Sashe 19
Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ta kai gefen hijabinta ta share hawayen da suka zubo mata a wannan lokacin. Ba wanda ta tuna a wannan lokacin sai Zinaru kanwar mahaifiyarta Yalwati da Malam Rashidu ya aura ya saki, rabonta da Zinaru tun ranar da ta bar gidansu.
Ta sani cewa duka kakanninta na wajen uwa sun rasu, amma Zinaru tana raye, za kuma ta iya sadata da wasu daga cikin dangin Yalwati in akwai, idan ita ba za ta zauna da ita ba har zuwa lokacin da Allah zai ba ta miji a nan Takai dai-dai da rayuwarta, wanda ba zai kalli tushenta, asalinta da tsohuwar lalurarta ababen kyama ba, tunda tushe da asalinsu daya.
To yanzu ina za ta nufa neman Zinaru? Shekarun da yawa, Takai da girma. Abin da ya kara ruruta wutar kukan da take yi kenan.
Ta bi gefen titi ta soma tafiya tana kukan, amma ta toshe bakinta da hijabin. Tafiya take cikin zafin nama ba tare da ta san inda take jefa kafafunta ba.
Horn din mota ta ji a bayanta ba kakkautawa, amma ba ta juyo ba ta ci gaba da tafiyarta, tunda ta san ita dai ba a tsakiyar titi take tafiya ba balle a ce ta matsa. Sai ma ta kara azama ta soma shigewa cikin gonakin masara.
Fakin din motar aka yi a gefe aka biyota da kafafu. Muryar da ta ji na kiran sunanta da karfi ya sata juyowa cikin razana da firgici. Baba Dacta ne da Sha’aban dan wajen Hakimi. Ya fi karfin ta kalle shi ta wuce, yana da kimar da babu mai ita a idanunta a duniya idan ka dauke iyayenta.
Don haka ta ja ta tsaya idonta cike da hawayen da suka kasa tsagaitawa. Har Baba Dacta ya iso inda take ya kama hannunta idanunsa shima sun kada sunyi jawur, amma ba hawaye a cikinsu.
Sha’aban ya koma ya matso da motar har inda suke. Baba Dacta ya bude kofar baya ya shigar da ita ya rufe, shi kuma ya zauna wajen mai zaman banza, Sha’aban ya ja motar suka hau titi.
Cikowar da ta ga kofar gidan Hakimi ta yi da bil-adama bai zamo bako a gareta ba, domin an saba yin bukukuwa da daurin aure a gidan Hakimin.
Sha’aban ya yi parking, wannan karon ma hannunta cikin na Baban suka shiga gidan. A dakin Hajiya Karima ta tadda Hakimi da kansa da sauran ‘ya’yansa wadanda suke kusa ba na nesa irin su Hibbah ba, har da Nabilah, da sauran iyayensu mata.
Ga Nabilah na suma ana yayyafa mata ruwa kamar mai iskokai, idan ta farfado ta yi surutai sai ta kara sumewa. Fuskar marikiyarta Inna Indo kamar hadari ta dubi Rahanen da Dacta ya shigo da ita shekeke!. Sai Haj. Karima Maman Nabilan ta asali ce ta nuna mata wajen zama, ta zauna a darare tana ta kuka.
Dacta yake gayawa dan’uwansa a bakin titi suka ganta dama ya kintaci lokacin tahowarsu ne da awoyin da za su dauka kamin su iso, ya je tashar ya daukota sai ya hangota bisa titi.
Hakimi ya ce, “Sannu Rayhanatu kin ji, insha Allahu kin yi sallama da rayuwar maraici, tunda kin samu uba irin MANSUR da nagartaccen miji irin IBRAHEEM da kuma ni surukinki Abdulkadir. Share hawayen nan Rahane, daga yau na tabbatar miki haka kawai ba za su kara zuba ba. Sai ko a kan wata kaddarar daban ba ta maraici da rashin dangi ba.
Muna yi miki barka da zuwa cikin zuri’armu ta alfarma wadda kudurinta shine kiyaye martaba da mutuncin talakawanta. Sannan muna farin cikin shaida miki cewa, mun samu kanwar mahaifiyarki Zinaru wadda ta hanyarta aka samu dangin mahaifiyarki. Sha’aban jeka shigo dasu”.
Ya mike da kansa ya iso har gabanta, ya dora mata warawaren farin zinare (bangles) a kan cinyarta.
“Ga sadakinki, mun daura aurenki da IBRAHEEM MANSUR TAKAI. Babanki ya karbi waliccin ki, na karbi na Da na Ibraheemu. Shaidar da Babanki Mansur ya yi miki ta kyawawan halaye, tarbiyya, biyayya da hakuri, ina fatan ta dore har a gidan aurenki.
