Sashe 12
Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
** **
“Daddy yaushe za ka dawo?”
Khalipha ya tambayi Baba Dacta a raunane, bayan sun gaisa ta waya. Maimakon ya ba shi amsar tambayarshi sai ya ce, “Ya ya na ji maganarka so cool, wani abu ya faru ne?’
Ya girgiza kai cikin karin hawaye ya ce, “Eh to, magana nake so muyi ta fahimta.....”
Sai kuma ya yi shiru.
“Ba za a iya barin maganar har sai na dawo ayi ta face-to-face ba? Tunda na lura mai nauyi ce?”
“To shi kenan Daddy, yaushe za a dawo?’
“Yanzu haka na taho on transit nake a Germany. Zuwa asubahin gobe ina Kano insha Allahu”.
** **
Dawowar Daddy gida lafiya, da kuma ganin yanayin fuskarsa bai canza ba ko kankani, yasa Dr. Asma’u cikin kokonton anya Khalipha ya yi abin da ya ce zai yi bisa umarninta? Irin kayan da ake shigowa dasu ana jibgewa a (store) ya kara tabbatar mata da lallai Khalipha ya rainata.
Kayan furnitures ne ‘yan ubansu-ubansu da manyan jakunkunan zamani shake da duk wani nau’in suttura ta kwalliyar mata da suka fi kama da kayan lefe.
Dr. cikin walwala yake matuka, a lokacin da yake nuna mata kayan, yana yi mata bayanin lefen Khalipha ne. Ya kaikaice ya zaro warawarai guda shida na farin zinare daga aljihunsa, ya ce ga shi ta adana, shine sadaki.
A wannan lokacin ya kwantar da harshe ya ce,
“Asma’u na san bani da kalaman wanke kaina daga daudar mai laifi a gareki, amma ina baki hakuri, bani kuma da hannu a ciki. Kamar yadda na ce ba zan hada ba ban hada ba, su suka hada kansu, ni kuma na ture komi, na zabi in cika umrnin Ubangiji in ya so in yi kaffara a kan alkawarin da na yi miki. Tsakanin ‘ya’yanki da ‘yar amanar da Allah ya bamu.
Zan iya cewa ban karya alkawari ba, tunda kuwa ban hada soyayya tsakanin Khalipha da Rayhanatu ba. Ki sa fahimta a cikin lamarin nan, ki sa albarka, ki dauki duniya da sauki. Khalipha ke son auren Rayhanah, ni kuma na ba shi da na tabbatar da amincewarta. Ga wannan.....”
Ya tura mata bandir din bugaggen (invitation card) na daurin aure da yasa aka buga masa a Dublin..
Ya kare da cewa, “Jibi Lahadi insha Allahu za a daura auren a gida Takai, Hakimi shine waliyyinta. Don haka ga wannan”. (Ya tura mata ATM Card dinsa na bakin (Gruaranteed Trust).
Ya ce, “Ki dauki abin da zai isheki, daga naira dari har zuwa miliyan biyu na lamince miki ki fara shirye-shiryenki. Na taho da komai na kawata gida, kayan kithcen ne sai ku mata. Da sauran abubuwan da babu sai ki karasa. Duk wasu activities da kike ganin za a yi ayi, amma ban da wanda za a hada mata da maza. Kin yi hakurin Mamina kin fahimceni?”
Sakatoto! Ta yi tana mishi kallon takaici, kamar ta amayo zuciyarta ta huta. Ta so yin kissa ta karya, amma ba halinta bane, don ba ta iya ba. Wadanda take yi a baya ma duk Dr. Halima ke koya mata, ga shi kuma ba ta zaci haka ba, ba ta koyo yadda za ta karbi zancen ba.
Sai kawai ta aje warawaran da ya dora mata a cinya da katinan daurin auren a nan gabanshi ta mike ta yi dakinta ba tare da ta ce da shi komi ba.