Sashe 12
Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
****
Kwanaki ke juyawa a hankali su koma satittika, satittika su bada watanni, watanni su bada shekara. Kamar yadda rayuwa take a kullum kenan, komai ma juyawa yake. A haifa, a mutu, a girma, a tsufa.
To hakan ce ta faru da Rayhanah, shekarun girma sun soma juyata daga kwaila zuwa matashiyar budurwa. Mai dauke da wasu ilhamomi da dama.
A yau Rahane shekarunta goma sha hudu, sun kammala karamar sakandire a Darul-Arqam suna jiran fitowar jarrabawarsu (placement) don wucewa babbar makaranta.
Shekaru biyu kenan da wucewar Ibrahim Jami’ar Chicagon Amurka, inda yake fafutukar kwalin zama cikakken (nephrologist) likitan koda. Yayin da Khalipha tuni ya kammala bautar kasa ya fara aiki da Ministry of External Affairs dake Abuja.
A yanzu idan kika ga Rayhanah zai yi wuya ki shaidata farat daya. Ta saje da ‘ya’yan Baba Dacta, fari kawai suka fita, sai fatarta ta ba da wata irin kala ta wankan tarwada mai sheki, jikinta ya fara cikowa ya nuna ilimi da hutu zallah.
Lokacin da jarabawarsu ta fito, kowacce makaranta daban ta ci. Amma Baba Dacta sai ya tattarasu su duka ya kai su ULUL-ALBAAB (Science Secondary) dake Katsina. Azizah ce ta ci gaba da Darul Arqam.
Har zuwa inda yau ke motsi, Abida bata daina cuzgunawa Rahane ba, musamman da aka mai da su nesa da gida babu Baba Dacta balle Khalipha.
Jawahir kuwa dama ta riga ta rainata kamar ita ce babbar. Haka take fadawa ‘yan ajinsu da ‘yan hostel dinsu Rayha ‘yar matsiyata ce ta zo ta makale musu, Babanta na kauye ya asirce babansu ya lika musu ita.
Sannan a gaban Raihan take fada, don ba tsoron Jawahir take ba. Uffan ko daga ido Rayhanah ba ta yi balle ta yi magana. Son Abida take bilhaqqi, saboda darajar iyayenta da Yaya Khalipha.
Khalipha wani irin mutum ne mai matukar tasiri da alheri cikin rayuwar Rayhanah, ko kadan baya son ya ganta cikin rashin walwala. Duk da dai dama ba mai walwalwar ba ce. Abubuwa iri-iri na gilmawa a zuciyar Khalipha a kan Rayhanah, yarinya ce da ta iya takun rayuwarta matuka, ta kuma iya tafiyar da mutum da halinsa.
Abubuwa da yawa kan sa a so mutum, muhimmi shine halayensa ba kyan sura ba. Rahane mai aji ce (classique). Duk da tushenta shine kauye. Ba kyakkyawa ba ce, sannan ba ta da wani abu mai fizgar hankalin namiji banda halayenta. A fuska kam babu kyan, amma a halittar jiki sai an tona cikin dubu kamin a samu goma irin Rayhanah.
Ba ta damuwa da lallai cewa sai ta sanya hearing aid in ba lokacin daukar darasi ba. Sai ta yi kwanciyarta shiru a kan gadonta, ta yi ta tunanin makomar rayuwarta.
Wato yanzu da Rahane ta kara shekaru, sai ta kara sanin ciwon kanta. Baba Dacta da Mami ba jininta bane, ba ta da kowa da za ta bugi kirji ta ce nata ne banda Babanta. Wanda ke ta fama da kansa a halin yanzu, yau ciwo gobe lafiya ba a san hakikanin abin da ke damunsa ba.
Ranar da Baba Dacta da iyalinsa suka gaji da rikonta, ina za ta je? Tsufa ya soma cimma Malam Rashidu. A zahiri babbar matsalar ciwuwwukansa kenan, ta fahimci cewa ita din abin tausayi ce. Karatun nan da Baba Dacta ya tsaya mata take yi shine kadai madogararta sai Ubangijin Talikai.
Duniya ba matabbata ba ce, haka komai na cikinta yana da lokaci. Ta fahimci akwai ranar da dole za ta bar hannun Baba Dacta da Mami tunda ba su suka haife ta ba.
Ranar da hakan ta faru ina za ta? Takai?
Ai ko gida basu da shi a Takai. Babanta babu lafiya ga tsufa, ta kowanne bangare idan ta duba sai ta ga kawai Allah ne gatanta sai yadda ya ga dama zai shirya mata rayuwa.
