Sashe 14
Salon Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan suka ciyar da junan su abincin suka k'oshi sannan suka shirya suka yi gidan Mummy, sun isa suka iske rasuwar mahaifin Mummy dattijon arziki mai dattako, Daddy yaji mutuwar sosai dan ubangidanshi ne nan aka bar tafiya zuwa kano akan gobe dan yanzu magrib ta kawo kai.
Dr. Nusayb ya bubbuga waya wa ya Sudais da Aunty Fatima ya shaida musu, duk suka ce gobe suna hanya sa had'u a can kano.
Daga gidan Mummy kai tsaye gidan Abdullah suka zarce a can sukayi magrib da isha'i suka ci dinner kafin su taho sai da Fa'iza ta ja ummi d'akin ta ta bata abubuwan karin ni'ima sannan suka musu sallama suka tafi, a hanya sai tambaya yake menene kuka fad'a da kuka shiga d'aki, tace, "ohhh! Sweetheart gulma ko toh bai shafe ka sirri ne", da haka dai suka isa gida cikin jin dad'i wannan dare ba k'aramin raya shi suka yi ba.
**** **** ****
Washe gari da sassafe misalin k'arfe shida suka d'auki hanyar kano cikin motar Daddy, Nusayb ne mai jan mota shi da Daddy suna gaba yayin da Mummy da Ummi ke baya.
Basu d'auki dogon lokaci bisa hanya ba suka isa, ganin Mummy gida ya k'ara rikicewa da koke-koke abun tausayi basu jima ba Aunty Fatima ta iso da iyalanta can kuma sai ga ya Sudais ma sun iso nan dai a ka ta ta'aziya wa juna.
Bayan sadakar uku duk suka koma suka bar Mummy akan sai anyi bakwai zata dawo..............
*Jiddah Samusa✍🏻*
[8/10, 9:48 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*
*Na*
*©Hauwa Esmaeel Musa*
*Page*6⃣8⃣
Bayan dawowar su daga kano da kwana 2 ya tattara Ummi suka koma abuja, hakan ba k'aramin dad'i ya mata ba ganin gata kusa da mijinta abun k'aunar ta.
Yau Asabar ba aiki, Ummi tayi matashi da cinyar Dr. Nusayb tana kwance, tuffa ne a hannunta tana ci ina gutsura shima ta bashi ya gutsura, can ya dubi k'irjinta yadda ya cicciko yace, "anya banyi ajiya anan ba kuwa?" ya fad'a yana shafa cikinta.
Tace ajiyar mai kuma? Bari dai na tabbatar tukun, ya d'ago ta suka yi d'akin shi yasa ta tayi fitsari ai ko yana dubawa ya ga tana da shigar ciki na tsawon wata biyu da sati uku.
Ihu yayi ya fara rawa daga bisani ya d'aga ta sama ya rink'a juyi dasu a cikin d'akin sannan ya dire ta ya rungumeta ya fara sumbatar ta sai da yayi son ranshi sannan ya barta.
Ya dubeta cikin ido yace, "Amina ta, mun kusa samun baby kina da ciki" ta zaro ido waje tace, "ciki wallahi tsoron haihuwa nake" yace, "haba mana kin manta kina tare da likita ne kuma insha Allah zai zo miki da sauki"
Waya ya hau bugawa su Mummy da sauran 'yan uwa, Aunty Fatima tana jin haka tace, "gobe zamu zo ganin mai ciki a gaishe mana da ita".
Nan Ummi ta sanar da Fa'iza da Falaq ihu ta sa da taji labarin cikin nan ta shaida mata an sa ranar auren nan da watanni shida, Ummi ta taya murna sosai.
**** **** ****
Watanni sun shud'e a halin yanzu cikin Ummi yana cikin wata na takwas komai wuya yake mata k'afafunta duk a kumbure suke ga BP amma dan jaraba tak'i bari ya d'auko mata mai aiki a ganin ta batasan zaman mai aiki tsabar kishi, sai dai shi ya taimaika mata da wasu aikin ganin haka sai Aunty Fatima ta bata Zareefa.
