Sashe 5
Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ALKAWARIN ALLAH YA CIKA......
Kamar daga nesa take jiyo kiran sallah, don haka ta yi hanzarin kai hannunta ta shafo na’urarta, don dai ta san bata kwanciya da ita, kuma gabanin alluran da Philips ya yi mata ta tabbata ta cire su.
Da gaske babu su a tare da ita, hakan kuma bai hanata jin kiran sallar Asubar ba. Ta yi saurin juyawa don ganin ta inda sautin ke fitowa. ‘Yar rediyon Dr. Mansur ce dake kan dirowar gadonta ke fitar da sautin kiran sallar. Daga masallacin Qubah.
Wata sassanyar iska kuma ta ji tana ratsawa ta cikin kunnuwanta zuwa cikin kwakwalwarta. Ba ta ko haufi jinta ne ya dawo! Rasss!! Kuma rangadadau!!!.
Sai ta yunkuro da karfi daga kwancen da take, sai Daddy ya yi saurin maidata kwancen sakamakon na’urorin dake lullube da kanta.
“Rayhanahtu aikin bai yi ba ko???” Dr. Mansur ya fada muryarsa na dan rawa jikinsa na dan karkarwa.
Ta dago ido a hankali ta dube shi sai kwallar farin ciki ta ciko idanunta. Ta kurawa Daddy ido kawai ta kasa cewa komai. Ko uban da ya haifeta iyakar kaunar da zai yi mata kenan. Ita kuwa da me za ta sakawa Daddy a fadin duniyar nan? Babu, ba ta da shi ban da ta yi masa addu’a a bayan kowacce sallar farillah kamar yadda take yiwa iyayenta da Iya.
Dr. Mansur ya gaji da kallon da Rahane ke masa babu ko kiftawa hawaye na zuba a idonta, ya karaso jikin gadonta yana tambaya “Rayhanatu........Rahane.......Rayhanah.......kina jina???”
Cikin kukan farin cikin da ya kwace mata ta ce, “Ina jinka Daddy, sosai, ba tare da hearing aid ba!”.
Sai ya juya baya ya yiwa Allah Sujjadah. Dai-dai lokacin da Dr. Philips da Dr. Imam suka shigo. Suka nufeta da azama suna ciccire na’urorin domin allon kwamfutar dake makale a sama ya nuna komai na Rayhanah ya dawo normal.
Kwanaki bakwai suka kara bayan nan duk cikin treatments din ne, da shan magani, sai da komai ya zama dai-dai sannan suka taho. Suka sauka da asubahin safiyar Litinin mai albarka a filin jirgin Malam Aminu Kano.
Daddy bai yi mamakin ganin cewa Mami ba ta zo taryarsa ba, ya san ba ta sani ba, kuma ko ta sani ba za ta zo din ba. Don ko sallamar kirki basu yi ba, wannan ne ya hanashi kiranta a waya har suka je suka dawo.
Matar Dr. Imam ta zo ta dauke su, suka aje Daddy da iyalinsa a gidansa dake Lamido Crescent sannan suka wuce nasu gidan a Badawa lowcost.
Malam Dahiru maigadi shi ya biyo su da kayansu. Daddy ya yi amfani da mukullin shi ya bude kofar reception suka bi matattakala zuwa sama.
Jawahir da Abida na barci Zizah ta fada musu a kai tana ihun murna, “Tashi Yaya Jawahir, Yaya Abida tashi, Rayhanah na ji (with out aid), it is successful...... ku tashii ku gani....”
A gigice Jawahir ta mike da gudu ta rungume Rayhanah, sai ga kwallar farin ciki. Abida kanta ta mamakantu, ta kasa komawa barcinta ta rasa cikin yanayin da take ciki, tana taya masoyan Rayhanah murna ko tana bakin ciki ne ba ta sani ba. Abin da ta sani shine jikinta ya yi sanyi, ta kasa hassala komai.
Rayha wanka ta yi, ta dauro alwala ta bada faralin Asubahi, ta yi addu’o’i na godiya ga Gafurun-Rahimun, neman Rahamar Allah ga iyayenta da Baba Dacta ba don ya mutu ba. Duk hirarrakin da Azizah ke zuba musu labarin kauyen Braemar ne da basu sani ba.
****
Sanda Daddy ya shiga bed room dinsa, ga mamakinsa sai ga Mami ta biyoshi fuskarta a sake kamar ba abinda ya faru.
“Maraba da bakin Scotland, duk da dai tafiyar da dawowar duka babu waya..... da fatan an samu nasarar abin da aka je nema”.
Ta fada tana loosing tie din wuyansa. Bai ce komi ba kawai kallon ta yake. Sai ta fada jikinshi tana kuka a hankali tana ba shi hakuri da cewa, ta zauna ta yi tunani ta ga cewa abin da ta yi bai kamata ba, kishi ne da sharrin shaidan, wanda baya so a zauna lafiya.
Tsakanin mace da mijinta sai Allah. Balle Asma’u da Mansur, wadanda suka gina rayuwarsu a kan soyayya, kauna da fahimtar juna.
Ya ce, “Ni me za ki ce min kuma Mamina, tunda kin daukeni dattijon banza, wannan furfurar da ta fara baibaye kaina duk ta banza ce. Ban taba zato ba Asma’u, ban taba zaton za ki iya zargina a kan komai ba balle Rayhanah! Zan dauki komai, amma ban da a taba mutuncina da gemuna da furfurata.
Zan iya rabuwa da komai a kan hakan Asma’u.......... Rayhanah ‘yata ce, ki sa wannan a ranki, ina jin wani abu daban game da ita a jikina da zuciyata mai kama da kaunar jini a kanta. Allah shi ya fi kowa sani. Amma kin bani mamaki Mami, mamaki sosai, wanda ya sanya ni cikin kokonton anya ke ce? Asma’u ina hankalinki ina tunaninki? Ina yardarm da muka yiwa juna........”
Ta yi saurin kai hannunta ta rufe mishi baki tana girgiza kai hawaye na zuba a idonta.
“Na tuba Dactana, na tuba likitan zuciyata. Tun ranar da wannan al’amari ya faru ban kara samun nutsuwar zuciyata ba, bana isasshen barci saboda nadama. Na yarda lallai lokacin hankalina ya tafi, ka yi hakuri Dactana, don Allah ka yafe mini.......”
Irin rikon da ya yi mata kadai ya isa amsar cewa ya yafe mata ko bai yafe mata ba. Tabbacin shima ya jigata da rashinta.
Da safe ne yake gaya mata duk abin da ya faru a Braemar da nasarar da aka samu. Ta mamakantu kwarai, kuma a lokacin ta tafi dakin su Rahanen.
Fuskarta da murmushi ta dubi Rayhanah ta ce, “Congratulation Rayhanah, Allah ya kara lafiya”.
A sanyaye ta ce, “Amin”. Tana son ta yi kuka zuciyarta cike da kaunar Mami da tsoron kada ta komo irin Mamin da ta koma mata a baya.