← Book details Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina fatan kin gamsu da bayanaina, cikin sanyin jiki ta gyad'a mishi kanta tana mai k'ura wa Khalifa ido a ranta tace, "shikenan kai ma haka zaka rayu kai kad'ai bazaka San dad'in d'an uwa ciki d'aya ba kamar ni.

Tun daga wannan ranar ta d'auki son duniya ta d'ora ma Khalifa ko kuka yake itama haka zata sa shi a gaba tana kuka inna mairo k'anwar mahaifiyar ta dake zaune da ita tun bayan suna ta rik'a mamakin ta............

*Jiddah Samusa✍🏻*
[12/20, 7:01 PM] ‪+234 806 161 2054‬: [8/12, 5:49 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*7⃣1⃣

Cikin muryar shagwab'a tace Daddy na ina wuni, b'angaren Daddy ya amsa da lafiya k'alau mamana ya jikin kuma? Ummi tace, "da sauki Daddy, yaushe zaka zo na ganka ne?"

Mamana inason zuwa na duba ki amma yanayin da kike ne da na ganki sai tausayin ki ya rufe ni ga wannan yaro yak'i kawo ki gida ki haihu, Dafatan dai yana kula dake? Ummi tace, "laaa Daddy karka damu yana kula dani sosai ba wani matsala" nan dai sukai ta hira daga bisani suka ajiye waya.

Doorbell suka ji, Zareefa ta bud'e sai ta ga maman ta aiko ta rungume ta tana mata sannu da zuwa, Ummi tace, "sannu da zuwa Aunty" yauwa mai ciki ta fad'a tana dariya, ummi tace, "ke ko aunty bari ya Nusayb ya zo sai na fad'a masa" tana rufe baki kuwa sai ga horn d'in motar shi.

Aunty Fatima tayi dariya tace, "eyeeeee masu yaya", Zareefa tace Ammi ai d'azu nima ya duke ni wai na bar mishi mata ta kwanta a carpet, ohhh! Shi d'in ko cewar Aunty Fatima, Sabir dake zaune yayi dariya yace, "madallah uncle ya burgeni wallahi".

Ammi kin ganshi ko? cewar Zareefa, toh zaki fara ko ai kun had'u kai ne babba amma sai tsokala toh kar na k'ara ji, suka had'a baki yi hakuri Ammi.

Nan Ummi tasa Zareefa ya kawo ma Aunty abun motsa baki.

Da sallama ya shigo ya su Sabir suka masa oyoyo sannan ya nemi kusa da Ummi ya zauna, ta mishi sannu da zuwa, ya amsa, ya dubi Aunty Fatima ya gaishe ta had'e da cewa yau kin tuno mu kenan, bawani kullum ana cikin tunawa da ku ai.

Ta k'ara da cewa Autan Mummy nifa cikin ummi yana ban tsoro ka duba duk yadda ta canza, yace, "bakomai insha Allah zata sauka lafiya".

Toh Allah yasa, Ameen.

Sun sha hira sosai Sannan Aunty Fatima suka tafi, Zareefa ma tace sam sai ta bi su suka had'a suka tafi tare.

*****
Da dare misalin k'arfe goma sha d'aya tana kwance bisa k'irjinshi, rokon ta yake ta ba shi had'in kai dan yana cike da buk'arta amma fir ta k'i, ture ta yayi ya fita falo ya kwanta ya rasa mai ke masa dad'i.

Yana fita tasa kuka a fili tace, "nasan kayi hakuri duk da nasan kai mai yawan sha'awa ne nima ba laifi na ba ne" dukkan su ba wanda ya runtsa, ita ciwo ne ya dameta yayin da shi kuma abun dad'i.............

*Jiddah Samusa*✍🏻
[8/12, 6:34 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*7⃣2⃣

Ko da ya tashi da asuba bai nufi d'akin ba masallaci ya wuce daganan sai da ya dawo ya iske ta numfashi sama-sama ta ke fitar wa, da sauri ya d'ago ta ya tattab'a jikinta yaji dai body temperature nata is ok, ya k'ara gwada BP nata yaga ya haura har d'ari biyu da ashirin.

Cikin rud'u ya buga wa Dr. Dangana waya ya sanar masa situation da Ummi ke ciki nan ya bashi shawaran a mata C.S kawai a cire babyn dan shine mafita, yanzu a samu ya d'an sauko sai a mata aikin nan suka yi sallama.

Alwala ya kai ta tayi tazo tayi sallar a zaune, sannan suka shirya lokacin har k'arfe takwas tayi, bata tare da yace mata komai ba ya deb'i kayan da zasu bukata na jaririn da nata, tace, "ya Nusayb yunwa nake ji fa" yace, "a'ah ba zaki ci komai ba dan aiki za'a miki" nan taji gabanta Ya fad'i, kai tsaye asibiti suka wuce gado a ka bata a ka k'ara mata gwaji sannan a ka mata alluran bacci dan ta samu hutu.

Baccin awa goma tayi sannan ta farka numfashin ta kuma ya daidaita, Aunty Fatima sai sannu ta ke mata, "tace ya Nusayb fa" sun shiga tiyata sun kusa fitowa ma.

Ummi tace toh bari nayi sallah, nan ta rama sallolin da ake bin ta, sannan tace, "Aunty wallahi yunwa nake ji har zuciya ta hura ta ke" kiyi hakuri bazai yiwu kici komai ba cewar Aunty Fatima.

