Sashe 6
Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To haka rayuwar Rayhana ke tafiya a gidan Dr. Mansur, cikin dadi ko akasin sa. Dama rayuwar ta gaji haka. Watarana zuma, watarana madaci. Mami ta daina kyararta, amma fa bata shiga sha’aninta kamar da. Girman da yake bayyana a tare da Rahanen yana bata tsoro, yarinya ta koma kamar black American, kirar jikinta da yanayin tsayinta mai sa maza su kasa dauke ido a kanta ne. Ga zigar Dr. Halima wadda ta fi komai yamutsa mata lissafi. Ta kan ce idan ba ta raba yarinyar nan da gidanata ba, to kuwa ta shirya shan mamaki a gaba. Asiri kuma ko ta ina Halima bankawa Khalipha take don ya yarda da maganar Radhiyyah, shi da ma kwata-kwata babu wanda ya san halin da yake ciki. Su ba kudi ne basu da shi ba, ba kuma wani abin hannun Khalipha ko iyayensa suke hange ba, kawai tana son samawa ‘yarta abin da take so ne, don ta samu kwanciyar hankalinta. Cikin wannan tsukin Khalipha ya dawo Morocco, ya kammala kwas din da aka tura shi, ya samu karin girma a ofis dinsu. Kowa ya sha tsaraba amma ta Rayhanah (is special). Kaya ne na matan Morocco zabga-zabga, wasu lafiyayyun dogayen riguna kala-kala guda goma sha biyu, da Pakistan da Abayat suma kowanne dozen guda. Ya yin da kannensa suka tashi da guda shida-shida, doguwar riga biyu, Pakistan biyu da Abayoyi guda biyu. Wannan karon kam Mami ta kara karfafa zarginta, ta kuma sa ido sosai a mu’amalar Rahane da Khalipha. Da Khalipha ya dawo ya samu wannan labari da bai taba samun mai dadi kamar shi ba, wato warkewar Rayhanah. Daki ya shiga ya gabatar da sallar nafila raka’a biyu ya yiwa Ubangiji godiya, ya yiwa Baba Dacta addu’a, ya roki Allah ya ba shi karfin zuciyar fuskantar iyayensa a wannan lokacin a kan bukatarsa. Sai dai abin da ke bakanta mishi rai kwarai shine, sabuwar mu’amalar da Mami ta tsiri yi da Rahane, na rashin sakar mata fuska, haka ko magana take yi da Khalipha idan Rahane ta shigo wajen sai ta yi shiru. Sannan idan Rahanen ta gaisheta ko ta yi mata magana, amsawa take a ciki kamar ba ta so. A sati daya da Khalipha ya yi cikin gidan yana hutawa kamin ya koma ofis Monday ya lura da hakan. Ba ta da zancen da take yi masa sai na Radhiyyah, and he is not interested at all. Ta kasa ta tsare ta hana shi kebewa da Rahane da yake tana cikin hutu. Ko yaushe tana tare da shi, abinci tare suke ci, fita ma in ta kamata sai ta ce shi zai kaita, a haka dai har ya cinye satin shi da Rahane sai dai ya hango ta daga nesa ko in sun fito cin abinci. Ranar Lahadi da yamma ya koma Abuja ya shiga sabon ofis dinsa, wanda bai sa shi farin ciki ba ko kadan, don tunaninsa da zuciyarsa basa kai, sun yi nisa cikin zuzzurfar soyayya marar misali. Khalipha baya da zabi banda ya kara kauracewa gidan su, baya son bayyana abin da ke zuciyarshi yanzu, amma zuciyar ta ki jurewa. Ya kan kira iyayen a waya su gaisa a kai a kai ya kuma ba da uzirin rashin samun zuwa da aiki ya yi yawa. A wata Seminar likitoci na federal govt. da Dr. Mansur ya je Abuja ya