← Book details Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 21

Sashe 19

Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta yi murmushi idonta fal da hawaye. Ya ci gaba da cewa,
“Idan Allah yasa na tashi abin da zan fara yi miki Rahane shine AURE. Bana son in kwanta dama ban ganki a dakin mijinki ba.
Sai dai kuma da na yi wani tunani sai na ga cewa kina da Uba makwafina, wato Likita Mansur. Na yarda shi mai kaunarki ne saboda Allah ba don wani bayyananne ko boyayyen dalili ba.
Don haka Rahane na horeki da yi masa biyayya kwatankwacin yadda kike mini. In ya saki ki yi, in ya hanaki ki hanu. Rayuwar dan Adam Rahane gajeriya ce, don da ta shigo saba’in shi kenan ta kare komin jin dadi kuwa, kada ki shagala da dadin duniya ki manta da Allah.
Duk rintsi ki yarda cewa mutum bai isa ya tsarawa kansa rayuwa yadda yake so ba sai yadda Ubangijinsa ya ga dama. Rahane ban bar miki gadon komai ba sai na tarbiyyar da na yi miki, wadda na tabbata za ta yi miki jagora har karshen rayuwarki.
Kada dadin duniya yasa ki shagala ki manta ko ke wace ce; talaka, diyar talaka, jikar talakawa. Talakawan ma na kauye. Don haka ki taimaki talaka a duk inda kika samu dama kema Allah zai taimaka miki kamar yadda likita Mansur ya taimakeki.
Ki zabi miji dai-dai ke, abin da nake nufi a nan shine, ki auri talaka dan’uwanki wanda zai daraja ki ya mutunta tushenki, in har zai ci dake ya shayar, ya tufatar, kada ki kai kanki inda Allah bai kai ki ba.........”
Kuka take sosai tare da katse shi da cewa, “Baba don Allah ka daina wadannan maganganun, masu kamadawasiyya, ni ba wani aure yanzu a gabana neman ilimi zan yi, shine sutturar mara galihu. Kuma Baba ni wa zai min auren idan babu kai? Baba me yasa kake yanke kauna da rayuwa a dalilin zafin ciwo? Ya Allah kada ka nuna min wannan ranar, wato ranar da zan wayi gari babu kai.....”
Ta ci gaba da wani irin kuka, ta kifa kanta jikin karfen gadon da Baban ke kwance.
Rahane dai ba ta sani ba, ba ta san abin da Khalipha ya ankara da shi ba. Ji ta yi an dafa kafadarta da wasu yatsu masu bala’in taushi. Ba sai ta juyo ba ta san Khalipha ne tunda su uku ne kawai a cikin dakin, ba ta kuma ji wani ya murda kofa ya shigo ba.
Ta dago a hankali ta dubi Khalipha idanunta kamar an gumbuda musu barkono. Shima nashin sun canja launi, ya kasa jarumtakar da zai rarrasheta bai san lokacin da hannayenshi suka yi motsi ba suka sarrafa kansu suka kai ga rungume Raihanah.
Sannan ya rufewa Malam Rashidu ido, ya ja zanin gado ya rufe shi har kansa. Dai-dai lokacin da Mami da Baba Dacta da wasu daga cikin Phyisothearapists na ward din suka shigo.
Idanun Mami a kan Khalipha dake rungume kam-kam da Rayhanah, ya kasa sakinta don kar ta fahimci abinda ya faru, ya rasa inda zai sa kansa, rikon da yayi mata mai karfi ne don kar ta juya, gaban Mami ya yi wani irin mugun faduwa ta tsaya turus! A bakin kofa.
Da gudu su Baba Dacta suka karasa suka bude rufar da Khalipha ya yi masa, gaba daya suka ce, “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!”.
Baba Dacta ya juya yana share idonsa da hankici. Da karfin gaske Rayhanah ta zame daga jikin Khalipha ta juyo da gudu ga Babanta, ta bude rufar ta ga abin da kowa ya gani.
Dora haannu ta yi a kan kirjinsa wai ta ji bugun zuciyarsa, ba ta san alamun mutuwa ba, amma ta tabbatar Babanta ya mutu. Tunda ga shi ta ji ba ya numfashi. Zuciyar shi bata bugawa ko alama.
Bayan wannan ba ta kara sanin me ke faruwa a duniyar ba, bayan gilmawar wasu taurari a idanunta. Da gudu Khalipha ya yi kanta shi da Baba Dacta, suka hanata kaiwa kasa, yayin da su Mami ke rufe Mal. Rashidun, likitocinsa na ta rubuce-rubuce cikin file din sa.

