← Book details Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 23

Sashe 2

Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Lokacin da Abida da Jawahir suka samu gurbi a Jami’ar Bayero, lokacin ne Rahane ta zana jarabawar barin sakandire. Cikin watanni uku ta fito, kuma Raihanah ta bai wa kowa mamaki daga ‘A’ sai ‘B’ a dukkan takardunta. Maki ne da daga Abida har Jawahir babu wadda ta same shi a kamala sakandiren ta.
Wannan farin ciki da Rahane ta sanya Dr. Mansur, shi ya yi sanadin da ya fara tunanin abin da zai mata as a gift don ya kara karfafa mata gwiwa, ta kuma fahimci cewa babu maraya sai rago. Nakasa ba hujja bace ta mutuwar zuciya.
Bincike suke iya bincike wajen manya-manyan likitocin kunne na gida da waje. Dr. Philips, Baturen Sikotilan ne, kuma malami ga Dr. Mansur tun zamanin yana karatu a jami’ar Trinity.
Dr, Philips tsohon likitan kunne da makogwaro ne (ENT Surgeon) wanda a lokacin ya tsufa, har ya aje aiki, yana zaune a kauyensu na haihuwa (Braemar) shi da iyalansa.
Tsufan Dr. Philips bai hana har zuwa lokacin ana kawo masa cases masu tsanani har gida (Braemar) ba. Idan al’amarin ya gagari manyan likitoci, haka nan manyan kasashen duniya na hayarsa domin ya yi musu aiki a fanninsa. Shine mutum na farko da Dr. Mansur da Dr. Imam suka tuno a lokacin da suka gama gwaji na karshe (hearing test) a kan lalurar Rayhanah.
Ko Mami ba ta san me ake ciki ba, sai da aka zo tafiya Abuja yin visa wanda ya kama dole ita Raihan ta je. Bai yi mata bayanin komai ba sai ana i gobe tafiyarsu Abujan da daddare yake gaya mata.
An ce zuciya bata da kashi, sannan Mami ‘yar Adam ce kamar kowacce mace, tunda zuciyar ta irin ta kowacce mace ce da Allah ya halitta da kishi. A lokacin da ya gaya matan ji ta yi gabanta ya yi mummunan faduwa.
Me Dr. Mansur ke nufi da ita da bai yi shawara da ita ba? Bai nemi jin ra’ayinta ba? Yana nufin shi da Raihanan za su kama hanyar Abujan ko me? Yana nufin da santaleliyar budurwa za ta barshi ya sata a mota su bar gari? Ko yana nufin haka zai sa yarinyar a gaba su bar kasar? Babu dangin iya babu na baba, ita mahaukaciya ko shashashar ina ce? Wannan kauna da kulawa da Dr. Mansur ke yiwa Rayhanah fiye da ‘ya’yan cikinsa ta magani da mece ce?
A take yanayin fuskarta ya sauya, kishi karara ya bayyana a kyakkyawar fuskarta. Sannan ranar da ta ga Khalipha rungume da Rayhanah a asibiti ta kara fado mata, da halin da Khalipha ya shiga a lokacin da hirar da suka yi. Tiryan-tiryan ta dinga dawo mata.......’an kasa ni! Soyayya ce Mami!!’
Nan da nan kwakwalwarta ta soma kimsa mata abubuwa daban-daban cikin ranta wadanda a zahiri ba haka suke ba. Wato uban na so, dan ma na so. Dalilin shigar Khalipha halin da ya shiga kafin ya tafi, yana nufin Daddy ya kasa shi. Tunda ya ga ba zai iya tarayya kan soyayya da mahaifinshi ba.
Hankalin Mami ya tashi kwarai, wata irin firgita ta kamata. Ta mike tsaye kawai ta yi daki, ba tare da ta ce da Dacta Mansur komai ba.
A lokacin ma cike form din neman visa yake yi a ipad dinsa. Jin Mamin ba ta yi magana ba ya daga ido ya dubi sashen da take, sai ya ga har ta kai kofar dakin barcinta.
