← Book details Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 23

Sashe 3

Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy na sharara gudu a kan titin Abuja da Rayhanah da Azizah, Azizah na gaba Rayha na baya. Basu jima da fara tafiya ba Azizah ta yi barci, don haka Daddy ya mika hannu ya rage mata karfin A.C.
Karfe goma sha daya na rana suna Abuja. Sai da ya kaisu suka yi break fast sannan suka karasa British House dake Maitama, suka bi layin neman visa. Don haka zuwa karfe biyar na yamma sun dawo Kano. Ya sauke su, ko gida bai shiga ba ya kada kan mota ya yi asibiti.
Ga mamakin Rahane sanda suka shiga falo Mami na zaune a kan carpet cikin wani yanayi da Raihanah ba ta taba ganinta a ciki ba. Tana yi mata wani irin kallo kamar ba ta san daga inda ta fito ba.
Ta yi sallama, Mami ba ta amsa ba, sai juyawa ta yi kan Azizah ta soma fadin “Da izinin wa kika tafi rakiyar? Kin gaya mini?”
Jikin Rahane ya yi bala’in sanyi. Azizah ta soma kyarma don ta san fushin Mami ba kyau, kamar ta saki kuka ta ce, “Mami kina barci lokacin, Daddy ya ce in shirya mu tafi”.
Ta ce, “Wuce ki ban wuri ko in yi kwallo dake wallahi”.
Da gudu Azizah ta karasa daki inda ta tadda na Abida na jiranta, ta harareta ta ce, “Ke yanzu don lalacewa shine kika raka wannan jakar yin visar fita waje tare da ubanki, ita ba matarsa ba, ba ‘yarsa ba, ba kowan kowa ba babu dangin iya babu na Baba?”
Jawahir ta ce, “Ai ba ita za ki gayawa haka ba, wanda ya yi mata umarnin zuwa rakiyar shi ya kamata ki je ki yi mishi wannan tunasarwar ba ita ba”.
Ta ballawa Jawahir din harara ta ce, “Nasa dake a ciki? Na ce na sa ki?”
Yadda ta hayayyako mata sai ka rantse da Allah ita ce babba ba Jawahir din ba.
Ta ce, “Sai na ji duka sannan in baki amsa”.
Abida ta yi tsaki ta fice daga dakin.
Mami ta juya kan Rayhanah ta kalleta da kyau, jikinta a matukar sanyaye ta kasa cira kafa daga inda take, a darare ta ce, “Mami mun dawo”.
Tace “to barkanku da zuwa”. Ta shige dakin ta ta bar ta anan.
Ta kwanta a gadonta amma barci ya ki zuwa. Hankalinta a masifar tashe yake. Me ya faru da Mami? Me ta yiwa Mami ta canza mata haka farat daya kamar ba ta taba saninta ba?
Yadda ta kwana da wadannan damuwoyi da tambayar kai da rashin mai amsa mata, haka Dacta Asma’u ta kwana.
Sai dai ita nata damuwoyin nema suke su fitar da ita daga hankalinta da tunaninta. Takun sakar da suka yi da Dr. Mansur ranar da ya kawo Rahane ke dawo mata filla-filla. Suna shiga sikeli na optical-illusion, wato tana fassarasu da abin da ta gani a fuska, ba wanda ke cikin zuciya ba.
Cewa da ya yi, “Maganar aure da ‘ya’yanki kuwa, ki sa ranki a inuwa sassanya, Allah zai bawa Rayhanah miji na ban mamaki, wanda zai kaunace ta domin Allah, ya rungumeta da LALURAR ta, ba lallai ‘ya’yanki ba, masu hali da dabi’u irin naki. ‘Ya’yanki ba sune kadai MAZA a duniya ba, sannan basu fi ‘ya’yan kowa ba!!! MAZA ma tukunnah, baki gansu ba Mami.....” Wanda a yau ta fassarasu kai tsaye, yana nufin shi da kansa zai auri Rayhanah!!!