yi tunanin bari ya kai ma Khalipha ziyara gida tunda Asabar ce baya zowa ofis. Gidan Khalipha da ma’aikatar su ta ba shi yana nan a (Maitama). Daddy ya yi horn maigadin ya bude mishi yana barka da zuwa. Daddy ya tambaye shi ko maigidana yana nan? Ya ce, “Eh, yana nan, amma gaskiya a tsukin nan baya ganin kowa, ya kuma yi umarni gare shi cewa ko waye ya zo neman shi ya ce baya nan ko ya same shi a ofis. Yanzun ma don ya ga Daddy ne shi yasa ya bude”. Daddy ya faka motarshi a gefe cikin rumfar adana motoci a kalla guda uku, ga ta Khalipha nan guda daya kirar (Cadillac Srx) da canzo daga Morocco, daga ita ba wata. Ya fito ya doshi (door-bell) ta falon yana dannawa. Jibril da ke wankin kayan Khaliphan a bayan gidan ya zo ya gaida shi, sannan ya ce, “Oga bai da lafiya Alhaji, kuma ya ki yarda cewa ba shi da lafiyar balle ya je asibiti, ni dai na yarda ba shi da lafiyar ko abinci ban yi zaton yana ci ba, don ya hanani yi mishi girki sai dai kullum ya yi ta aikena siyen abinci, kuma yadda na kawo haka nake fiddashi abin da ya taba ba yawa. Ba zai bude ba, da dai ka kira shi a waya”. Da sauri Daddy ya dauko wayar yana kiran Khalipha sannan ya yiwa Jibril inkiya da hannunshi alamar ya tafi. Anyi sa’a wayar Khalipha tana kunne, kuma ya sanyata a caji nesa da shi kadan, yana kwance gefen gadonshi da ruwan tokan (pjs) a jikinshi, ya tasa kwamfuta a gaba yana shigar da sakonni. Sarai ya ji kararrawar amma bai yi niyyar budewa ba, sai kuma ga kiran waya dole ya mike zuwa gareta, ga mamakinsa kiran Daddy ne. Da sauri ya amsa wayar. Daddy ya ce, “Ina kofar falonka”. Cikin rashin kuzari ya bude kofar. Daddy ya tokare hannayenshi jikin kofar falon yana kallon shi. Gaba daya ya zube ya yi jajir, idanuwansa manya masu sheki sun zurma ciki, hakan bai hana shi bayyana a kyakkyawansa ba. Yana shirin russunawa Daddy ya yi saurin kama hannunshi suka idasa shiga cikin falon, ya zaunar da shi a gefensa cikin bakaken (leather seats) din da suka yiwa falon kawanya. Kafin Khalipha ya furta gaisuwa Daddy ya katse shi da cewa........ “Me ya faru? Me ya same ka, ka kulle kanka kai kadai cikin gida? Me ya zabgar da kai haka? Mece ce damuwarka Khalipha? Gaya min maza, wannan ba Khaliphana da na sani bane”. Sai ya fada jikin mahaifinsa shi kuma ya rungume shi sosai, ba kuka yake yi ba, ajiyar zuciya yake yi. Ji ya yi zuciyar tana sanyi daga zafi da suyar da take yi. Wani bangare na zuciyarsa na karfafa shi da cewa, ka yi amfani da wannan damar da Allah ya kawo, ka fadawa Daddy abin da ke neman kwantar da kai ya salwantar da ci gaban rayuwarka. Daddy uba ne mai fahimta, da akida daban da ta Mami. Babu haufi zai fahimceka, ya mallaka maka abin da rai da zuciyarka ke so. Walwalarka da kuzarinka su dawo, ka dauko Rayhanah ku rayu tare har abada, ku haifi ‘ya’ya masu albarka har zuwa karshen rayuwarku. Duka wannan tunani Khalipha ya yi shi ne cikin ‘yan dakikan da basu wuce goma ba. Daddy bai katse shi ba, ido ya zuba masa yana sauraren amsar bakinsa. Khalipha ya