Wani tunani ne ya fado zuciyar Rayhanah farat daya, zuciyar ta ce AURE! Rayhanah ki yi aure ki samu ki kafa naki iyalin ki yi tabbatacciyar rayuwar iyali. Ki haifi ‘ya’yan da za su rungumi rayuwarki wata rana.
Amma abin tambayar a nan shine, wa za ta AURA? Wane ne zai iya aurenta da LALURAR ta? Wane miji ne zai juri cewa sai matarshi ta saka inji kafin ta ji magana? Wane ne zai ba ta kwarin gwiwa irin wadda Khalipha ke ba ta? Wane ne mai kirki irin Khalipha?
A cewar Abida ita MUNAFUKA ce, son Yaya Khalipha take yi, shi yasa ta damu da shi fiye da kowa a gidan. Idan ita MUNAFUKA ce don tana son mai kyautata mata, ita kuma da take tozartata a bayan idon Khaliphan yaya sunata? They are all the same kenan ko?
Kwata-kwata ma ita ba ta san wane irin so Abida ke nufi ba, don ta kan ce ya fi karfin ki.....ba ajinki bane.....me zai ci dake? Ya yi kama da mai saran kofaton Doki ne? Da sauran maganganu irin wadannan wanda inda sabo, to RAYHANA ta saba jin ire-irensu daga bakin Abida.
Abida ta fi Jawahir power, ta fita baki, ga tsiwa, ga rainin wayau. In ta raina mutum ya shiga uku. ‘Abida Hukuma’. Sunanta kenan in ji Khalipa, domin duka baya karya mata zuciya sai dai ma ya kara tunzurata ga abin da ake dukan nata a kansa. Ya kara kangarar da zuciyarta a kansa.
****
Wani abu da ya kara ta da ma Abida hankali a kan Rayhanah shine, kokarin da ta zo ta fita sakamakon wasa da tsokanar da ta sawa ranta.
Sunyi jarrabawar shiga aji biyar, Rayhanah ta kwace 3rd position na ajin wanda Abida ke kai tun farkon shigarsu Ulul-Albaab, ita kuma ta kwaso na goma.
Sun zo gida hutu ranar Asabar, a yammacin ranar ne Khalipha ya iso, sanye yake da ‘yar ciki da wando har da babbar riga na wata danyar shadda (sheraton) kalarta coffee wato ruwan kasa. Ya dora hula damanga a kan goshinsa, daman dai Khalipha ba dai iya karya karin hula ba, ita ma ruwan kasa ce.
Takalmin fatar damisa ne a kafarshi budadde wanda kudinshi ya haura naira dubu ashirin, Dattijon, daure yake da agogon polo na fata a damtsen hannunsa launin kayan jikinsa. Shigarshi reception rataye da babbar rigarsa a kafudunshi da wata karamar bakar jaka mai dauke da komatsansa masu muhimmanci.
Da sassarfa ya soma taka steps don cimma falon sama, sai suka yi karo garam! Da goshinsu shi da Rayhanah.
Goshin nasa ya kama ya ce, “Kai-kai-kai! Rayhanah goshi za ki fasa min in rasa matar aure?”
Ita ma ta kama nata goshin cikin irin muryar zolayar da ya yi mata maganar da ita ta ce,
“Kai Yaya Khalipha, kai ne fa ka kara mini”.
Ya bita da idanu luuuu! Wani chemistry ya yi aiki cikin ‘yan dakikai. Ba ta taba ganin irin wannan kallon da Yaya Khalipha ke mata yanzu a idon kowa ba, ji ta yi ba za ta iya jurewa kallon ba don haka ta yi saurin dauke idonta ta rabe ta gefensa za ta wuce, sai ji ta yi ya riko hannunta ba tare da ya juyo ba.
Mintuna uku suka dauka a hakan, ta yi saurin zame hannunta da sassarfa ta karasa sauka daga matattakalar zuwa aiken da Mami ta yi mata wajen Mal. Dahiru maigadi.
Tun daga wannan ranar Rayhanah ta samu kanta da matsananciyar kunyar Khalipha, ba ta kara bari ya ganta ba, in ta jiyo muryarsa a falo ba ta fita. Shi kuma dama tuni ya daina shiga dakinsu, tunda suka dan tasa. Balle yanzu da suka zama ‘yammata ko yau aka yi musu aure gobe za su haihu.
Ya damu kwarai da ya ganta, don haka yake yawan zaman falon amma ko keyarta babu. Mami da Dacta sun je wata seminar likitoci a kan cutar Shan Inna a kasar Algeria, daga ita sai Abida ne a gidan, don Jawahir ma da Azizah suna Jos. Har ya kammala week end dinsa ya koma Rayhanah na mishi boyo.