← Book details Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 17

Sashe 6

Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gogan kamar bai san mai ake ba cin abincin shi kawai yake tare da wasu nazari.

Ana kammala cin abincin Daddy suka musu sallama akan Insha Allahu gobe zasu dawo, suka rakasu bakin mota sannan suka tafi.

Ummi duk baki ya mutu ganin su Daddy basanan an barta da mai cin zalin ta,

Nusayb ko sai wani fara'a yake wanda bata tab'a gani a fusk'arsa ba, yace "mhmm yarinya tayi rashin hankali sai na mai da ita pepper soup".

Ummi ba tace komai baki ya mutu.

Nusayb ya samu Asabe yace yau bana buk'atar kiyi girki, Ummi za tayi dan haka ki kiyaye kar naji ko nagani.

Toh yallab'ai ba damuwa, amma kana ganin ummi za ta iya kuwa? Kasan ta da son jiki.

Nusayb yace, ai ko ita ce mage sarkin son jiki yau sai ta aikatu, in aka barta haka ai ba gata bane.

Hakane yallab'ai kayi gaskia dan duk gatan mace in bata iya girki ba toh akwai matsala dan d'akin miji zata je. Mai zata dafa ma ne?

"Sakwara da egusi soup" cewar Nusayb.......

*Jiddah Samusa✍🏻*
[7/24, 6:46 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*2⃣6⃣

Keeeeee! Na'am inji ummi, zo nan da saurin ta tazo tace gani Ya Nusayb likita bokan turai,

Yace, mhmm! Ke kika sani, kinsan mai nakeso kimin?

A'a, inaso ki dafa min sakwara da miyar egusi.

Ummi ta zaro ido had'e da nuna k'irjinta ni ya Nusayb? Ba ga Asabe ba.

Nusayb yace, ke nake buk'atar ki min in kika k'i kuma ki ji na jaki,kuma ban amince Asabe ta sa miki hannu ba.

A'a ba a kai ga haka ba ai zanyi ma, bari naje nayi wanka nazo na fara had'a wa, tana shiga d'aki ta d'auki wayar ta, ta k'ira layin Falaq, tana d'auka tace "Dan Allah besty ki zo ki tayani yin abinci a ya Nusayb nasan ke kin iya kuma in zaki shigo ki shigo ta balcony sai mu had'e a madafa" nan ta katse layin.

Ta shiga wanka a gurguje ta fito, ta shirya cikin wani material riga da skirt "pink color" mai ratsin "blue" da adon stones "silver" a jiki ya zauna d'as a jikinta sannan ta fito.

Tana shiga madafa ta fere doya ta d'ora a wuta ta ja ta tsaya dan batasan abu na gaba da zatayi ba, cikin ikon Allah Falaq ta fad'o nan ta taimaika mata, amma tace sai dai ita ta daka sakwara, ummi tace ba matsala zanyi ai kin min mai wahalan gashi nima na koya.

Nan ta fara daka sakwara hannunta duk yayi jaaa abunka ga farar fata bai daku sosai ba ma haka ta mulmula tasa a flask, sannan ta je ta jere mishi a table.

Ta zuba musu nasu suka ci ba laifi miyar ta d'an yi sai dai barkono , tace toh yanzu ki gudu gida saboda kar ya ganki, falaq tayi dariya tace shegiya mutuniyar" na tafi.

*************

Zaune yake da misalin k'arfe uku na rana bisa dining, ummi tsaye a kanshi tana zuba masa abinci, ta gama zuba wa zata tafi, yace dawo ki zauna, ba musu ta dawo ta zauna ta zuba tagumi tana jiran sakamako.

Ci kawai yake amma ba dan ran shi ya so ba dan sakwarar ba ta daku ba ga miyar barkono daga karshe ya hakura ya ture plate d'in sannan ya kora ruwa.

Ya dubeta fuska a had'e yace wannan wani irin abinci ne? Haka kika ga ana yi a gidannan?