dago ya kalli Daddy idanunshi sun kada sun koma brown dinsu masu sheki dake cike taf, da kwalla, wadda babu alamun za a ba ta damar zubowa saboda dauriya irin ta namiji da rashin son nuna karaya. Ya maida kai ya sunkuyar, sakamakon kwarjinin da idanun mahaifin nasa suka yi masa. Amma fa wani bangare na zuciyarsa na cewa da shi, “A kul! Ka bari wannan damar ta subuce maka...” Cikin rawar murya da sarkewar harshe ya ce, “Daddy… Rayhanah…. Rayhanah nake so ka aura mini”. Dr. Mansur bai tambaye shi wace Rayhanah ba, tunda Rayhanah daya suka sani a duniya dukkansu, basu san wata mai wannan sunan bayan ita ba. Dr. Mansur bai yi mamaki ba, shi kansa jikinshi na ba shi akwai wani boyayyen al’amari game da Rayhanah a kanshi da ‘ya’yansa tun ranar da ya fara ganinta jikinshi ya ba shi hakan. Wannan yarinyar rayuwarta cikinsu na nuna al’amura da dama wanda Allah kadai ya sani. Sai dai kuma kash! A inda ya yi fatan al’amarin ya kasance ba a can ya kasance ba. Anyway a hakan ma baya da ja, kuma yayi farin ciki, amma yadda yasan yunwar cikin sa haka yasan cewa Mami ba za ta taba amincewa ba, musamman da yake ta fishi power a kan Khalipha. Tabbas Khalipha ba wani abu ke damun shi ba sai soyayya, irin soyayyar da ya yiwa Mami mai azabtarwa, wadda ba a lokaci daya take faruwa ba, a hankali take shigar mutum ta yi masa kisan gilla batareda ya sani ba, tayi masa babakare a zuciya da gangar jiki. Ta hana shi sukuni da nutsuwa har sai ya mallaki abin da take so. Wannan shirun da Daddy ya yi ba karamin kada Khalipha ya yi ba, tsoron shi Allah, tsoron shi kada Daddy ya ce ba zai ba shi Rayhanah ba ko ba zai yi mata aure yanzu ba. At 34, yana cikin wani mataki na tsananin bukatar diya mace, amma fa Rayhanah kadai. Ga dimbin mamakinshi Daddy murmushi ya yi ya dafa kafadarsa ya ce, “Wannan shine abin damuwa Babana? Har a sanya zuciya cikin takura? Baka tsoron hypertension kake wasa da aiki da lafiyarka? Rayhanah ai ‘yata ce kamar yadda kake Da a gareni. Idan har kana so ita ma tana so me zai hana in mallaka muku juna? Ni ai abin farin ciki ne a gareni in aurar da Rayhanah a hannun da na tabbatar ko bayan raina ba za ta wulakanta ba. A da, na yi niyyar ba zan aurar da Rayha da su Abida ba sai sunyi zurfin karatu, amma tunda har haka ta faru, bani da ja da yin Allah. Abdallah jeka nemi so wajen Rayhanah, idan ta baka ni mai daura aure ko gobe ne. Alas! Babu sauran damuwa ko?” Hawayen farin ciki suka zubowa Khalipha, ya rungume Daddy yana kuka sosai. Daddyn na share masa da hankicinsa yana cewa, “Haba Babana, tsakanin uba da dansa ai ba godiya. Duty na ne as a father in tabbatar da farin cikinku in har bai sabawa addini ba. Hakkina ne in yi muku aure, saboda kun kai munzali, amma sabgogin neman duniya suka sha’afar dani ga yin hakan, har sai da ka ankarar dani. Nima na gode Babana. Ya isa kukan nan bana son shi, ya isa!” Haka ya ci gaba da share mai hawayen har kunya ta kama Khalipha. Daddy da kansa ya je kitchen ya dauki tray ya bude firij ya debo