Sashe 14
Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gaza nutsuwa da son sanin auren wa za a daura a Takai? Kada zancen Dr. Halima fa ya tabbata, Rayhanah ta zama kishiyarta Dr Mansur ya yi auren huce haushi da ita. Tasan zuciya irin tasa idan ransa yayi mummunan baci bahagon hukunci yake yankewa. Ai sai ta mike ta zari makullin mota ta nufi gidan Dr. Halima a gigice domin maganar ta fi karfin ayita a waya. Dr. Mansur macijin sari ka noke ne, shirunsa a kan al’amari na nufin daukar mataki wanda ba zai yiwa victim dadi ba. Tana tafe da gudu tayar motarta ta gaba ta fice, motar ta gangara ta bugawa wata katuwar mota duk fitilunta suka kwankwatse, Allah ya sota ba abin da ya sameta, sai buguwa da kanta ya yi a jikin sitiyari, sai dan gilashin da ya yanki goshinta. A take jami’an tsaro suka cika wajen suka jawo mata bacin lokaci da biyan cin hanci. Ba ta isa gidan Dr. Halima ba sai da magariba. Dr. Haliman ta ganta afujajan ga jini na zuba duk ya bata tsadadden swiss lace yellow dake jikinta. Ita ta yi mata dressing din wajen ta rufe da plasta, sannan Mamin ta koro mata bayani. Maimakon Dr. Halima ta tayata jimamin abin da take wa gigita da tsoro a kai, sai guda ta je ta sakarwa Radhiyya a ka, ta kira Babanta a take ta sanar da shi. To dama shi Alh. Kabir shanyayye ne, take babu bin ba’asin wannan kagararren aure ya soma gayyatar jama’arsa ta waya. Radhiyya ta kunna (Nancy Agram) tana taka rawa a gaban Mamin har ta ji wani bangare na zuciyarta ya yi mata ba dadi, amma ta kasa nunawa ko a fusaka sai dariyar yake take taya Radhiyyah. Ta kuma ce, “To Radhiyyah kinga dai kokari da fadi-tashin da muka sha ni da mahaifiyarki don samun farin cikinki, kin kuma san Khalipha ba shi ya ce yana ra’ayinki ba. Don haka (handle him with care Radhiyyah), ki kular min da shi don Allah shima ki yi hakuri da shi sai a hankali, insha Allahu komi zai daidaita”. Radhiyya ta rungume Mami har da hawayen farin ciki a idanunta. Haka Mami ta dawo gida a salube gwiwa babu nauyi. Don ko cikakkiyar sallama basu yi da Dr. Halima ba, ba ta tofa wani abu a kan damuwarta ba, she is busy calling her people su zo daurin auren Radhiyya da Khalipha gobe. Idan Mami ta ce ta yi barci a daren yau ita kanta ta san karya ne. Ga azabar ciwon kai, ga radadin ciwo, ga tunani, fargaba da damuwa. Har sha biyun dare Dr. Mansur bai shigo gidan ba, tana falo tana dakon shigowarsa amma har karfe biyun dare babu ko inuwarsa, wannan ya tabbatar mata a Takai zai kwana. Ta soma kiran wayarsa ana cewa a rufe. Sai ta koma kiran Khalipha shima a rufe. Tamkar wadda aka yiwa allura ta zabura ta yo dakin ‘ya’yanta mata, kwayar idanunta sun zurma ciki sosai tashin hankali da zullumi. Abida da Jawahir kowacce na barci a gadonta, sai Azizah a kan sofa take nata barcin. Daga can kusurwar karshe ta dakin ta hango Rahane tana kan sallaya da hijabin da ya rufe dukkan jikinta sai fuska da tafin hannu, amma ko kafafunta ba a gani, tana rike da Alkur’ani bugun Misra tana karantawa amma