← Book details Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 23

Sashe 9

Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Shi kansa ya san ya fada ne don ya yi causing damuwa a zuciyarta, amma ya san nauyi ne da rashin sabo ya hanata daga wayar.
Ai kuwa ya kunnata, da sauri ta kira lambarsa ta sake kira ta ci gaba da kira amma ya share ya ki dagawa. Rahane sai ta soma kuka, Allah ya sota ita kadai ce dakin lokacin.
Hawayenta na zuba a kan wayar ta yi typing text ta tura masa.
“Ka yi hakuri Yaya Khalipha ba haka bane, ban san me zan ce maka bane”.
Shima shiru makatau ya ki replying. Sai ta rufe wayar gaba daya tana tsane hawayen idonta da gefen hijabin sallarta. Wahaltaccen barci Rahane ta yi, da mafarkai barkatai wadanda babu Khalipha a cikinsu sai IBRAHEEM!!!.
Wannan al’amari ya fara tsorata Rahane, wanda take so yake sonta daban, wanda take gani cikin mafarkinta daban. Ya Allah! Meye gaminta da Ibraheem? Da ta manta shekaru takwas? Ba ta kara tuno shi ba, balle wani abu da ya shafe shi, sai yanzu da Khalipha da soyayyarsa suka shigo cikin rayuwarta?
Washe gari ranar Juma’a kenan, tana masallaci tana Azkar bayan an sakko daga sallar Juma’a, tana yi tana share hawaye saboda damuwa, ta yi alkawarin ba za ta sake kunna waya ba tunda ita tasa Yaya Khalipha ya yi fushi da ita.
Gobe ne Asabar din karshen wata, kuma gobe Baba Dact zai zo ya dauke ta. Yau watanta guda kenan a Informatics Kazaure.
Zaituna classmate dinta ce, ita ce ta shigo cikin masallacin tana dube-dube, ta hangota a can lungu ta dukunkune cikin farin hijabin sallar ta ko jan carbi take ko karatu take ita kadai ta sani.
Ta nufeta da hanzari ta ce, “Tun dazu ake nemanki Yayanki ya zo za ku tafi”. Cikin mamaki ta ce a ranta, “Wane Yayan nawa?” Haka dai ta mike ta bi bayan Zaitunan.
Daga nesa ta hango wata dalleliyar Cadillac srx ruwan makuba, gilasanta masu duhu ne (tintics), don haka ba ta gane ko waye a ciki ba. Don haka ta ja gefe ta tsaya, Zaituna ta wuce hanyar hostel.
Hannuwanta a kirji tana harare-harare da jiran ko ta kwana don ta yi zaton irin lalatattun ‘ya’yan masu kudin nan ne da suka cika Informatics suna diban ‘yammata su fita dasu. Ta yi tsaki ta juya za ta tafi, sai ya sauke gilasan motar gaba daya ya ce,
“Rayhanah!:
Da sauri ta juyo, Yaya Khalipha ne.
Ya fito daga cikin motar ya yi tattaki har inda take.
‘Yar ciki da wando na farin yadin filtex ne a jikinshi, da alama babbar rigar na cikin motar da hula ruwan kasa a kanshi. A yau ne ta taba yiwa Yaya Khalipha kallo na sosi, na cikin ido da ido. Ta gano ba karamin kyakkyawa bane, sannan kamanninshi da Mami a sarari suke bai da digon Baba Dacta ko kadan, fari ne shi sol kamar Mami, bai da digon bakar fatar Baba Dacta.
Sannan fatarshi ta nuna alamun ba cikakken dan Nigerian bane ya fi kama da mutanen Middle East. Idan ta hada da kanta ta yi judging za ta fidda tambayoyi da dama, me Khalipha ya gani a tare da ita da har ya zabe ta ta zame masa uwargida kuma uwar ‘ya’yanshi?
Ita dai ta san ita ba kyau ne da ita ba, ba ‘yar kowa ba ce, bata da abin da za ta ja hankalinsa dashi. Babu wanda zai ba ta amsar wannan tambayar sai shi Khaliphan kansa.
To sai take tambayar kanta ita din ai ta san da hakan amma take sonshi, kuma kyawun sura ba shine dalili ba. Tana son Khalipha ne saboda halayensa kawai da yadda yake mutunta ta yake martabata tun tana nakasasshiya. Kaskantaccen asalinta ba abin juyawa a kalla bane a wajen Khalipha. For him, (Inna akramakum indallahi atqakum).
Da idanun dake cike da wadannan maganganu Rayhanah ta daga ido tana duban Khalipha.
“Idan ni munafuka ce don ina son Yaya Khalipha kamar yadda Abida ta ce, na yarda a rada min sarautar munafukai”.
Rahane ta ce a zuciyarta.

