← Book details Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 23

Sashe 17

Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ASALINSU
Su ‘yan asalin Takai ne gaba da baya, basu da wata daukaka ko wani mulki ko suna (reputation) kawai bayin Allah ne da suka fi karfin abin da za su ci, da wanda za su daura. Da ita da Gwaggo Jummai kakar su Rahane uwarsu daya ubansu daya.
Lokacin da Malam Rashidu ya fito neman auren Rahane (Yalwati) dukkansu babu wanda ya marawa al’amarin baya, ba don komi ba kuwa sai don cewa ba haifaffen Takai bane bakon haure ne daga Tsangaya, wani kauye cikin karamar hukumar Albasu. Amma ba don karancin samunsa ba.
Ko da Rashidu ya yi alkawarin ba zai raba ‘yarsu da mahaifarta ba basu yarda ba, Babanta ne ya yi musu bazata ya karbi sadakin Rahane daga Mal. Rashidu, ya ce ko bangon duniya ne ya kaita, ba inda aure baya kai mace, balle ina Tsangaya ina Takai? Ban da neman zance irin na mata?
Sai kuma Rashidun ya basu mamaki da soyayyar da yake yiwa Yalwati. Ya je ya tattaro komi nasa daga mahaifarsa, bai bar ko allura ba. Dama gaida mahaifiyarshi Iya Bilki ke kai shi Tsangaya sai ya je ya dauko abarsa ya ajiyeta kusa da shi, uba ya jima da rasuwa, dangi sun kare, ita kadai ta rage mishi. Ya kawo ta ya ba ta daki a gidan mahaifin Ado da yake haya a ciki.
Bayan mahaifin Ado ya rasu, Ado ya gaji gidan. Zamane suka yi mai dadi shi da Rahane da mahaifiyarsa, domin Iya Bilki ba tsohuwar banza ba ce ta san abin da take yi. Ashe zaman nasu na dan takaitaccen lokaci ne (shekara biyu) Allah ya karbi ranta wajen haihuwar Rayhanah.
Don haka iyayen Yalwati (Rahane) basu ji ko dar wajen ba shi Zinaru ba, a lokacin da Iya Bilki ta nemi hakan. Ta je ta zuba musu rashin mutuncinta ta fito ta koma gidan tsohon mijinta a Albasu.
A lokacin da Iya Bilki ta rasu Inna Juma ba ta Takai tana birni tana wanke-wanke tsayin wasu shekaru masu yawa tun bayan rasuwar mijinta Malam Saleh, ba ta kara jin duriyar Rahane ba sai da ta dawo birni take tambayar al’ummar kauyen, su ma suka ce basu sani ba, amma dai kowa ya san sunyi rikici da Ado, wanda shima ya dade baya kauyen sai da cutar zamani ta dawo da shi jinyar dole gida.
A bakin Ado ne ya ce ta bincika gidan Hakimi shi can ya barosu. Inna Juma ba ta yi kasa a gwiwa ba ta ci gaba da binciken Rahane da Zinaru har Allah ya hada su.
Ta kawo gwauron numfashi ta daga ido tana duban Rahane, wadda barci ya yi awon gaba da ita. Ta mike ta kashe mata fitila ta kunna mata na’urar sanyaya daki, da yake ta yi rayuwar Birni ba ta da duhun kai sam. Ta jawo kofar dakin ta nufi wanda aka ce shine nata.
****
Chapter 17 · 0% Book details