Tsaye take rik'e da gambun motar shi duk ta marairace fuska tace, "yanzu dan Allah bazaka barni naje bikin besty na ba", look! nace ki bar zancen nan zuwa ne baza ki je ba bakya ganin yanayin da kike ciki ke bakya tausayin kanki ne, karki k'ara min zancen nan in Allah Ya sauke ki lafiya da kaina zan kai ki har gidan ta dake zaria kinji ko,kai ta gyad'a idanunta cike da hawaye yana gani amma ya fuske dan yana fara lallabata zata fashe masa da kuka, na ya mata sallama ya nufi asibiti.
Tana shiga cikin gida ta danna kiran Falaq bugu biyu ta d'auka tace, "maman baby ya akayi ne?" Ummi tace, "meye ma ba ayi ba ya Nusayb ya hanani zuwa bikinki".
Falaq ta k'yalk'yale da dariya tace, "wallahi ya min daidai a sai da na gaya miki ki bari saboda halin da kike ciki ai komai d'an lafiya ne amma bakya ji".
Ba zaki gane ba Falaq ni nasan mai ke damuna a cikin jikina, ji nake kamar na kusa barin duniyan duk abinda nake cikin k'arfin hali nake yi duk dan kar hankalin ya Nusayb da Daddy ya tashi inason zuwa gida dan naga Daddy shiyasa na k'arfafa zuwa bikin amma ya hana.
Cikin tausaya Falaq tace, "karki d'aga hankalin ki insha Allahu xaki sauka lafiya kullum cikin taya ki addu'a mu ke dan Allah ki daina sa damuwa a ranki ko dan lafiyar jaririn dake jikinki"
Toh shikenan besty nagode, Allah ya bar zumunci.
Ameen ya rabbi cewar Falaq.
*Jiddah Samusa✍🏻*
[12/20, 6:59 PM] +234 806 161 2054: [8/10, 6:12 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*
*Na*
*©Hauwa Esmaeel Musa*
*Page*6⃣5⃣
1 WEEK LATER......
A cikin wad'annan kwanakin tunin Nusayb yayi nasarar siye zuciyar Ummi da nau'ikan *SALON K'AUNA* ya mantar da ita komai ba abinda ake a wannan gidan in banda mutunta juna da soyayya, a tunanin Nusayb a baya ya zaci duk ranar da ta ga wurin kwanan shi zata daina ganin girman shi amma sai yaga akasin haka, a ko yaushe burin ta ta mutunta shi a matsayin shi na mijinta.
******
A burkice ya shigo tana ganin shi ta mik'e ta masa sannu da zuwa, zama yayi ya kafe ta da ido tace, "lafiya kuwa na ganka haka?" yace, "ba lafiya, kinsan jibi hutuna zai k'are sai gashi na samu waya daga director lalle gobe na zo akwai aiki da zamu yi a Egypt na tsawon wata biyu".
Dafe k'irji tayi had'e da cewa, "har wata biyu?" wallahi kuwa na rasa mafita d'aya dan banson nayi nesa da ke ko kad'an, bakomai ya Nusayb shi aiki da ma haka ya gada dan haka karka damu wata biyu kamar sati biyu ne zaka dawo mu kasance da juna ai.
Hakane tashi muje ki had'a min kayana, a sanyaye ta bi bayanshi duk jikinta take cikin damuwa amma dan ta k'arfafa mishi gwiwa yasa ta dake, nan da nan suka shirya kayan, ya dubeta yace, "baby na bari naje wurin Abdullah na dawo ko"
Toh shikenan sai ka dawo Allah ya tsare cewar Ummi.
Yana fita kitchen ta nufa ta duba ta ga akwai abubuwan amfani, nan ta shirya mishi snacks kamar su cake, meat pie, doughnut, cookies cikin k'ank'ani lokaci ta kammala ta kai cikin kayan shi ta saka masa, sannan ta zo ta d'aura girki kafin magrib har ta gama ta sa turaren wuta ta kunna na'urar sanyaya d'aki sannan ta shiga wanka, ta shirya cikin "English wear" riga da wando ta tufke kitson ta na cukku da aka mata da ribbon.
