← Book details Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 23

Sashe 1

Rayuwar Rayhana Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

 [12/24/2019, 21:47] Takori: RAYUWAR RAYHANAH - 2
Ji ta yi kamar an dora mata dutsen Uhudu a kanta, sabida nauyin da kalamansa yayi mata, a gigice ta dago ta dubi Khalipha jikinta na bari na rudewa da gigicewa.
Ta shiga waiwaye-waiwaye kada wai ko wani ya ji abinda Yaya Khalipha ya ce. Amma ga jin dadinta kowa harkar gabanshi yake yi da iyaye da ‘yan’uwansa nesa dasu sosai, don sai da ta ware kanta can nesa da jama’a kamin ta zauna.
Shi kuwa Khalipha ko a kwalar rigarshi, bajewa ya kara yi a gabanta yana gaya mata duk kalaman soyayyar dake fitowa tun daga karkashin zuciyarsa ba daga fatar baki ba. Idanunshi a lumshe, ya yi kyan da bata taba lura ashe yana da shi haka ba.
Karkarwar da jikinta ke yi ya karu, don Khaliphan ya ki yin shiru. Ita kuma gaba daya a gigice take kada kannensa dake matukar ganin girmansa su zo su ga abin da yake yi, wanda ita bata sani ba.
Sauran kadan ta tsuge da zawo da ta hango Jawahir ta nufosu da sassarfarta. Da karfi ta ce, “Yaya Khalipha ka cika min hannu, ga Jawahir nan”. Lokaci guda kuma tana kici-kicin kwace hannun nata daya rike cikin nasa da karfi kamar zai balla ta.
Amma Khalipha ko gezau bai yi ba, juyawa kawai ya yi yana tsimayen isowar Jawahir din.
Mikewa ta yi da karfi ta fizge hannunta saura kadan ta fadi. Cikin zafin nama ta zauna a kan kututturen iccenta tana kokarin dai-daita numfashinta, nutsuwarta, bugun zuciya da yanayin fuskarta kafin isowar Jawahir.
To ita ma Jawahir din duk da ta ga abin da ta ganin, amma da yake wayayya ce ba ta nuna komai a fuskarta ba, a zuciyarta cewa ta yi, “Na san wata rana irin wannan na zuwa, tsakanin Raiha da Yaya Khalipha, Intimacy din ya isa, haka kulawar da suke wa junansu a gida kadai abin a digawa ayar tambaya ne.
A gaban Khaliphan ta zube tana dariya.
“Yaya Khalipha yau kai ne da visiting, ina Mami ina Zizah? Ina Daddy?’
Ta jefo masa tambayoyin duka a lokaci daya bakinta kamar zai tsage don fara’a da farin ciki.
Ya ce, “To duk wadannan queries ni kadai Jawahir, wanne zan fara amsawa?”
Dariya ta yi tana kallon Raiha ta ce, “Don Allah Rayha Yaya Khalipha bai kara kyau ba?”
Ta rausayar da kai ta ce, “Ni bana yiwa mutum kallon kurilla”.
Ta ba shi dariya sosai, ya ce, “Har da ni RAHANE?”
Ko don albarkacin wannan suna da ya kirata da shi ya isa ya sata dariya.
Ya mike yana duba agogon hannunsa, lokacin rufe makarantar ya karato.
Ya ce, “Ku zo muje mota ku kwashe kayanku har na wannan shashashar (Abida)”.
Suka mike suka bishi har boot din motar ya kwaso ya basu. Haka ya ware na Rahane. Wannan karon ma Jawahir ta diga ayar tambaya, amma wayewarta yasa ba ta nuna komai ba. Saboda yawan kayan sai juniors dinsu suka sa suka tayasu kai kayan hostel.
Tun daga wannan ranar Rahane ta kasa samun sukunin zuciyarta. Tunanin Yaya Khalipha da al’amarinshi day a zo mata dashi kadai zuciyarta ke yi dare da rana, yini da safiya.
Sai dai bata barin hakan ya shafi karatunta ko kadan saboda alkawarin da ta daukarwa ranta na farantawa Baba Dacta wannan karon da kyakkyawan sakamako. Amma fa duk sanda ta kwanta, ko ta kadaice tunanin Yaya Khalipha take yi. Ba abin da take so irin ta ganshi, ko ta ji muryar nan tasa mai sanyi yana cewa ‘RAHANE’.
A haka suka zana WAEC da NECO har da JAMB, suka yi sallama da Ulul-Albab. Ya yin da Rahane ta zana (qualifying) wato jarrabawar shiga aji shidda.
Sun zo gida hutu a lokacin Khalipha an tura shi kwas a kan aikinsa a Nigerian Embassy na kasar Marocco. Wanda zai yi tsayin watanni tara.
Khalipha ya yi murna da wannan tafiya, ko babu komai zai yi nisa da Rayhanah na dan wani lokaci mai tsaho. Ba tare da al’amarin dake zuciyarshi ya bayyana ga kowa ba. Ya na da relief tunda ya bayyana shi gareta. Duk da bai san me ke wakana a tata zuciyar ba.
Sai dai kuma ya bar ita Rahanen cikin dabaibayi mai yawa, da soyayya mai cin zuciya. Duk da ita kanta ba ta san cewa soyayyar ce ke dawainiya da ita ba.
Ta san dai tunda Yaya Khalipha ya tafi ta shiga kewa, rashin kuzari a cikin gidan da makaranta duka. Tunda ya tafi ko waya basu taba yi ba, domin Baba Dacta ya hana kowaccensu rike wayar hannu, ya ce sai ya ga kamun ludayinsu a jami’a tukunna. Hakan ne yasa ko Khalipha ya yi waya da Mami ko Daddy sai dai ya a ce a gaishe su. To da haka rayuwar ke mikawa.
Chapter 1 · 0% Book details