ba a fili ba. Dai-dai lokacin da ladanin wani masallaci dake makwabtaka dasu ya kwalla kiran sallar Asubahi. A yadda Mami ta nufota a fusace kamar kurar dake jin yunwa ya sata rufe Alkur’anin da sauri ta aje gefe, tana karanto duk addu’ar da ta zo bakinta, don ta yi zaton Mami rufeta da duka za ta yi. Bayan ita dinma bata da lafiya, adalilin duk wasu hanyoyin sadarwa tsakaninta da Khalipha sun yanke. Baya neman ta, ita kuma idan abu ya dameta, bata iya gayawa kowa, kawai tasa a ranta Khalipha ya gama yayinta ne dama ba aurenta zai yi ba, yaudara ce kawai irin tasu ta ‘ya’yan gata. Ya samu wata dai-dai da shi, ita kuma ya rufe duniyarta. Wannan ciwon da Khalipha ya ji mata a zuciya, shi ya kassara ta, ciwo take a tsaitsaye duk da bata kwanta ba. Wani bangare na zuciyar tata kuma sai ya ce, “To ai Khalipha ba shi da laifi, bai yaudareki ba, ke kika yaudari kanki, da kika dauki dukkan amana da soyayyar duniya kika bashi, da saninki kan cewa kina zaman ‘yar karo ne a gidansu amma kika zarme kika wuce gona da iri, wai shine life-mate dinki......” Wannan tunanin din dai, bai rage komi daga son da takewa Khalipha ba, sai beken kanta da take gani. Ba ta gama tunane-tunanenta ba da mamakin abin da ya kawo Mami dakinsu yanzu da asubahi haka kamar Damisa, ta ji Mamin ta finciko ta babu ko takalmi a kafarta. Figarta kawai take har a kan step din bene wanda zai sadata da reception din gidan, tana buguwa tana komai amma Mami ba ta fasa janta ba sai da ta dangana da gate. Ta bude kofar wucewar mutum ta cillata wajen gidan tana cewa, “Ki tafi gidan ubanki! In ya mutu ne ki nemi danginki. Ba nufina in wulakanta ki ba, amma ke kin dauko hanyar wargaza min rayuwar iyali, kin rabani da mijina da ‘ya’yana da kwanciyar hankalina. Taimako ba hauka bane, Allah ya gani na yi iya wanda zan iya. Ina rokonki Rayhanah kada ki sake waiwayen inda muke, ki je kauyenku ki yi aure ya fiye miki da ci gaba da zama cikin iyalina kin ji na gaya miki”. Garammm! Ta rufe kofar. Karar kofar kenan da ta razana Malam Dahiru dake sallah ya fito da gudu ya ga shigewar Mami da kulle kofofin reception dinta da ta yi. Sai kuma ya ji shesshekar kukan mace a wajen get dinsa. Da azama ya bude ya fita yana haskatata da tocilan dinsa. “Wace ce a nan?” Ya tambaya cikin barazana, a lokacin da kwayar idonsa suka shaida wadda ke tsugunne a gefe tana kuka..... “Rayhanatu?” Ya ambaci sunanta cikin kokwanto. Hawaye kadai ke zuba ta ce, “Taimakamin da kudin Motar da zai kai ni Takai Malam Dahiru......... don Allah ba don ni ba......” Ta ci gaba da kuka mai matukar ban tausayi. A kidime ya ce, “Rayhanatu ba inda za ki, shigo daga nan, sai Dacta ya dawo koma mene ne ba zan barki ki tafi ba don kin yi ma Mami laifi. Ki yi hakuri ki daina kukan ya dawo”. Tana kuka sosai ta ce, “Malam Dahiru za ka iya bani ko ba za ka bani ba?” Yadda ta fiddo masa manyan idanunta dake jike jagab da hawaye sun kuma kada sunyi jawur, sai jikinsa ya hau bari. Ya ce, “Zan shiga matsala ne Rayhanatu idan