Jin ana k'iran sallah yasa tayi nata kafin ta fito falo ta zauna had'e da kunna TV, ta kamo tashar MBC2 ana wani movie mai suna "Thor: the dark world" bata jima ta ji horn d'in motar shi fita tayi ta tarb'o shi ya rungumeta tsam sai kuma ta turo baki yana ganin haka yace, "ya akayi matar?"
Cikin muryar shagwab'a tace, "toh ba kaine ba kawai ka tafi kayi zaman ka" ohhh! Yi hakuri na biya ta gidan Mummy na musu sallama ne amma yanzu kam gani na dawo sai yadda kikayi dani" dariya kawai tayi tace, "oya muje kaci abinci favorite naka na dafa ma"
Jin haka yasa ya d'aga ta sama yana juyi da ita sai dariya suke...............
*Jiddah Samusa✍🏻*
[8/10, 7:15 PM] Jiddah Samusa✍🏻: *🍃SALON K'AUNA🍃*
*Na*
*©Hauwa Esmaeel Musa*
*Page*6⃣6⃣
Washe gari da kuka suka rabu da Ummi dakyar ta barshi ya tafi akan Asabe zata zo ta tayata zama kafin ya dawo su koma abuja.
Cikin kunar rai ta wuni duk da binini bayan d'an lokaci sai ya k'ira wayarta yaji lafiyar ta, sai yamma Asabe ta zo sannan ta saki ranta yayin da shi kuma flight d'in k'arfe tara na dare zasu bi.
Zaman su da Asabe ba laifi dan dama mutuniyar ta ce, kullum tana sak'ale da wayar ta a kunne tana waya da mijinta duk abunda d'ayansu zaiyi sai ya sanar wa d'an uwanshi hatta cin abinci ko wanka, bacci ko kacokan d'akin shi ta koma da yi ta rungume kayanshi tana shak'ar k'amshin turaren shi, haka zai mata waya da daren har sai yaji sauk'ar numfashin ta ya tabbatar tayi bacci sannan ya ke kashe wa. Abdullah ya k'okarin ziyartar ta ko ya kawo mata Fa'iza su wuni, in zata je gidan Mummy kuma direba ke zuwa ya d'auke su ita da Asabe in sun wuni ya dawo dasu ga Falaq ma tana zuwa mata.
Bata da matsalar komai damuwanta rashin mijinta kusa da ita ne kawai ga wani ciwon kai da take fama dashi da tashin zuciya da kwankwasonta ga bayanta dake ciwo ta tsakiya duk tak'i sanar masa gudun kar hankalin shi ya tashi.
**** **** ****
2 MONTHS LATER.......
Shirye-shirye take ba ji ba gani Asabe na kama mata wasu aikin dan yau maigida zai dira Kaduna, murna fal cike da zuk'atan su.
Girke-girke kala-kala suka yi bayan sun kammala ta shiga tayi wanka bayan ta fito ta tsane jikinta kulaccan ta shafa sannan tabi duk wani sako na jikinta ta shafe shi humra mai k'amshi 'yar maiduguri sannan ta shirya cikin shadda "pink color" d'inkin doguwar riga ta kashe d'auri kamar zata je gasar kyau.
Ta fito tana jujjuyawa a gaban Asabe tace, "ya kika ganni toh nayi?" Asabe ta rik'e baki tace, "uwar d'akina irin d'aukan wannan wanka haka ai sai kisa yallab'ai ya susuce", Ummi ta k'yalk'yale da dariya kawai, Asabe tace, "toh kin ga ni tafiya zanyi yanzu tun kan ya samo ni".
Ummi tace, "kai Asabe ki bari ya iso mana ku gaisa sai kace ana koranki, a'ah 'yar nan gara dai na tafi cewar Asabe, toh shikenan ina zuwa.