Yadda Ibraheem ya karbi zabin da mahaifinsa ya yi masa hannu bibbiyu, muke fatan kema ki karba. Ki yarda cewa baka auren mijin da ba naka ba, kamar yadda baka auren macen da ba taka ba. Komai na rayuwar Dan Adam tun fil’azal rubutacce ne a (Lauhul-Mahfouz). Muna son jin ta bakinki Rayhanah, shin kin amince da zabin Babanki ko kina da uzirin da zai hana ki yin hakan?”
Girgiza kai take cikin kidima da gigicewa. Wannan fa shi ake kira reshe ya juye da mujiya…. Ana bikin duniya ake na kiyama….. Abinda ta samu harshenta na fadi ba tareda ta shirya kalaman daga kwakwalwarta ba kawai shine,
“Idan ni din ban yi biyayya ga zabin Baba Dacta ba…., idan shi bai ji kyamar hadani da Dan da ya fito daga jikinsa ba, duk da kauyancin da talaucin nawa, da lalurar dana samu kaina ciki a baya…. ai ni ba zan ki karbar zabinsa ba ko da tura kaina cikin dakin Zakuna ne.
Yadda Allah zai tambayeni idan ban yiwa iyayen da suka tsugunna suka haifeni biyayya ba, na tabbata haka zai tambaye ni idan ban yiwa Baba Dacta ba.......!” Ta ci gaba da kukan da bata san dalilinsa ba. Ta barsu suna juya tasirin kalamanta a zukatan su.
Daidai lokacin da ta ji sallamar jama’a, ta daga kai a hankali tana kallon su. Wasu harbatsattsun kauyawa ne babu wadda za a ce “gara ita”. Da kyar ta gane Zinaru a cikinsu saboda cindon dake gefen hancinta.
Ji ta yi kamar anyi mata gafara ta mike tsaye tana kallon su idanu a warwaje. Zinaru ta karaso ta rungumeta, wani hamami na baki da hammata ya nausheta, mugun naushi kuwa, rokonta take ta yafe mata, alhakinsu ya sanya ta wulakanta a rayuwarta.
Abinki da ‘yar likitoci, da dai ta samu Zinaru ta saketa ai sa ta yi toilet din Haj. Karima da gudu ta rika kelaya amai cikin sink kamar ta amayar da ‘yan hanjinta. Su sun dauka kuka ta je tana yi, don haka ba wanda ya bi ta.
Da ta wanko fuskarta ta dawo ne Zinaru take mata bayanin sauran matan su hudu, biyu tsofaffi biyu za suyi shekaru arba’in haka, amma wahalar rayuwar karkara tasa sun fi kama da tsofaffin.
Akwai mai fara’a sosai cikin dattijan mai amsa sunan Inna Juma, Zinaru ta ce, “Juma kanwar kakarki ce wadda ta haifi ubanmu, Inna Hanne Yayar mahaifinmu ce, don haka uwa ce a gareni ke kuma kaka a gareki. Ta-sidi da Kubra kannen mahaifiyarmu ne gasu duk a Albasu suke aure, ni kuma a Jahun.
An nemo ni Takai ta hanyar Inna Juma da yake ita tana nan Takai ko bayan mutuwar mijinta Malam Saleh, bata taba haihuwa ba, mu kam akwai tarin iyali. Ina yi miki ta’aziyyar Iya Bilki da Malam Rashidu, ki dubi Allah Rahane ki yafe mini..........”
Kuka sosai Zinaru take yi har Rahane ta ji zuciyarta ta girgiza. Ba ta son kukan babba ko kadan balle Zinaru da take jin ta kamar mahaifiyarta. Duk da bata kasance mai kyautayi a gareta ba.
Ta yi saurin rike hannunta, “Na yafe miki Inna Zinaru, wallahi na yafe muku baki daya Allah ya yafe mana”.
Juma ta ce, “Bar ‘yar banza da kukan munafurci, sai yanzu da kika ganta a matsayin mutum mai daraja da kyawun gani kika san ta yafe miki? Kin taba zuwa kin ganta ko sau daya bayan barinki gidansu? A matsayinta na diyar shakikiyarki?
Al’umma ban san bolar da muka kai zumunci a wannan zamanin ba, na cikin ka kawai shine naka. Sau nawa ina tambayarki inda take kina cewa ba za ki rike ta ba? Duk ma inda take ta je kowa ya yi ta kansa? Sai da na bi diddigi ta wajen marigayi Ado ya gaya min inda ta fada? Kauce daga nan kada in maganre ki........”
“Inna komai ya wuce”.
In ji Haj. Karima.
“Rayuwar duka ‘yar afuwa ce, kema ki yi hakuri. Mun godewa Allah da ya hada ku cikin sauki, a taru duka a yafewa juna komai na duniya dan afuwa ne. Da Ubangijinmu baya yin afuwa a garemu da bamu kawo yanzu ba”. (In ji Hakimi).
Duk cikinsu Rahane ji ta yi Inna Juma ta fi kwanta mata. Ita ce tsohuwar ciki, amma ta fi su kwari da kyan gani, da alamun tsafta a tattare da ita kuma da jin cewa tana sane da ita, har tana neman ta.