← Book details Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 21

Sashe 3

Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Yamma lis! Malam Rashidu ya dawo gida ya jingine kekensa a jikin danga, ya dauko kullin buhun da ya dawo da shi daga kasuwa ya shigo gida.
Dai-dai lokacin da ita ma Rahane ta dawo daga makarantar allo, ta yiwa babanta sannu da zuwa ta cika mishi buta da ruwan alwala ta kawo mishi.
Ya ce, “Sannu Rahane, Allah ya nuna min aurenki da miji na gari”.
Murmushi kawai ta yi. Ya yi alwala ya shige masallaci.
Rahane na cin tuwon ta bayan isha’i wani yaro ya shigo ya ce, “Wai ana sallama da Rahane”.
Kafin ya rufe bakinshi Iya ta yi wuf ta sunkuto tabarya ta yi kan yaron dai-dai sanda Malam Rashidu ya sawo kai, ya yi maza ya rike tabaryar tuni yaron ya yi ta kansa.
Ya ce, “Haba Iya, idan kika fasa musu kan Da me za ki ce dasu?”
Ta ce, “Gafara nan tun ban sauketa a kanka ba, gobe idaan sun kara aiko shi ya yarda ya zo”.
Ya ce, “Yi hakuri Iya, ba wani bane Ado ne, kuma da izinina ya zo su gana da Rahane”.
A firgice Rahane ta dago ta dubi mahaifinta, kamar ba ta ji dai-dai ba. Iya ta saki tabaryar ta ce, “Wane Ado kake nufi?”
Ya ce, “Ka ji Iya, Adon guda nawa ne ban da wannan makocinmu, mamallakin gidannan da muke ciki?”
Iya ta yi salati ta sanar da Ubangiji, ta ce, “Kanka daya Baban Rahane?”
Ya kama hannun Iya ya zaunar da ita ya ce, “Ki kwantar da hankalinki Iya, na riga na bawa Ado Rahane, ki bar kama jita-jitar jama’a a kan Ado domin mutumin kirki ne”.
Iya ta saki baki tana mishi kallon mamaki, ta ce, “Adon da yake shan wiwi, taba da sholisho, ‘ya’ya shida kowanne uwarsa daban. Adon dake sakin aure da zarar matar ta samu ciki? Wanda yake rayuwa kudu cikin arna shi ka dauki kamilar diya kamar Rahane ka ba shi?”
Malam Rashidu ya yi murmushi ya ce, “Su matan kin san me suke yi masa yake sakinsu? Amma Rahane fa? Bana jin ta, don ba ta da matsala. Ki yiwa mutumin da ake yada jita-jita a kansa kyakkyawan zato, don a karshe hakkinsa kawai ake dauka.
Duk wadannan abubuwan da ake fadi game da Ado a garin nan na yi bincike a kansu.
Na farko dai Ado yana shan taba amma ba abin maye ba. Na biyu ba zai tafi da Rahane kudu ba, a nan zai barta tare da matarsa ta yanzu. Na uku su matan da yake saki din laifinsu ne ba nashi ba kamar matarshi ta farko Hassu sata ta yi mishi, ita kuma.....”
Kawai Iya sai ta tashi ta barshi a wurin ta shige dakinta. Rahane ta yunkura za ta bita ya balla mata harara sannan ya nuna mata hanyar kofar gida.
Ta toshe bakinta ta soma kuka ta nufi kofar gida.
Ado na tsaye jikin kararen da suka zagaye gidan, zai yi shekaru talatin da bakwai. Baki ne wuluk wanda idanunshi suka koma ruwan kasa suna nuna alamun shaye-shaye. Bakinsa wawakeke cike taf da jajayen hakora, bai da tsayi, don ko ita ta fishi tsayi.
Ta karasa gabanshi tana kuka kawai ko uffan ba ta ce mishi ba. Ya gyara tsayuwa bakin nan a bude ya ce, “Haba Rahane? Mene ne abin kuka? Maimakon ki godewa Allah ni Ado mai shanu da mota na zo gareki na nemi aurenki ta hannun mahaifinki?