Nusayb da Dr. Dangana sai da wani Dr. Oliver suka shigo suka samu ta farka nan Dr. Nusayb ya k'ara gwada BP d'in cikin ikon ubangiji ya sauka dan haka nan suka shirya k'arfe takwas sai a shiga da ita tunda yanzu ba wata patient a kasa daganan sauran doctors d'in suka fita

Nan yayi waya ma nurse d'aya ta kawo mishi kaya da kuma katata, da kanshi ya sa mata rigar wajen sa katata sai da tayi ihu saboda zafi sai sannu yake mata nan ya zauna suna hira suna bata baki shi da aunty fatima.

Duk wannan wainar da ake toyawa basu fad'a wasu Mummy ba cewar su sai ta sauka tukun.

Bayan sallar isha'i aka wuce da ita "theatre room" anyi aiki cikin nasara an ciro yaro namiji d'an wata takwas da sati biyu sak ubansa bayan an gama shirya su a ka wuce da ita d'akin hutu hannun d'aya d'auke da jini d'aya kuma drip.

Doctors da nurses sai congratulations suke wa Nusayb bakin shi kamar gona auduga, sai a sannan suka shaida wasu Daddy murna kamar mai..............

*Jiddah Samusa*✍🏻
[12/20, 7:02 PM] ‪+234 806 161 2054‬: [8/14, 5:47 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*7⃣5⃣

Kwanci tashi ba wuya Ummi har ta gama wanka yayin da inna mairo ta koma gida, ba k'aramin kulawa suke samu ba daga mijinta yana iya bakin k'okarin shi dan ganin ya faranta mata rai yayin da soyayyar su ba wani rauni da ta samu face hab'aka da ta ke k'ara yi.

A yau suke shirin kai ziyara ma 'yan uwa inda lagos zasu fara zuwa gidan ya Sudais, maigidan ne ya shigo d'akin Ummi d'auke da Khalifa a hannun sa yana k'wala mata k'ira maman Khalifa wai baki gama ba ne, cikin muryar ta mai taushi tace, "nagama had'a mishi ruwan yanzu dama nakeson zuwa na karb'o shi" ya mik'a mata shi ta wuce bathroom dashi yayin da shi kuma yayi kwance bisa gadon ta.

Cikin bafo tasa yaron zata mishi wanka ta fara wanke kanshi zuwa fuskar shi garin wanke masa da ruwa ta sheka masa ruwa yabi kansa a gigice yaron yasa k'ara kan a ce mai ya shid'e, da gudu ta fito dashi tana kuka shima a birkice ya tashi ya nufi kansu ya karb'i Khalifa yana tambayan ba'asi tana dire wa ya wanka mata lafiyayyen mari, sannan ya bi ta kan d'an shi nan dan yaron ya dawo hayyacinsa.

Sai a sannan ya tuna da marin da yayi wa Ummi, hakuri ya rik'a bata akan bada sanin shi hakan ta faru ba cikin kuka tace bakomai, shi da kanshi yayi wa yaron wanka sannan ya bata ta shirya shi,zuwa k'arfe goma duk sun gama shirin su Dr. Dangana yazo ya kaisu Airport dan jirginsu sha d'aya zai tashi.

Sun sauk'a a lagos lafiya yayin da ya Sudais ya kwashe su ya kaisu gidanshi dake Victoria lsland sun samu tarb'a sosai daga wajen Lubna kwanan su biyu suka wuce kaduna cike da tsaraba da aka cika su dashi.

Tsakanin Daddy da Mummy sai ka rasa wanda yafi son Khalifa a cikin su kowa yafi son ya zamo yana mak'ale da shi, Kwanan su d'aya a kaduna ya kaita zaria gidan Falaq sun ji dad'in had'uwa matuk'a, Falaq ba k'aramin tausayawa ma Ummi tayi ba jin halin da ta tsinci kanta aciki, sun wuni a can sannan suka dawo kaduna kai tsaye gidan Abdullah suka isa acan suka rashe sai bayan sallar isha'i suka koma gida.

Washe gari kuma suka tafi garin buzu suka musu kwana 2 Dr. Nusayb ya cika su da kud'i da kayan abinci, a hanyar dawowar su kuma suka tsaya a kano gidan kakannin sa suka gaishe su sannan suka dawo kaduna, Washe gari suka koma abuja...........

*Jiddah Samusa✍🏻*
[8/14, 7:04 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*

*Na*

*©Hauwa Esmaeel Musa*

*Page*7⃣6⃣

Bayan shud'ewar wasu satittika bikin Dr. Dangana ya rage saura kwana biyu sam basu ga ta zama ba sai shirye-shirye suke ba kama hannun yaro.

Yau take rannan aure dubban jama'a suka shaida d'aurin auren *feenah* da *Dr Aliyu Dangana* a babban masallacin juma'a dake cikin birnin kebbi akan sadaki dubu hamsin.

Ana gama d'aurin aure a ka wuce da Amarya da babban aminiyarta Miemieangel da sauran k'awayenta sai 'yan uwa da abokan arziki zuwa abuja, kai tsaye gidan iyayen shi a ka kaisu dake wuse.

Da dare misalin k'arfe takwas a ka wuce dinner Dr. Nusayb na mak'ale da Ummin shi da yaron su sun bada sha'awa sosai wa jama'a' yan mata sai kawo masa hari suke amma basu samu shiga ba ummi tayi babak'ere a zuciyar shi, karfe goma a ka tashi sai a sannan a ka wuce da amarya ita kad'ai sai angon ta zuwa gidansu dake Utako.

**** **** ****
Misalin k'arfe biyar na yamma ta gama aikin girkin ta da komai ta turare gida da turare sai k'amshi ke tashi tayi wanka ita da Khalifa, ta shirya cikin Miniskirt sai wata 'yar top da tasa wanda cibiyanta duk a waje yake sai k'amshi suke ita da yaron ta suna jiran iso war maigida.
Chapter 16 · 0% Book details