Tunanin Mami ya gushe kwata-kwata, ta yadda da fassarar zuciyarta. Daman ita mace duk shekarunta da hankalinta, da iliminta in aka zo batun KISHI gushewa suke yi.
Tun daga wannan ranar Rayha ba ta kara ganin hakorin Mami a gidan nan ba, ita ba ta kore ta ba, amma ta fita sabgarta. Ita da Abida take sha’aninta ko Jawahir ta san Mami ta canjawa Rahane fuska. Damuwar duniya ta yiwa Rayha yawa.
To wa za ta gayamawa damuwar da take ciki ya taimaketa koda da shawara ne? Babu, Yaya Khalipha ne da Jawahir, to amma wace ce Jawahir kuma wane ne Khalipha? ‘Ya’yan Mami ne, za ta kai musu karar mahaifiyarsu ne ko ya ya? Me ta yiwa Mami? Rashin wadannan amsoshin sai su sa ta kwantar da kai cikin cinyoyinta ta yi ta kuka.
A haka aka gangara har sati biyu. Daddy ya je Abuja ya karbo visa. Ko da ya dawo ko Mami bai tsaya nunawa ba balle ya bata lokacinsa wajen yi mata bayani.
Gaba daya ya fita sha’aninta tun ranar da ta yi masa wannan haukan. Muraran ya gane yanzu kam bata bayan zaman yarinyar nan a gidanta. Don haka ya tattarata ya watsar ya gani ko da gadon ubanta aka cika aka saya mishi gidan? Ya tabbata da hakan ne da tuni ta koreta watakila.
Ranar tashinsu ta kama Asabar, Azizah ce ‘yar rakiyar Rahane. Ta Lagos suka tashi a daren Lahadi, da shi da Dr. Imam, Rayha da Azizah.
A cikin jirgin ‘boeing 709’ da suke ciki Rahane kanta ta kwantar a kujerar dake gabanta, ba ta kuka sai tunanin rayuwa da kalubalen da ke cikinta.
Daddy ya juyo ya mika mata wani kyakkyawan carbi dan Madina ya ce ta yi ta maimaita “Wa-man-nasaru illa min indillahil Aliyul Azeem, Allahumma ashfiny wa afani, ya shaafee ya mu’afee”. Har suka sauka.
A Aberdeen suka sauka, basu kwana ba a ranar suka wuce ‘Braemar Village’ ta Aberdeenshire.
Ba kamar yadda suka tsara ba, cewa za su sauka a hotel. Dr. Philips ya ce, “A’a, yana da gidan gona a jikin gidansa inda yake kiwon kaji da tattabarun Ingila farare sol da agwagin ruwa, kifi da kangaroo (babba da jaka).
A cikin wannan gidan dakuna ne falle biyu ko ko a ce hut, domin hutawarshi da iyalinsa ko sauke bakinsa na nesa. A nan ya yiwa su Daddy umarnin su sauka, har su ga abin da Allah zai yi. Amma bai dauki nauyin abincinsu ba (kun san Bature) da tsimilmila. Duk da haka ya yi umrnin Rayha da Aziza su zauna cikin iyalinsa.
Matar Dr. Philips ita ma dattijuwa ce ‘yar shekaru hamsin, sunanta Mummy Regina. Amma da wuya ka bai wa Regina wadannan shekaru a zahiri za ka ba ta arba’in da uku ko da biyar ne. Baturiyar Dundee ce, kuma tsohuwar lauya mai zaman kanta. Yaranta biyu, Cynthia da Chelsea duka ‘yammata ne a jami’ar Aberdeen.
Sai dai sun girmewa Rayhanah sosai, don dukkansu degree holders ne a bangarori daban-daban. Yanzu haka ita Cynthia MBA take yi (Master of Business Administration). Chelsea kuma ba ta fara masters din ba tukunna. Turawa ne ‘yan asalin Sikotilan iyaye da kakanni.

Kauyen Braemar kauye ne mai tsohon tarihi a Scotland. Braemar wani dan kankanin kauye ne a tudun Grampian (Grampian High Land) wanda ke yankin Scotland.
