← Book details Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 23

Sashe 22

Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Haduwarta da Mansur Balarabe Sardauna, ta samo asali ne a matsayinsa na daya daga cikin malamansu, a lokacin shi ya yi graduating yana aikin da ya zamewa duk wani foreigner dole bayan kammala karatu kamin ya koma kasarsu.
Ya lura in ana darasi tana yawan fita ta je ta shayar da baby a hannun wata dattijiyar Balarabiya da take aikin leburanci a Jami’ar, take rike mata dan saboda Allah, don ta lura Asma’u ce kadai Musulma a bangaren da take kula da shi. Amma abinda yake daukar hankalin Mansur da Khalisah (dattijuwar), basu taba ganin uban dan ba, ga shi Balarabe ziryan ita kuma da ganinta ka ga ‘yar Nigeria.
A al’ada irin ta Bature, mace mai aure kusan koyaushe tare take da mijinta duk inda za su je, balle idan akwai karamin yaro kusan uban ne ke da wannan alhaki na kula da yaron a lokacin zirga-zirga, shi zai tura shi zai dauka, basa barin matansu su sha wahala.
Hazakarta a karatu na ba shi mamaki yadda take yin zarra da manyan maki (marks) a cikin Turawa. Ya damu da al’amarin ta, gata yarinya karama da ko ashirin ba ta rufa ba. Idan yana lacca kusan rabin hankalinsa a kanta yake, idan tambaya ce ita yake jefawa, ba ta yin kasa a gwiwa wajen farke masa zare da abawa.
Tafi-tafi Mansur ya kasa sukuni da tunanin Asma’u da begenta dare da rana. Uncle Yohan shi yake daukar nauyin karatun Asma’u, ba yadda bai yi ba don ya samo mata Nanny din da za ta dinga kula mata da Khalipha a gida ta je ta dawo tunda ba ta son shi a hannun Marye. Asma’u ta ki.
Ya ce, zai dinga kai shi gidan raino na Turawa shima ta ki. Don haka ya yi fushi ya rabu da ita kamar akan ta aka soma haihuwa. Ga shi Allah ya jarrabi zuciyarsa da son Khalipha kasancewar shi Allah bai ba shi haihuwa ba.
Daga shi har Marye kyamarsu take, ko abincinsu ba kowanne take ci ba. Don a Jos Marye murde kan kaza take da ranta ta cizge ta cillar ta fige ta dafa. Ire-iren wadannan yasa Asma’u ta gwammace Yohan ya ba ta kudi ta sayi ‘halaal’ ta dafa da kanta ko ta yi take away daga makaranta a wajen larabawa musulmi ko Pakistani mazauna turai.
Asma’u bata takurawa Yohan da cewa lallai sai ya Musulunta ba, don ta lura tana tufka ne Marye na warware mata, ko yaso ya saduda zigar Marye ke hana shi. Tana nuna masa cewa addinin Musulunci addini ne na takurawa kawai, sannan Musulmin da ya zama kasurgumin Musulmi shine yake zama terrorist (dan ta-adda).
To Allah shi ke hukunta al’amura yadda yaso, idan ya so bawanshi da shiriya ruwa da iska basu isa su hana ba. Marye ta yi mutuwar wulakanci a Dublin inda wani ginin bene ya rubza da ita da jama’a masu dimbin yawa, ko gawarta sai part-part aka tattara, sauran namanta ya zama na ungulu da tsuntsaye.
Asma’u ta ja dan’uwanta a jiki, dare da rana, yini da safiya tana kwadaita masa dadin addini musamman na Islam. Ta kan ce, “Shi Musulunci haske ne kuma guidance ne, wanda zai sada dan Adam ga nutsuwa da kwanciyar hankali, hanya ce kawai dake nuna maka yadda za ka rayu a kan tafarki madaidaici. Tsani ne mai mika mutum kusa da Ubangijinsa yaje ya iske sakamakon abin da ya shuka a rayuwarsa ta duniya.
Ba abin da addinin musulunci bai koya mana ba, hatta shiga bandaki, tsarki, wanka, cin abinci duk Islam ya kawo su a kan hanya sahihiya (to the heaven)” Haka dai, yau da gobe har Allah ya taimaketa ta yi galaba a kan Yohan, ta kai shi wajen Limamai suka musuluntar da shi ya mai da sunanshi Yahya. Hakan bai hana har yau jama’ar da suka san shi kiranshi da Yohan ba.