Ni masoyinki ne, ba kowacce mace nake iya cewa ina so ba, sai mai sa’a kamarki. In baki yi murna da hakan ba, to ba za ki yi kuka ba”.
Rahane ta ga cewa kuka ba zai mata ba, gara ta roke shi ya yiwa Allah ya rabu da ita ko kadan ba ta son shi. Ba tun yau ba, haka nan ko ganinshi ba ta son yi saboda kamanninsa.
Ta ce, “Don Allah don Annabi ka yi hakuri ka nemi wata, ni makaranta nake so na yi...” Ta ci gaba da kuka.
Ya ce, “In don wannan ne Rahane daina kuka, zan barki ki ci gaba da makaranta amma bayan anyi auren mu”.
Ta zaro ido ta ce, “Ni ba zan yi aure ba, yoyon fitsari yake sawa”.
Ya bushe da dariya ya ce, “Duk karyar nasara ce Rahane, iyayenmu da kakanninmu basu kai ki ba duk aka yi musu aure, me ya same su?”
Cikin kuka ta ce, “Nifa bana sonka, ko dole ne?”
Ya yi fuska sosai, sai kuma ya ce, “Ayya! Kin makaro, zamanki lafiya da matsiyacin ubanki kawai shine ki yarda ki aure ni, wanda daga ana bashi ‘yar dari biyar ya yarda ya bani aurenki. In ke baki sona, ni ina sonki, dama ba son na zo nema ba tunda baki da kunya, har ki dubi tsabar idanuna ki ce bakya sona, ba ki yi tunanin cewa ina da kamar ki a gida ba.
Aure kuwa nan da sati biyu tunda kin bullo min ta nan. Makarantar ma na fasa barin ki kiyi, shashashar wofi!”
Ya karkace ya zaro kudi a aljihunsa ya haska da cocilan ya ce, “Ungo nan, ki raba ke da kakarki”.
Ya kuma turo mata wata katuwar leda, “Amshi nan ki sabunta tufafinki kafin a kawo lefe shashashar yarinya da ba ta san abin arziki ba”.
Juyawa ta yi tana kuka sosai ta nufi cikin gidansu bata karbi kudi da ledar da yake tura mata ba.
Ya bi bayanta ya kira wata yarinya dake sai da gyada a nan gefensu, ya ba ta kayan da kudin ya ce ta kai mata. Shi kuma ya saki wani matsiyacin fito ‘fiii-fiii....’ ya yi gaba yana cewa,
“Kwanan nan zan farke santaleliyata, Rahane!”.
Rahane na shigowa gida tana kuka ta yi ido hudu da Babanta a tsakar gida yana dakon shigowarta.
Kofar dakinsa ya nuna mata, wato ta shiga. Shi kuma ya tashi ya bita. Ya zauna a kan tabarmar shi ta kaba dake shimfide a dakin ya dubi Rahane wadda ke ta kokarin hadiye kukanta karfi da yaji.
Ya ce, “Rahane!” Ta cira kai ta dube shi idanunta jawur.
Ya ce, “Ni Babanki ne, ni na haifeki, kin san kuma ba zan cuceki ba. Ko baki son auren Ado ki yi hakuri ki tusawa zuciyarki son.
Na samu kaina da talauci mai yawa, kada ki manta gidan nan ma da muke ciki na Ado ne, amma yau tsayin shekara goma sha daya tun haihuwarki Ado bai kara karbar kudin haya na ba.
Idan na ce zan gaya miki irin taimakon da Ado yake mini ba za ki taba yarda ba. Ya sha siye kayana don in samu abin da zan baku ku ci, ba don yana da bukatar su ba.
Duk halin banzan da ake kira mishi ni na yi bincike kansu ban gani ba, zancen nan da nake miki yanzu haka ya samo min aikin kula da dawakin Hakimin Takai, na daina wahalar shan rana a kasuwa, babu wani cinikin arziki. Idan kika ki auren Ado me kike so in ce masa, ko in masa na biyashi alherin da yake yi min?
Don haka ki kwantar da hankalinki, ki kwantarwa Iya. Idan har kina kaunata Rahane ki nunawa Iya kina son auren nan kin ji Rahane? Don Allah ki fitar dani kunyar Ado”.