Braemar kauye ne mai kayatarwa da za ki ga gulbi na kwarara a kan duwatsu masu dadadden tarihi, ga tsaunika masu kyau tare da tsofaffin gine-gine na gargajiya, wanda suke ba da wani launi mai ban sha’awa. Kyawun kasar Scotland ya shafi wannan kauye na ‘Breamer’.
Akwai wani dutse dake mahadar kogunan ‘Clunie’ da ‘Dee’ ya zama wata mahada ta shakatawa ga al’ummar kauyen, kewaye da wannan mahadar akwai kimanin tsaunuka ashirin wanda sun kai tsahon kafa 3,000.
Braemar ya shahara saboda wasanni da ake gabatarwa a garin duk shekara. Wanda ake musu lakani da wasnanin tsaunuka. Shi wannan gagarumin biki ya samo asali ne tun shekarar 1832, wato zamanin sarauniyar Ingila Victoria wadda ta albarkaci wannan bukukuwa.
Har zuwa yau ‘ya’yan gidan Sarautar Ingila suna halartar wadannan wasanni wanda a yanzu Sarauniya Elizabeth ita ce babbar uwa ta wadannan wasanni.
Ana gabatar da wannan bikin ne a Asabar din farko ta watan Satumba, inda ake bushe-bushe da kada-kaden gargajiya masu dimbin tarihi wanda in ba a irin wannan wajen ba da wuya ka ji irinsu.
Wannan wasa ya kunshi gasar busa sarewa da ganga tare da raye-raye irin na da, sannan wasannin gargajiya. Braemar cike yake da dadadden tarihi domin a nan ne aka yi boren Jacobite a shekarar (1715) wanda ya komar da ‘Stuart’ kan gadon sarautar Birtaniya. Dai-dai wajen da aka gudanar da wannan bore shine a yanzu gurbin masaukin baki na ‘Invercauds Arms Hotel’ wanda su Dr. Mansur suka so sauka a can.
Wani marubuci Robert Louis Stevenson ya fara rubuta bangaren farko na tsibirin taska (treasure Island) a garin Braemar a watan Agusta na shekarar 1881. A yau guraben da suke dauke da tarihi sun zama wajen saukar baki. Fadoji biyu sun kara ma garin Breamar armashi, wato fadar ‘Kindrochit’ wadda aka gina a shekarar 1390, tana tsakiyar wannan kauyen. Sai kuma fadar Braemar wadda ke tsahon rabin mil (mile) daga garin Braemar.
Wani wajen kuma mai dadadden tarihi shine cibiyar tarihi da ake wa lakabi da ‘Highland Heritage Center. Wannan cibiya tana dauke da bayanai masu kayatarwa da suka shafi tarihin garin Braemar. Bayanan sun hada da bayanin bukukuwan tuddai, da bayanin Sarauniya Victoria, da fadar Balmoral da sauraansu.

Dr. Philips ke bai wa su Daddy wannan tarihi na kauyensa a kwanakin su biyu da zuwa, suna zaune cikin ‘hut’ suna shan coffee.
Su Daddy suka girgiza kai cikin gamsuwa da samun karin sani. Dr. Philips ya aje dan kankanin kofinsa a dan teburin dake tsakiyarsu. Ya dubi Daddy ya ce ya yi masa karin bayani kan wanda ya turo masa ta yanar gizo kan sanadin matsalar yarinyarsu.
Tiryan-tiryan Daddy ya zayyano masa komai. Ya ce, “To bayan hakan wane mataki aka dauka na gaggawa?”
Dacta Imam ya mika masa komai a rubuce cikin ‘Ipad’ dinsa.
Da shi da su gaba daya suka shiga Laboratory, dake cikin private asibitinsa. Bayan sun biya duka payment din duka ta yanar gizo, sunan asibitin Spire Little Aston. Dr. Philips ya shigar da Rahane ya soma gudanar da CT Scan and MRI Scan. Tsayin sati biyu kafin sakamako ya fito. A daren ranar ya sanya su gaban kwamfuta yana yi musu bayani kamar haka;
Chapter 3 · 0% Book details