← Book details Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 21

Sashe 16

Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Khalipha na zaune ne a kan kujerar zaman mutum biyu, gwangwanin Maltina ne a hannunsa yana sha, amma saboda rungumar bazata da kannen suka yi masa gwangwanin ya fadi ya zube a cinyarsa.
Farin kaftan nashaddah (hilton) ne sol a jikinsa dinkin Mohammed, amma haka suka wanke shi da Maltinar. Hakan bai sa ya yi fushi ba, surar Azizah ya yi daga hannun Rayhanah ya yi sama da ita ya cilla ya cafe.
Ya ce, “I’m missing you.....”
Ya hadasu ita da su Abidar ya rungume gaba daya yana durkushe dai-dai tsahon su. Ba tare da ya ankara da bakuwar fuskar dake gefe ba.
Ita Rahane daki ta wuce don ta ga hankalinsa na kan kannenshi ko ta gaishe shi ma ba jinta zai yi ba, ta ce bari ta bari sai ya nutsu sai ta gaishe shin.
Khalipha bai samu kansa daga hayaniyar su Azizah ba sai da aka kira sallar magariba. Ya mike dauke da Azizah ya kawota dakin Mami, lokacin ita Mamin tana shirin yin sallah ta wuce asibiti, don yau ma aikin kwana za ta yi.
A gadonta ya dire Azizah ya ce, “Mami Dactan nan (Himu) ya bar miki mukullin daki ne?”
Ta ce, “Ka duba yana jikin kofar”.
Ya rungumeta ta baya ya daura kai bisa kafadunta ya ce, “You didn’t miss me Mami.....”
Ta ce, “Sai in yi ta rawa ina tsalle ka dawo sannan ka yarda na yi kewarka”. Dariya ya yi ya juya ya fita.
Wanka ya yi, sannan ya daura alwala, ya zuba wata shadda kaftan ruwan kasa. Khalipha Mansur baya sanya kananan kaya sam, sai shaddah, yadi ko jallabiyar Saudi ( in a gida ne). Shi yasa Mami ke kiranshi (Dattijo) a yawancin lokuta.
Daga kallo na farko da ka yiwa Khalipha za ka gane mutum ne mai faram-faram da haba-haba da jama’a (sociable) sabanin Ibrahim (anti-social in nature).
To haka a kamanni da sura, Khalipha Mami ne sak, fari sol da shi, ga tsayi ga zati. Kwayar idanunshi ba baka ba ce (brown) ce mai sheki. Da ka ganshi ka ga Mami. Kamar ta yi kaki ta tofar.
Khalipha na da kirkin da Ibrahim bai da shi, ko daga mu’amalar kauna bayyananniya dake tsakaninsa da kannensa, wadda basa samu daga Himu ko kadan. Don haka suma basu dauke shi da wasa ba, suna bala’in kaunarsa.
Ya damu dasu suma sun damu da shi sosai ba kadan ba. Daga sanda ya zo gidan Mami da Daddy sun huta da koyar da yara aikin makaranta. Ya hada digiri dinshi mai daraja ta daya daga Jami’ar (BAZE) a kan hulda da kasashen ketare, sai jiran posting din Bautar Kasa.
Yadda kamanni da halayya suka sha ban-ban tsakanin Himu da Khalipha, haka dabi’u da akidu. Khalipha dattijon ne da gaske, yaro mai halin manya. Don haka shi kansa Daddyn ma sau tari kan kira shi da (Dattijo).
Bayan sallar isha’i duk suna bisa tebir kamar yadda yake a al’adarsu. Rahane ta fito jaye da hannun Azizah, tana ta rigima duk hancinta ya toshe da mura. Rahane sai aikin share mata hanci take da hawaye duka, da guntun tishu dake hannunta.
Ya dan juya ya dube su jin Mami na fadan a daina kunna A.C da daddare tunda ba lokacin zafi ne ba. Ya dan kara juyowa sosai ya kalli yarinyar don a da ya yi zaton idonsa ne bai gani sosai ba, ya dubi Mami ya ce, “Ina kika samo ‘ya?”
Ta ce, “Allah ne ya bani”.
Kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru ya ci gaba da cin abincinsa. Don ya ga bai kamata ya ci gaba da yiwa Mamin tambayar a gaban yarinyar ba.
Rahane kujera ta hau kusa da Jawahir, don ko kadan ba ta zama daf da Abida, sakamakon kisan mummuken da take mata, ‘yan yatsunta take murjewa da kafar kujerarta, ko ta faki idon kowa ta takata da tsinin takalminta da take sawa musamman don muguntar. Iyakaci a ga tana kuka in sun koma daki, tambayar duniyar nan Jawahir za ta yi amma sai ta ce babu komai Iya take tunawa.