na barki kika tafi....... ki ceci hanyar cin abincina ni da iyalina kada ki yi sanadin rabuwata da karimin mutum irin Babanku. Ita ma dai Hajiya wane irin laifi danka zai yi maka ka kore shi? Korar ma cikin duhun Asubahi?” Da ta ga Malam Dahiru ya tsaya ya tsinke mata da surutu mai ban haushi a gareta, ba kuma shi da niyyar taimakon nata. Bakin ciki ya yi bakin ciki a zuciyar Rayhanah, sai kawai ta tattare doguwar jallabiyyar dake jikinta ta yanka da gudu, gudun da ba ta taba zaton ta iya ba kamar filfilwa a lokacin gari ya soma haske. Ko kabarin iyayenta ne ta yarda ta koma da ta kara kallon ko da get din gidan su Khalipha, Abida da Mami, da suka yiwa zuciyarta rauni mai zurfi da ba zai taba warkewa ba. Malam Dahiru dai girma ya soma cimmasa, ba zai iya wannan gudun da Rahane ta fyalla ba balle ya kamata. Sai ya dau wayarsa ya kira Dacta ya gaya mishi iya abin da ya gani. Ga mamakin Mal. Dahiru, Dacta bai wani razana ba, bai yi mamaki ko fadan da ya yi tsammani ba, cewa ya yi da shi, “Don me baka ba ta kudin motar ba? Hau babur dinka maza ka bita ka ba ta kudin ka yi tafiyarka”. Ya jefa waya a aljihunsa ya tashi babur aguje shima ya bi hanyar da ta bi wadda za ta sadata da bakin titi. Unguwar Lamido Crescent unguwa ce a Kano ta wadanda suka san muhimmancin BIRO (‘yan boko). Babu ruwan kowa da kowa, ba cinkoso ba sa-ido kamar kana Abuja. Don haka ko gilmawar motoci babu a dai wannan lokacin. Sanda Mal. Dahiru ya hawo kan titi ya hangota can gaba da shi tana bin gefen titi sauri-sauri gudu-gudu kamar mai yin Safah da Marwah. Ita kanta ba ta san ina take jefa kafarta ba, fatanta kawai ta ganta a Takai, koda akan iska ne, kuma hawaye basu bar tsere a kan kundukukinta ba tana ta sharewa da zurmemen hijabinta. Da ta ji karar babur a bayanta ai sai ta kara artawa a guje, shima kuma ya nuna mata mutum da inji ba daya bane, ya sha gabanta har ya dan bugeta ta fadi a kan titin. Ya taimaka mata ta tashi ya rike hannunta gam-gam domin kiciniyar kwacewa take tana rokonsa kada ya maidata gidan Dr. Mansur, ya tafi ya kyaleta tunda ba zai taimaka mata ba. Mal. Dahiru ya ce, “Na rantse da mahaliccina ba zan mai da ki ba. Hau bayana in kai ki tashar Mariri in sa ki a motar Takai”. Kukan dai bai tsaya ba, amma ta ji sa’ida a ranta. Ta dane bayan babur ya ja suka tafi. Lokacin gari ya fara haske misalin karfe shida na safiyar Lahadi kenan. A tasha Mal. Dahiru ya sata a motar Tsangaya, ya sanar dasu a Takai za su sauke ta. Ya kirgo kudin da suka bukata ya basu ta shiga gefen taga daga baya ta zauna. Tana share idonta tana dagawa Mal. Dahiru hannu da godiya. Ya zagayo tagar da take ya mika mata naira dari biyu da kunshin kosai mai zafi. Hannu biyu tasa ta karba, tana gode masa. Ta share hawaye ta ce, “Sai wata rana...... Malam Dahiru na gode a gai da Sahura”. (Matarsa). Bai bar tashar ba sai da ya ga tashinsu, bayan motar ta cika. Shima sai ya ji danshi a kan fuskarsa, yarinya-yarinyar kirki, me ya raba ta da mutanen kirki irin wadannan? A