Rahane ta daga kai. Ta yarda kawai da kudi Ado ya saye Babanta. Abin da ba ta taba tsammani ba, kwadayi daga Babanta!
Ya ce, “Shi kenan Rahane jeki. Allah ya yi miki albarka”.
Ta mike hawaye na mata ambaliya ta fita ta samu Iya na sallah mai tsayi, sai ta hau ‘yar yaloluwar katifarsu ta kwanta.
Barci ya kasa dauke Rahane, duk iya satarsa kuwa. Duk da kasancewarta karamar yarinya ‘yar shekaru goma sha daya tana da zurfin tunani da hangen nesa.
Tana son Babanta fiye da yadda shi yake sonta, ta san Babanta ba shi da kwadayi, don haka ta yi matukar mamakin yadda ya yi hakan, kamar ma tsoron Adon yake ji.
Ta tuno wai ya samo masa aikin kula da Dawakan Hakimi, kuma baya karbar kudin hayarsa. Wannan ne dalilin da yasa zai bashi ita. Abune da take da yakinin cewa, Iya ba za ta taba yarda ba, wato ayi mata aure yanzu, don haka ta dan samu salama a cikin ranta.
Har barci ya dauke ta, kayan da Ado ya biyota dasu suna nan a gefe ko daga su Iya ba ta yi ba.
Da asubahin ranar Iya ta tashe ta don ta yi sallah. Ita kuma tana hada kayan su cikin Ghana must go. Kaf ta hada kayansu bata rage komai ba.
Rahane na sallah tana jin Iya da Babanta na fafatawa. Iya na cewa, “Gidan Ado ko? To daga yau bamu kara kwana cikinsa ni da Rahane, in dai a kansa ne za ka ba shi auren yarinya mai daraja irin Rahane. Sai ka san yadda za ka yi da shi da kudinsa da kake ci.
Ba aikin gidan Hakimi ba, Allah yasa aikin Hajji ya samo maka. Sai ka ganmu, sannan ka yi mata auren”.
Iya gigicewa Malam Rashidu ya gigice, don ya san halin Iya kwarai in ta furta abu, to wallahi ba mai iya hanata.
Shi ba wani abu bane don sun tafi, bai san ya zai yi da Ado ba wanda ko mahaliccinshi baya tsoro, yadda yake tsoron Ado a kwanakin nan.
Ya yi magiyar ya yi lallashin amma Iya ta yi banza da shi. Da ya gaji ya mike jiki babu kwari ya fita, ya kasa zuwa ko’ina yana zaune a dakinsa ya saka wannan ya kwance. Bai ma san sanda Iya tasa Rahane a gaba ba suka fice. Rahane dauke da dakon kayansu zuwa tashar motar Rake suka hau bayanta suka bar Takai baki dayanta.
****
[12/24/2019, 17:56] Takori: Tunda suka hau titi Rahane kuka take tana tunanin Babanta da abin da ka je-ya-zo. Shi kenan yanzu ta rabu da Babanta? Shima ta raba shi da mahaifiyarsa dake matukar son shi? Ina za su? Yaushe zasu dawo? Ko dai ta hakura ta ce da Iya su koma ta auri Adon?
Ita kanta Iya kuka take ranta cike da tunanika masu yawa. Ko dai su koma ne? Ta fishi iko da diyarsa ne? Ko ta fishi sonta? Ta daure mata gindi kenan ta ki yin biyayya ga mahaifinta. Ita ba aure ne ba ta son a yiwa Rahane ba, mijin ne bai yi mata ba, da shekarun Rahanen.
Mummunan hatsarin ya faru ne a kwanar shiga garin Tsangaya. Inda wata motar haya peageout irin masu mugun gudun nan ta karawa Akori-kurar raken da su Rahane ke ciki ta kife.
Wasu suka zubo kan titin, wasu suka fada cikin ramuka motar ta danne su. Tsirarun motocin dake gabansu da bayansu suka tsaya don kawao agaji. Ga shi babu jami’an tsaro a kan titin baki daya.
Chapter 3 · 0% Book details