Yohan (Yahya) ya shiga Islam ne da zuciya daya. A wannan lokacin Yohan ya yi karfi na ban mamaki cikin kasuwancin da yake yi tsakanin Ireland da Nigeria. Ta hanyar Asma’u ya auri wata mutuniyar Somali zaunannun Dublin wai ita Aasiya. Ba ta taba yin aure ba amma ta manyanta domin cikakkiyar likitar mata ce.
Shekara ba ta kai ga fita ba Dr. Aasiya ta haihu da namiji. Ashe matsalar daga Marye ne ita din ta sani likitoci sun gaya mata, wannan ne yasa ta san duk hanyar da ta bi ta hana Yohan zuwa asibiti a bincike su sai karyar bari (miscarriage) take masa.
Har lokacin Asma’u na jinyar Khalipha dake fama da hypertitis B. Zuwan Aasiya gidansu ya kawo sauki mai yawa cikin rayuwarta duk da ita ma Aasiyar ma’aikaciya ce a babban asibitin kasa amma tana taimaka mata sosai wajen rainon Khalipha har Allah ya raya shi, ta kai shi wata Islamic school a London (Al-Muntada Islamic Pri. Sch.) boarding, ita kuma ta koma Dublin. Duka cikin aljihun Uncle Yohan.
A shekarar Dr. Aasiya ta kara haihuwar diya mace, a wannan lokacin shekarun da Mansur zai yi yana aikin wucin-gadi da jami’ar Trinity sun kusa cika, zuwa lokacin ya yi duk binciken da zai iya a kan Asma’u, ya tadda komai, wato ba ta da aure, uban dan ya rasu.
A matsayinshi na Bahaushe Ba-Kano kuma wanda ya fito daga jinin sarautar Takai abin ya zo a karkace, saurayi da auren bazawara mai da. Duk da addininmu bai hana ba, karewa ma hakan sunnah ce, kuma ya san yayansa Abdulkadir ba zai taba ki ba. Shi a kaunar da yakewa Asma’u ma, ko kantin kwari ta haife zai rike mata, kuma in ta amince zai aureta.
Kai tsaye bai doshi Asma’u ba, domin ba fuska, kullum suturce take cikin yalwatacciyar suttura da karamin hijabi iya kafadunta. Sai ya bi ta hanyar da kowacce UWA ba za ta iya kaucewa ba.
Wato yaje ya yi kawance da dattijuwar lebura Khalisa, yake tayata hidimar Khalipha kafin Mamanshi ta kai shi makarantar kwana. In ba shi da lacca wajen Khalipha da Khalisa yake lalacewa. Siyo wannan, siyo wancan duk na Khalipha.
Har Asma’u ta fara mamaki saboda ta san ko shi wane ne a Trinity da tarin iliminsa. A hankali suka soma gaisawa, tunda an ce mai Da wawa. Wani irin so Mansur kewa Khalipha wanda ko shi ya haife shi sai haka, ba kuma don komi ba sai don kamanninsa da mahaifiyarsa. So na hakika shine ka so uwa tare da dan ta.
Sai ga Asma’u na gayar da Mansur Takai kullum, har in ba ta ganshi ba ta hau tambayar Khalisa yau Baban Khalipha bai zo bane? Khalisa kan ce, ya zo ya sumbace shi ya ba shi chaculates ya tafi. Sai Asma’u ta yi murmushi har ta kai Khalipha London a bisa shawarar Mansur a haka suke.
Mansur shi ya lalubo mata makarantar kasancewar ya zauna England kafin Ireland inda ya yi karatun share fagen shiga jami’a. Ya fita sanin UK da Islamic Schools masu yawa dake cikin ta. Sai kuma aka koma kawance har cin abinci take gayyatarsa gidansu wajen Uncle da Dr. Aasiya. Ta kai ta kawo duk wani wanda ya rabi Asma’u, to ya saba da Mansur mai yi mata son kan-uwa-da-wabi, wato sonta yake tare da dukkan ahalinta da duk wanda take tare da shi.
Tare suke zuwa London dubo Khalipha duk wata. Lokacin komawar Mansur gida ya cika, amma ya kara neman visar aiki ya shantake ya ki tafiya saboda Asma’u. Su kuwa gwamnatin Dublin ai gaba ta kai su don dama irin Mansur din suke so su suke gudunsu domin kishin kasa (Patriotism). Irin na ‘yan bokon nijeriyar jiya ba na yau ba.
Sai suka shiga jika shi da kudi, gida cikin gidajen malaman Jami’ar Trinity da Insurance, accommodation and allowances. Da Hakimi ya bi ba’asin fasa dawowar tasa bai boye masa ba, “He cannot live without Asma’uuuuu!!!”
Chapter 22 · 0% Book details