← Book details Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 21

Sashe 5

Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jama’a makota suka soma cece-kuce kan cewa yau sati biyu kenan basu sa Malam Rashidu da Rahane a idanunsu ba, sun dauka ma barin garin suka yi ba tare da sun yiwa kowa sallama ba.
Dr. Mansur ya ciro malun-malun din da yake snaye da ita ya sanyawa Malam Rashidu. A nan ya soma gaya musu yau sati uku kenan Ado ya kulle shi yana azabtar da shi a kan sai ya fada masa inda ya kai Rahane don kar ya bashi aurenta. Bayan shima bai san inda suka tafi ba ita da Iya.
Kowa ya ce, “Ado zai aikata fin haka. Allah ya saka masa”.
Dr. Mansur ya ce, “Sunyi hatsari ne ita kadai ta sha aka kaita asibitin su, Allah ya yiwa Iya rasuwa tare suke da gawarta”.
Malam Rashidu ya rikice da kuka shi yana yi Rahane na yi. Jama’a na ambaton “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Allah ya ji kan Iya Bilki, Allah ya yi mata rahama”.
Kan ka ce meye wannan jama’ar Takai ma’abota kara da hadin kai sun cika kofar gidan. Tare da Dr. Mansur da I.M aka sallaci Iya Bilki, aka dauketa zuwa gidanta na gaskiya. Dacta da I.M suka wuce gidan Hakimin Takai.

Dr. Mansur dan asalin garin Takai ne. Da shi da Mai-Martaba Hakimin Takai cikinsu daya, sai dai shi Mansur dan boko ne na a buga a jarida, kwata-kwata baya sha’awar sarautar tasu, ko zaman garin su sai dai ya zo da ziyara, yana Kano tare da iyalinsa. Shekararsu goma a kasar Ireland suna karatu shi da mahaifiyar su Ibraheem (Asma’u) wadda ‘ya’yanta suke kira (Mami).
Mami ‘yar asalin garin Jos ce, (arnan Jos), a da, bata da addini, sunanta (Anita Shiyana). Sun hadu da Dr, Mansur a jami’ar TRINITY dake (Dublin). A hannun Mansur ta karbi musulunci ta kuma rike shi da kyau, ya sanya mata sunan mahaifiyarsa (Asma’u) wadda ta dade da rasuwa, don haka shima Mamin yake ce mata.
Mami cikakkiyar likitar yara ce (paediatrician) da ta san aikinta. Duka yaransu biyar, kowane da rata sosai tsakaninsa da wanda yake bi a haihuwa.
Rayuwar Mami zallanta na (Irish) wato na mutanen Ireland ne, ga masifar son ‘ya’ya. Ba ta son kowa ya rabe su, daga ita sai ‘ya’yanta sai mijinta. Sabanin mijin, Dr. Mansur mutum mai kara da kawaici, ga faram-faram da mai da kowa nasa, ga son zumunci da muhimmanta shi. Ga son mutane da saukin kai,

