah Fase ta samu ciki kowa ya tayasu murna haka suka ta rainon cikin har ya isa haihuwa ta samu d'iya mace fara sol da ita gata kub'ul-kub'ul da ita a ta ke a ka nad'a mata "baturiyar karai-karai".....

*Jiddah Samusa ✍🏻*
[7/16, 1:11 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*
Chapter 1 · 0% Book details