← Book details Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 17

Sashe 17

Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Horn d'in motar shi ta ji dama al'adar shi ce muddin ya dawo sai ya mata horn ta zo ta tarb'e shi sannan su shigo ciki dan haka yau hakan ne ta kasance after dress dake gefen ta ta d'auko ta saka sannan ta rungumi Khalifa suka fito, yana hango su wani sanyi yaji ya ratsa shi fitowa daga cikin motar yayi ya rungume su baki d'aya sannan ya karb'i Khalifa ita kuma ta d'auko briefcase nashi da ledojin abubuwan motsa baki da ya kawo musu dan ba ya tab'a dawowa gida hannu banza.

Da shigar su ciki tayi wurgi da after dress dake jikinta, a tsanake ya kwantar da Khalifa dan kwalliyan ya tafi da shi sai daya sarrafa ta son ranshi sannan yayi wanka ya zo tayi serving nashi abinci.

Da dare bayan sun gama dinner suna zaune a falo Khalifa sai kananan kuka yake dakyar ya yi shiru wannan ma sai a k'irjinshi baban shi ne yana jijjiga shi a haka yayi bacci.

Ta dube shi ta turo baki yace, "yadai?" cikin muryar shagwab'a tace, "gaskia yanzu ka daina sona" cikin firgici ya zaro ido yace, "mai kika ga na miki wanda ya nuna na daina sonki wallahi ina sonki har kullum wutan sonki ruruwa yake cikin k'albina".

Tace, "toh ba kaine ba kullum kana rik'e da Khalifa ko bacci ne yana jikinka bayan kuma waje na ne yanzu kawai ka mayar dani gefe".

Dariya yayi sosai irin wanda bai tab'a yi ba ita kanta tayi mamakin shi, sai da ya tsagaita sannan yace, "wato dai kishi kike da Khalifa" bawani kishi ta fad'a tana dariya sanin kanka a jikinka na saba bacci amma yanzu ka yayeni, toh naji sai a raba biyu kowa gefe da gefe cewar Dr. Nusayb.

Dariya tayi ta mintsine shi mai zafi har sai da yayi k'ara ta mishi gwalo ai ko ya kwantar da Khalifa bisa kujera suka fara zagaye falon wai sai ya kamata daga karshe dai yayi nasarar kamata sai haki suke nan suka rungume juna suna musayar kalaman soyayya cikin rad'a................

*Jiddah Samusa✍🏻*
Chapter 17 · 0% Book details