Bata san ina zata saka kanta da fushin da khalifa keyi da ita ba, bata san da wace kalma zata roke shi ya daina fushin da yakeyi da ita ba, da ace zata iya data gaya masa cewa zuciyarta mai rauni ce a kansa ba za ta iya jurewa ba.
Sai hawaye suka balle a idonta, ta yi saurin juya masa baya tana sharewa da gefen hijabinta.
Hannunta Khalipha ya kama ya janyota har seat din mai zaman banza na motarsa, kansa ya daura a kan sitiyari ya lumshe idonsa, ya jima kafin ya bude (but she is still wiping tears).
Khalipha bai tausaya mata ba duk da ya karanci dalilin tashin hankalinta, ya kuma san duk wani motion na zuciyarta a kansa. Sai cewa ya yi, “Sorry for the uninvited visit, na kasa jurewa ne Rayhanah! Ban zo don in saki kuka ba, ki yi hakuri. Insha Allah ba zan kuma zuwa ba da izininki ba. Now go to your hostel tunda na saki kuka......”
Da karfi take kokarin kafar da hawayen, sannan cikin karkarwar murya ta ce, “Ni Yaya Khalipha kana misjudging dina, kana yanke min hukunci da abin da ba shine a raina ba”.
Da sauri ya ce, “To mene ne a ran naki?”
Ta sunkuyar da kai, hawayen na son kara gocewa ta ce, “Daban ne da abin da kake tsammani.....”
Sai a nan ne ya tausaya mata, ya yi murmushi ya ce, “Is it opposite?”
Ta daga mishi kai a hankali ba tare da ta bari fuskarta ta kalle shi ba.
Sai Khalipha yasa gefen babbar rigarsa yana share mata hawaye yana cewa, “Kin karbe ni a matsayin uban ‘ya’yanki Rayhanah ba tare da hakan ya zamo karamci, sakayya ko tursasawa kai ba?”
Wannan karon ma girgiza kai ta yi sama wato eh, wata zuciyar na gaya mata cewa,
“Ki bude baki ki gaya masa kema ba yau kika fara son nasa ba”. Amma kawaici da mutunta kai a matsayin ta na diya mace ya danne komai.
Sai ya rankwafo ya leka fuskarta, tana ta fyace hanci. Duk kokarinsa na son ta kalle shi cikin ido ba ta yi hakan ba, ta runtse idonta da karfi.
Sai ya zakuda kadan ya ce, “Rahane, haba Rahanena, dube ni mana”.
Ba ta san sanda ta yi dariya ba ga hawaye a idonta, ta ce, “Idan na ce maka Audu ai na rama”.
Khalipha ya kama baki, “A ina kika san real name dina Rahane?”
Ta juya masa keya ta ce, “A idon matambayi”.
Khalipha ya rikice gaba daya, ya kasa controling effect din (tasirin) wannan acting na Rayhanah. Hular ma cireta ya yi a hankali ya dora mata a kan cinyarta.
“Dama kina da baki Rayhanah?”
Turo mai siraran lebbanta ta yi gaba tareda juya masa keya ta ce,
“Shafa ka ji”.
Ya ce, “A shafa labari-shuni???”
Dariya ta yi wadda ta fiddo fararen lafiyayyun hakoranta masu sheki, ta ce, “Ko a Jakar-Magori idan ka shafa za ka ji”.
“Shake my hands RAYHAH......”
Ya fada a wahalce tare da mika mata hannun damansa wanda ke daure da ruwan kasar agogon ‘Swatch’.
Ba ta mika mishin ba, sai ta bude kofar motar tana fadin “An kira sallah Yaya K....... can I go?”
Ya shafo sumar kansa ahankali daga goshinsa har zuwa keyarsa idanunshi a lumshe, sun kada sun zama brown dinsu ya ce a wahalce,
“Go to Masjid Rayhah........! tun kafin ki kashe ni da raina!!”.
Chapter 9 · 0% Book details