Ummi tace, yanzu meye laifin abincin nan ya Nusayb ai nayi kokari ma wallahi, ba ka ga irin wahalar da na sha ba, dubi hannu na fa, ya dubi hannunta gabakid'aya yayi jaa, sai yaji ba dad'i tausayin ta rufe shi, amma sai ya fuske yace toh naji nan gaba ki kula, ta murgud'a baki yayi kamar bai ganta ba, yace a ranshi "Amina duniyan Allah"

*Jiddah Samusa✍🏻*
[7/24, 8:35 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*2⃣7⃣

Ya Nusayb ummi ta anbata cikin d'ari-d'ari, meye? Ya furta cikin halin ko'in kula, ummi tace dama tsarabar ce ko zaka bani.

Ya kafe ta da ido yace, wai ke wani irin naci ne dake? Ki je ki d'auki duka ledojin tun kafin ki cinye ni d'anye.

Tasa ihu ta ruga da gudu d'akin shi ta d'auko, kai tsaye d'akin ta, ta wuce ta zazzage kayan bisa gado a fili ta furta

"Wow!"

Ta fara d'aga wa tana dubawa, ya sai mata dangin kayan kamshi da na shafe-shafe, sai wata abaya 'yar ubansu ga tarkacen su chocolate kaya dai son barka, ta fita ta mishi godia.

*************

Da dare tana zaune ita kad'ai a parlour tana kallo, Nusayb baya nan ya tafi wajen Abdullah.

Sai goma da rabi ya shigo gidan, ya iske ta ta nad'e cikin kujera tana rik'e da cikinta duk ta galabaita, da sauri yayi kanta yana tambayar mai ya same ta, ba amsa, can ya tuna da lokacin period nata yayi ashe.

Ya sunkuce ta ya kaita d'akinta, sannan ya zo ya kira Asabe ta zo ta taimaika mata ta shirya, bayan wasu mintoci ya koma d'akin tare sa kayan aikin sa.

Yasa Asabe ta kawo mishi ruwa, ya b'alle maganin ya bata sha ba musu dan har jikinta rawa yake, wajen Allura ne a ka sha daru dakyar ta bari ya mata sannan ya d'aura mata "drip" ya ja bargo ya d'an lullub'a mata, ya dubi Asabe yace sai ki kwana tare da ita, daganan yasa kai ya fice

Haka dai al'amura ya ta gudana bayan su Daddy sun dawo Washe gari shi ma ya koma bakin aikin sa.......

*Jiddah Samusa✍🏻*
[12/20, 6:57 PM] ‪+234 806 161 2054‬: [8/1, 4:14 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*3⃣4⃣

Isar sa "National Hospital" ke da wuya ya had'u da Dr. Dangana, yace, "Alhamdulillah wallahi naji dad'in zuwanka Dr. Nusayb, ga can wata mata an kawo haihuwa toh yazo da matsala dole sai an mata aiki, nasan kuma kai baka da matsala da ikon Allah dan haka muje".

Dr. Nusayb yace, "matsala ta da kai yanzu shigo wa ta fa ko office ban je na zauna na huta ba, da ba nan da dawa zaka yi?", tunda ga ka ai shikenan dan Allah kayi sauri ceton rai ne.

Cikin ikon Allah sun samu nasara wajen yiwa matar aikin.

Dr. Nusayb bai bar asibitin ba sai k'arfe goma na dare saboda patients sunyi yawa kowa shi yakeson gani saboda k'warewarsa a aiki.

**** **** ****

Washe gari da misalin k'arfe biyar da rabi na yamma ya isa gidan Aunty Fatima, da sallamar shi ya shiga cikin babban falon yayin da ya zauna bisa k'ayattatun kujerun da sukai wa falon k'awanya.

Ba kowa cikin falon can ya ciro wayar shi mai tsadan gaske wanda ni kaina Jiddah ban tab'a cin Karo da irin ta ba sabon yayi ne, yayi dialing numbern aunty fatima, bugu d'aya ta d'auka tace, "Autan Mummy ya akayi ne?" yace, "gani fa cikin gidanki naji shiru kuma ko haniyar yaran babu".