Sai dai kuma ta yiwa kanta maganin abun, ta daina yarda ta zauna kusa da ita. Wanda hakan bai yiwa Abida dadi ba, don dai ita nan duniya babu wanda take jin haushi irin Rayhanah.
“Zauna mana Rayhanah”. In ji Mami.
Ta zauna sosai ta fara cin abincin da Mamin ta yi serving dinta. Sakwara ce da miyar alayyahu da ganda da kifi, musamman don Khalipha Mamin ta yi girkin da kanta, don nan duniya ba abincin da Khalipha ke so irin sakwara.
Sunanshi na ainihi sunan mahaifin su Mami ne da ya Musulunta wato (Abdallah). Dacta Mansur da bai iya fadi a matsayin sunan na sirikin sa mai rasuwa shine yake cewa Khaliphan, to sai kowa ya kama. Abdallah ta bace bat, sai Khalipha.
Da kyar Rahane ta iya cin abincin nan saboda kallon ta da Khalipha ke yi jefi-jefi. Ga kukan Azizah ya dameta, jinsa take har cikin ranta. Ko kadan ba ta son kukan yarinyar.
Garin kallon nashi ne ya hango aid din dake makale bayan kunnenta. Ya zare gilashin shi a hankali yana kara kalla ya ce, “Mami bakuwar taku ba ta ji ne?”
Ta bata fuska ta ce, “Wai kai Khalipha baka gani ka yi shiru ne sai ka ce dan jarida?”
Ya maida gilashin sa yace, “Sorry Mum, I’m curious in cases like these….!”.
Ta ce, “Iftila’i na rana daya, sun samu accident ne shine sanadi”. Yace “ta yaya accident zai zamo cause to hearing impairment? Ku dai kara bincikawa, haka kawai ma ji kan dauke, mostly as a result of typhoid fever ko meningitis, ko kuma hereditary factor (gado) na amosanin kunne (otesclerosis)”. Mami tace
“to Dr. Khalipha, babu daya kanwar biyu, professionals basu ga hakan ba har sai sun gudanar da CT Scan and MRI Scan wanda abune dake neman naira miliyan biyu cash. Kuma ba’ayin shi a Nigeria.
Mahaifinta kuma ya tabbatar lafiyar ta kalau ta baro gida kamin suyi hadarin kuma bata gada daga ko’ina ba (uwa ko uba)”.
Ya mikawa Rahane hannu wadda ta sunkuyar da kai......
“Shake my hands, Rayha.....”
Murmushi ta yi amma bata bashi hannun ba.
Ya ce, “To shi kenan tunda bakya abotar dani”. Ya fada cikin launin shagwaba da langabar da kai.
Ba ta san sanda ta yi dariya ba, fararen hakoranta yiri-yiri farare sol suka bayyana. Babba dashi yana shagwaba a gaban mamarsa.
Ya ce, “Do not your problem slow down, you will achieve a lot in life!”
Ita bata ma ji mai ya ce ba saboda yadda harshensa ke harde da Turanci gangariya, sai gwani a harshen ne kadai zai iya fahimtarsa.
Wannan ya samo asali ne da haihuwar Khalipha da Himu da Mami ta yi a Ireland (Dublin). Inda Khalipha ya yi karatun shi har zuwa aji biyar na sakandire kamin su tattaro su dawo Nigeria.
A haka aka kare cin abincin. Koyarwar Yaya Khalipha daban take, ko yaro shine jaki wajen dakikanci dole ya gane koyarwar Yaya Khalipha.
Da ya zo kan littafin Rahane, ya gane Rahanen na da rauni a lissafi (Mathematics) don haka ya tabbatar ta yi a gabansa dai-dai sannan ya kyaleta.
A daren ne Mami take ba shi labarin Rahane, ya saurara da nutsuwa. Yana tsaye jikin balcony na dakinsu yana kokarin kunna Marlboro da lighter ya hango Abida ta fizge hearing aid din Rayha ta yi cilli da shi tana cewa.
“Banza ‘yar kauye, wadda bata ji said a inji, ai sai ki ji mu gani”.
Da gudu Rahane ta bishi inda ta yar ta dauka, sai ta ga ya fashe. Abida ta gudu tana kyalkyala mata dariya.
Durkushewa ta yi a nan tana kuka don ba ta san me za ta ce da Baba Dacta ba, domin ya yi mata gargadi sosai a kan takula
Chapter 16 · 0% Book details