Tunda ya shigo gidan Hakimi tunanin Rahane da Babanta yake, da yanayin ban tausayin da ya baro su a ciki. Suna hira da dan’uwansa Hakimi Abdullahi Takai, amma ya lura sam hankalin dan’uwan nasa baya tare da shi.
Ya yi gyaran murya “Wani abu ya faru ne Mansur?’
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, “Wani abin tausayi nake tunani, Allah ya ja da ran Hakimi”.
Ya warware masa komai. Shi Hakimi bai san su ba. Ya ce, “Yanzu da kasa kanka cikin dogon tunani irin haka me kake ganin za ka iya yi a kansu? Talakawa fa na da yawa a kasar nan, ba su kenan ba, kuma ba za su kare ba”.
Dr. Mansur ya girgiza kai ya ce, “Allah shi ya hada jinina da wannan yarinya, zan tafi dasu Kano. Shi ya yi min aikin gadi, ita kuma yarinyar zan hadata da su Abida in dau nauyin iliminta, don da ganinta ba haka Allah ya yi nufin barinta ba!”.
Hakimi ya girgiza kai, jin yadda yake maganar (with confidence) kuma tun daga karkashin zuciyarsa “Ka tafi da yarinyar kawai, ka bar min uban a nan za sa a kula da shi. Daman kuma sarkin Dawaki ya rasu, ina neman nitsattsen mutum wanda zai jure hidimar Dawakai na babu lalaci har na baza cikiya a cikin gari.
To ka san halin talakawan namu basu yarda su rabemu saboda gudun wulakanci, na shaidi jama’ar Takai a nan”.
Dr. Takai ya ce, “Hakan ya yi, na ji dadi sosai Yaya. Bari in tura Ibrahimu ya zo dasu”.
Ya dauko waya ya kira I.M ya ce, “Daddy ina barga tare da Dawakan Mai Martaba”.
Ya ce, “Daure ka zo maza, ko da yake ba sai ka dawo ba, ka je ka zo min da yarinyar nan da mahaifinta yanzu. Ina tare da Hakimi”.
Ya rausayar da kai ya ce, “Daddy why me (me yasa sai ni)?”
Doctor ya ce, “To wa ya san gidan idan ba kai ba?’
Yana daga cikin mota yana kallon yadda jama’a ‘yan zaman makokin Iya suka cika harabar gidan, yana daga cikin motar bai fito ba yana ta shan kamshi da jan numfashi.
Can kuma ya yafito wani saurayi ya ce don Allah ya daure ya zo masa da Malam Rashidu da ‘yarsa, ya sanar dasu wadanda suka kawo yarinyarshi daga Kano ne suka aiko shi ya tafi dasu inda suke (gidan Hakimi).
Mutumin ya juya ya doshi gidan. Shi kuma I.M ya ci gaba da zama cikin motar yana kallon rusasshiyar kofar gidan. Cikin ranshi yana kissima abubuwa daban-daban, ko neman me kuma Daddy yake wa muten nan bayan taimakon da suka yi musu, me kuma zai yi musu oho!
Bai gama tunaninsa ba ya hango Malam Rashidu tafe yana rike da hannun Rahane wadda duk aka kwailewa ciwonta dake cikin bandeji jini sai zuba yake.
Ji ya yi tsigar jikinshi ya tashi, don bai son ganin fitar jini daga jikin dan Adam ko kadan. Tun kan su karaso ya tada motar, ya mika hannu ya bude musu kujerar baya suka shiga ya ja motar suka tafi ko uffan bai ce musu ba.
Tsakanin gidan Malam Rashidu da gidan Hakimin Takai akwai tazara sosai, Malam Rashidu bai taba zuwa gidan Hakimi ba sai yau.
Tun daga soron farko ya tube takalmansa ya rungume, ita kuwa Rahane a hannu ta rike abinta, tsaf take cikin nutsuwarta. Ibraheem bai tsaya dasu a ko’ina ba sai a falon da Doctor Mansoor da Hakimi suke zaune.
A nan ya tube nashi takalman suka shiga. Idon Dacta Mansoor a kan kunnen Rahane, bai ga hearing-aid din da suka makala mata ba. Ya juya ga Malam Rashidu ya ce, “Ina abin da ke makale a kunnen Rayhanatu?’
Malam Rashidu wanda ke ta kwasar gaisuwa gurin Hakimi ya juyo ga Dacta Mansoor ya ce, “Eye? Na’am?”
Dacta Mansoor ya ce, “Akwai karamar na’ura makale a kunnenta sanda muka zo, ina take?”
[12/24/2019, 17:56] Takori: Malam Rashidu bai wani fahimce shi ba sakamakon wani suna da ya ji ya ambata wai Rayhanah, sai ya dauka ba da shi yake ba.
Haushi ya bala’in kama Doctor Mansur ganin Malam Rashidu ya saki baki yana kallonshi kawai bai ba shi amsar tambayar shi ba. Shi dai Mal. Rashidu tun dazun yake ta yiwa Rahane magana bai ji ta ba shi amsa ko daya ba, sai ya dauka duk cikin halin rasuwar Iya ne. Bai kawo wani abu daban ba.
I.M ya dubi mahaifinshi ya ce, “Ina ganin sanda mutumin banzan can ya cafketa hearing-aid din ya fadi”.
Dacta Mansur ya ce, “Maza ku koma ku dubo”.
Malam Rashidu ya ce, “Ranka ya dade me zan dubo?”
Ya dubi Ibraheem ya ce, “Ka tashi ka je ku dubo na ce”.
Ibraheem ya cika fam, kiris yake jira ya fashe. Ya mike suka fito falon shi da Mal. Rashidu kamar ya shake shi don takaici. Shi bai ga dalilin da zai sa Daddy ya daura masa al’amarin talakawan nan ba, babu dangin iya babu na baba.
A guje ya fizgi motar suka koma gidan Malam Rashidu, dakin Iya inda akai gumurzun Rahane da Ado suka yi ta dubawa har Allah ya bawa Mal. Rashidu sa’ar ganin dan injin a bayan randar Iya.
“Wannan ne?” Ya tambayi I.M. Karba kawai ya yi ya fice bai ce da shi ko uffan ba, ya yi gaba ya bishi a baya. Suka koma gidan Hakimi.
Dacta Mansur ya karba ya bude ya canza batir wanda dama yana cikin aljihunsa ya matsa ya makalwa Rahane ‘yar na’urar a bayan kunnenta.
Ya ce, “RAYHANAH!” ta dago ido a hankali ta ce, “Na’am Baba Dacta”.
“Za ki bini gidana in sanyaki cikin ‘ya’yana ko za ki zauna da Babanki a nan gidan Hakimi? Daga yau Babanki ya dawo nan za a ba shi aikin yi da kyakkyawan muhalli”.
Ta juya ta dubi Babanta wanda ya zaro ido yana kallon su. Dacta Mansur ya dube shi ya ce,
“Ka amince in rike Rayhanah har illa masha-Allahu a Kano?” Ya girgiza kai ya ce,
“Aure zan yi mata!”.
Chapter 5 · 0% Book details