← Book details Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 21

Sashe 9

Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Sai yanzu ne kewar Iya Bilki ta dawo mata sabuwa, ta shiga kuka a hankali amma mara amo, domin ta toshe bakinta da dan kwalin kanta.
Karfe takwas da rabi dai-dai na safe motar Mami ta shigo farfajiyar gidan, I.M ke tukin, shima a asibiti ya kwana.
Jefi-jefi suna hirarrakin da suka shafe su shi da mahaifiyarsa, ya yi parking din motar a muhallinta yana cewa,
“Nifa gaskiya Mami zaman yarinyar nan da Daddy ya kwaso bai min ba, kuma ba matsayin ‘yar aiki ba, duk taimakon da ya kamata ya bata na likita da patient dinsa ai ya ba ta, hatta hearing aid din fa shi ya saya da kudi ba kadan ba.
To na mene ne kuma na tahowa da ita? Shi bai san yanzu zamani ya canza ba (sunan litafin Takori mai zuwa) Kowa ta kansa yake, ka jawo mutum inuwa shi kuma da ya ji sanyinta ya turaka rana”.
Mami ta ce, “To ni dai babu ruwana mun riga mun rufe wannan babin da shi. Da ai na kowa ne HIMU (sunan da take kiranshi kenan wato Ibrahimu)”.
Ya kyabe baki bai sake cewa komai ba, ya dauko jakar Mami da lab-coat da sauran takardunta suka shige ta kofar kicin.
Firji ta fara budewa ta dauko robar ruwan FARO mai rangwamen sanyi ta sha tambulan biyu.
Al’adarta kenan a kullum da safe kafin ta sanya komi a cikinta yana da fa’ida sosai, ga lafiyar jiki da ta zuciya.
Ibrahim dakinsu ya wuce don ya yi wanka, jinsa yake kamar a kwatami saboda rashin wankan. Mutum ne mai masifaffar tsaftar gaske, sannan mai baudadden hali.
Abin nufi, da wuya ka gane inda Ibrahim Mansur Takai ya sa gaba, ba za ka iya gane farat daya yana da kirki ko ba shi da shi ba, mahaifinsa kadai ya san kansa, shi kuma kadai ya iya tafiyar da shi da baudadden halin nasa.
Ibrahim na da kyau, wanda kallo daya za ka yi mishi ka ga hakan. Wankan tarwada, mai tsayi da rashin kauri. Yana da siririn saje a gefen fuskarsa mai laushi da sheki, da ka ganshi ka ga Mansur Takai, ta karan hancin, da manyan idanunsu.
Sannan mai tattsauran ra’ayin akidun Malam Nasara. Sai dai kuma mutum ne mai riko da sallah, tabon sujjadar dake tsakiyar goshinsa kadai ya isa shaidar hakan.
Ba za ka iya dorar da wani abu a kan halayyar shi ta zahiri da badani ba, wannan sai mahaifinsa, duk yadda kuke da shi kuwa.
Nutsuwa irin ta Ibrahim daban take, za ka iya ganin hakan a kan ko me yake yi, kamar cin abinci, sallah, tafiya da duk wani motsi da zai yi ko a karatun likitancinsa.
Dacta Mansur na son Ibrahim son da baya yiwa Yayansa Khalipha, saboda komi nashi Ibraheem ya dauko. Magana in ba mai muhimmanci ba ce Ibrahim baya yinta, ko hira ake cikin abokan karatu Ibrahim baya tofa nashi in ba mai ma’ana ba.
Chapter 9 · 0% Book details