****
A gidan Hakimi aka yi jana’izar Mal. Rashidu. Ya kuwa samu jama’a na ban mamaki, kwana uku ana karbar gaisuwa, har zuwa lokacin Rahane na gadon asibiti jininta ya hau sosai, ta ki ci ta ki sha, sai ruwa ake ta kara mata leda-leda.
Ba kuka take yi ba, don ta nemi hawayen a idanunta ta rasa. Kwance kawai take ba ta umh ba ta uhm-uhm sai kallon gilmawar mutane da shige da ficen likitoci.
Wato shi kansa kukan (wuri shi ka samu), wani tashin hankalin ya fi karfin ka yi masa kuka.
Kuka rahama ne a lokacin da zuciya ke ciwo, ciwo irin wanda babu irinsa a rayuwa. Rahane ta kasa kuka sai addu’a take cikin zuciyarta ita ma Allah ya dau ranta ta bi iyayenta da Iya ta huta.
Yanzu kam ta tabbata ta zama marainiyar gaba da baya. Da dai-dai da dai-dai Allah ya yi ikonsa a kan wadanda ya bata su zame mata garkuwa a rayuwa, kuma bango abin jingina.
Shi kenan kuma ita yanzu ba ta da kowa! Idan Baba Dacta da iyalinshi suka gaji da rikonta ina za ta je?
...........“Sai dai kuma da na yi wani tunani sai na ga cewa kina da Uba makwafi na, wato Likita Mansur.....”
Ta tuno kalaman Mal. Rashidu masu kama da wasiyya. Ashe hirar karshe ce Baba, kaicona da na katseka!!!
A wannan lokacin ne ta samu hawaye suka zubo, ba tare da ta san suna kwarara ba sai ta ji an sa tissue ana share mata.
Ta juyo kadan sai ta ga Jawahir, ita ma kukan take tayata. Ta ce, “Rayha ki yi hakuri, Baba kwananshi ne ya kare, kin sani ko muma zamu iya mutuwa a kowanne lokaci. Addu’a za ki yi mishi. Rayuwa yanzu kika fara ta Rayhanah, ko ba iyaye za ka rayu idan haka Allah ya tsara maka.
Belle ke kin rayu da Baba, ya yi miki tarbiyya, ya baki ilimi dai-dai karfinsa. Sannan bai barki a hannun da za ki wulakanta ba.
Rayha ki daure ki tashi mu ci gaba da fafutukar rayuwa, darussa za su wuce ki, alhalin Allah bai nufa rayuwarki ta zo karshe ba.
Ina miki ta’aziyyah Raihanah, Allah ya ji kan Baba, ya ji kansa ya yi masa rahama, yasa Aljannah ce makomarsa, ya sanya mana dangana”.

Kwanaki bakwai da suka biyo baya, aka yi sadakar bakwan Mal. Rashidu. A cikin wadannan kwanakin, kwana biyu kacal ta yi a gida, ragowar a gadon asibiti.
Tuni Khalipha ya koma bakin aikinshi cike da alhinin RAYUWAR RAYHANAH!. Ga nakasa ga hawan jini, sannan ga maraiaci na uwa da uba da rashin dangi. Tausayi ba zai barshi ya ci gaba da ganin Rayha cikin wannan halin ba.
Ta rame kwarai, ita dama shiru-shiru jiki ba jiki ba, yanzu abin ya koma daga eh, sai a’a. Sai da Baba Dacta yasa aka soma rubuce mata Alkur’ani tana sha tsayin sati biyu.
Hatta Abida ta rage rashin mutuncin ta don ganin Rayhan, a yanzu kam wani dan Adam bai da abin da zai bata mata rai da shi, ko yankata za ta yi ba za ta daga ido ta kalleta ba balle ta san tana yi. Tunda ta jure rabuwa da Iya da Baba, to mene ne ma ba za ta iya jure shi a rayuwar duniya ba? Duniya ta fita a kanta sai fatan cikawa da imani.
Sati biyu bayan nan suka koma makaranta suka soma shirin zana jarrabawar shiga aji shida. Rahane kam ba fus, sakamako bai yi kyau ba. Sun ba ta maimaicin shekara guda (repeating), yayin da su Abida suka shige aji shida suka barta a aji biyar.
Amma maimakon Baba Dacta ya yi fada kamar yadda suka zata, sai ya ce “Rayhanatu a hakan ma kin yi kokari, Allah ya yi miki mai kyau a duniya, mai kyau a lahira a dalilin juriyar ki kan kaddarorin ki da kyawawan halayenki”.
Sati biyu Khalipha bai zo gida ba, ba don komi ba sai don baya son abin da ke zuciyarshi a kan Rayhanah ya fito sarari. Ya zo wani limit da ba zai iya boye soyayyarta ba zuciyar ba za ta iya basarwa ba.
In kuma har ya yi kokari ya boye din, to za ka iya karantar hakan cikin kwayar idanunsa cewa yana so.........kuma yana tausayin Rayhanah.
Haka nan ya samu kansa da wani sabon tunani, wato ya kai Rahane waje, masu jajayen kunnuwa su duba lalurarta. Babu cutar da ba ta da magani. Likitocinmu ba finsu kwarewa aka yi ba, kayan aiki ne bamu dasu kamar sauran kasashen da suka ci gaba.
Daga fara aikin shi zuwa yanzu yasan yanada account mai nauyi don bashi da almubazzaranci kuma babu nauyin kowa a kansa. In ma ya kakare ya tabbata Baba Dacta zai agaza masa in ya gaya masa kudurin sa.
To amma Rayhah ta balaga, shekarunta goma sha shida ya za ayi Baba Dacta ya yarda su tafi wata uwa duniya tare? Duk da neman magani ne?
Wata zuciyar ta ce, “To ka fito fili mana ka sanar da Daddy kana sonta ya aura maka ka tallafi rayuwarta da taka? In ta zama matarka shikenan babu sauran shinge. To amma anya ba ta yi kankanta ba? Ya tabbata ko Daddy giyar wake ya sha ba zai aurar da Rayha a wadannan kananun shekarun ba. Don haka furtawar ma bata da amfani.
Da ya kwashi wata daya bai zo gida ba, kewarshi ta damu al’ummar gidan, kada Azizh ta ji labari. Duk sanda Mami ta kira wayarshi sai ta jita a kashe, haka in ta yi amfani da social network baya responding.
Zuciyar UWA! Ba irin tunanin da ba ta yi ba. A yau dai ta kasa daurewa ta samu Daddy da zancen.
Ya ce, “Lafiya ita ke buya Asma’u, amma ba rashinta ba”.
Duk da haka ta kasa sukuni, a ranar Alhamis Daddy ya daga kasar Ireland domin halartar taron “Old Students Alumni of Trinity University”. Kwananshi daya da tafiya ta dauki hanyar Abuja ita kadai a motarta, tana tafe tana zancen zuci.
Chapter 19 · 0% Book details