Ya yi dan jim yana ‘yan sake-sake. To me ya bata mata rai cikin wannan maganar? Ya aje biro ya mike ya bita dakin, sai ya ganta zaune a bakin gado ta yi tagumi da hannuwa bibbiyu, yanayin fuskarta kuwa ba zai karantu ba.
Zama ya yi kawai kusa da ita kafadunsu na gugar na juna.
“Asma’u Zatun-Nidakaini (ma’abociyar mayafi biyu). Mai sunanki ma’abociyar hikima da ilmi ce diya ce ga Sayyadina Abubakar As-Saddik. Lokacin da Manzo (S.A.W) ya yi Hijira zuwa Kogon Hira ita ke kai masa abinci tana rufe da mayafin..........”
Sauran maganar makalewa ta yi a makogaronsa ganin Mami ta soma kuka. Hankalin Dr. Mansur ya tashi, kololuwar tashi kuwa.
“Me ya faru Asma’u? Na fadi abin da ya bata ranki ne? Ina so ne kawai in gaya miki kissar mai sunanki, ba ta fushi a kan abin da ba ta da sani a kansa, ko kuwa abinda bai kai ya kawo ba”.
Mami ta sharce hanci da ido da tishun dake gefen gadonta. Magana ta farko da ta furta masa tun shigowarsa ita ce,
“Hausawa baku da kirki, baku da amana wallahi”.
Ido ya dan bude kadan yana kallon ta, ya ce, “Mu din kuwa? To me muka yi mu Hausawa rainon Musulunci?”
Ta ce, “Kuna kafa hujja da addinin Allah ku ci amanar matayenku, ku kuntata musu ku saka musu hairan da sharran. Ayi Magana ku kafa hujjah da addini bayan shi addini ne mai adalci ga kowa. Wannan na daya daga cikin abubuwan da ke tsorata masu niyyar Musulunta su ga addinin Musulunci very scary, don baku da sanin yakamata da amana, musamman aka zo maganar kara aure.”.
Dr. Mansur kallonta yake sosai cikin idanunta dake ta kwararar da hawaye, ya ce, “To wane Bahaushe ne zai kara aure?”
Idanunta jage-jage da hawaye ta balla masa harara ta ce,
“Ba ga ka nan ba? Ka rasa da abinda za ka saka mini sai da son auren Rayhanah? Hakan ba cin amana bane? Duk taimako da karar dana yi maku?”
Ya kama kanshi yana girgizawa don ma ya rasa ta cewa, ya ce, “Da shekaru hamsin da biyar din zan auri ‘yar sha bakwai? Tukunna ma, wai wace Raihanan kike nufi ne?”
Gaba daya ranshi ya gama baci, Mami ta ga wani irin fushi cikin kwayar idonsa da ba ta taba gani ba. Tsigar jikinshi ta tashi gaba daya, jijiyoyin kansa sun fito rada-rada, idanunshi sun kada sunyi jawur.
Ganin yanayin da ya fada yasa ta kasa bashi amsa. Ya mike tsaye zai fice daga dakin yana cewa,
“Lallai kuwa duk inda mace take, komin girmanta da iliminta da shekarunta kamar dabba take”.
“Nice dabba Dacta Na?”
“Ai ina ga ma wata dabbar za ta fiki hankali”.
Ya yi ficewarsa ya rufo mata kofar, ji kake garaam!.
Kai tsaye dakin su Raihan ya shiga, dukkansu karatu suke na Alkur’ani irin (pieces) din nan mai kowanne izfi biyu. Su kan taru ne har Azizah da ta dan kara tasawa duk sati biyu suyi saukar Alkur’ani, su yiwa kansu da iyayensu addu’a da ‘ya’yan da za su haifa a gaba.
Bai tsaya ba ya ce, “Rayhanatu ke da Azizah ku yi shiri zamu tafi Abuja karfe shida na safe in Allah ya kaimu”.
Suka daga mishi kai ba tare da sun katse karatun nasu ba.

****
Chapter 2 · 0% Book details