Tace, "laaaaaaa ganinan bari na sauk'o".

Aunty fatima da mijinta mai suna Senator Albdulkarim Marafa, suka iso cikin falon, nan ya bawa Dr. Nusayb hannu suka gaisa tare da tambayoyin harkokin yau da kullum.

Ya dubi Aunty fatima yace, "ina yaran fa?"

Tace, "Sun tafi Millennium Park", ya zaro idanunsa ba dai har da Amina ba?

Aunty Fatima tace, "ai itace shugaban tafiyar ma dan ita ta matsa".

Dr. Nusayb ya mata wani irin kallo, Abban Sabir yayi dariya yace, "a'ah Dr. Lafiya kuwa irin wannan kallo, ko dai akwai abu a k'asa ne?

Dr. Nusayb zaiyi magana sallamarsu ta katse shi........

*Jiddah Samusa ✍🏻*
[8/1, 4:50 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*3⃣5⃣

Sanye take cikin wani material lace "lemon green" d'inkin riga da skirt, ya amshe jikinta sosai ya d'an kamata, sai d'an bingil gyale da ta yafa.

Bayan ya k'are mata kallo ya kawar da kai, wani kishi mai zafi ke nuk'urk'usar shi, Allah ne kad'ai yasan irin mazan da suka ganta a haka.

Ummi tace, "ya Nusayb ina wuni" ya dubeta ya watsar ba tare da ya amsa ba, ganin hakan yasa ta yatsina fuska a ranta tace, "mutum sai bakin hali kar ka amsa mana damuwar wa" ta tashi ta ja hannun zareefa d'iyar Aunty fati suka yi ciki.

Dr. Nusayb ya dubi Sabir yace, " My son zo ka d'auki mimi ku je sama" da gudu ya zo ya kamata suka haura upstairs.

Falon ya rage daga Nusayb sai Aunty Fatima, dama tuntuni mijinta ya fita, ya dube ta cikin b'acin rai yace, "haka mukayi dake Aunty? Meyasa zaki barta ta fita? Kuma ko zata fita ki duba irin tufafin dayake jikinta duk ya matse ta, ko wani Tom n Jerry ya gama ganinta meye amfanin haka"

Nasani Autan Mummy, amma kasan ta nuna tanason fita zaga gari ai bai kamata na hana ta ba, zata ji ba dad'i.

Amma aunty, kinsan dai yadda nake kishi Amina, ina sonta ina kaunar ta har jinin jikina, na d'auko ta na kawo wajenki ba dan komai ba sai dan ta zama na tana kusa dani wallahi, duk lokacin dana so ganin ta zanzo na ganta, gaskia banji dad'i ba.

Aunty Fatima tace, "toh in ban da abunka Dr. Wannan wani irin *SALON K'AUNA* ce? kana k'aunar abu a ranka amma ka tsaya zurfin ciki, baka tunanin wani yazo ya ma shigar sauri? Kuma in kana gadarar kai d'an uwanta ne dole ta soka, kana ganin Daddy zai amince ne? Ba zai tab'a mata dole ba gara tun wuri ka cire wannan ra'ayin naka kasan abinda kake ahto................

*Jiddah Samusa ✍🏻*
[8/1, 5:23 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*3⃣6⃣

Dr. Nusayb yace, "Akwai lokacin da nake jira da zarar yayi insha Allah zan sanar mata".

Ahto da yafi maka.

Yace, "Aunty please k'ira min ita" tace, "toh Autan Mummy baban soyayya" duk suka k'yalk'yale da dariya sannan ta tashi ta nufi d'akin su, ta iske Ummi kwance a gado tana game a wayar ta zareefa na gefen ta.

Ta sa baki tace, "Ummi ki zo yayanki yana kiranki tana gama fad'in haka ta juya".
Chapter 6 · 0% Book details