← Book details Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 21

Sashe 17

Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

da shi, ita kuma ba za ta iya ce da shi ga laifin Abida ba.
Da hanzari ya ajiye abin da ke hannunsa ya fito zuwa harabar gidan, tsugunawa ya yi gaban Rahane ya karba yana gyarawa. Ido ta dago ta dube shi sai ta hau share hawaye da hanzari, don bata so ya ganta tana kukan ba. Da ya gyara sai ya mayar mata ya ce, “Tafi gida”.
Tun daga ranar Khalipha ya sa ido a kan mu’amalar Rayha da Abida, Jawahir da kuma Azizah. Ya gane Abida bata son Rayhanah sam-sam, komi ta yi sai ta kushe ta gwale, ta wulakantata. Ya ci gaba da bibiyarsu da hankali, nan ya gane kaunar da Jawahir ke wa Rahane, suna son junansu sosai, da kaunar da Rahane kewa Azizah wadda ta sayo mata kauna a zuciyar Mami.
Tara Abida yake yi, bai yi kuma niyyar sanarwa Daddy ba shi zai yi maganin abin. Yau suna zaune shi da Malam Dahiru maigadinsu a kan benci suna hira, su kuma yaran suna can wajen shukokin grass-carpet suna wasanninsu ya hango Abida ta janyo mesar da ake bai wa shukoki ruwa ta saki ruwan a kan Rayhanah, tun daga kanta har kafafunta ta jikata sharkaf, amma ko uffan yarinyar nan bata ce ba. Ta ja mesar ta gudu da ta hango Jawahir na tahowa.
Tun daga ranar ya lura Rayhanah ta daina shiga cikinsu. Ba ma ya ganinta kwata-kwata. Daga baya ya lura kullum tana daki ne kwance a gadonta lullube da bargo. Sai ta ji Mami ko Baba Dacta a falo sannan take fitowa, amma ko abinci in basa nan ba ta ci.
Ganin haka shi kuma duk sanda zai ci abinci sai ya tura Azizah ta kirata, ya cika mata filet ya ce sai ta cinye a gabansa. Ya soma janta a jiki ta hanyar labarai da son jin damuwarta, da kuma ba ta misalan rayuwa kala-kala a kan kaddarar da Ubangiji ya yi nufi ga bayinsa, sai su karbeta su kasance masu godiya a gare shi, don in ya baka wannan, sai ya hana maka wancan, ya ga cewa za ka gode masa ne ko za ka butulce a kan wannan jarrabawar kankanuwa da ya yi maka?
Kwarai Rahane ke jin dadin hira da Yaya Khalipha, halinsa ba daya ne da na dan’uwansa ba, komai nasu opposite. Ita Rahane yadda Yaya Khalipha ya damu da lalurarta ita ba ta damu kanta haka ba. Ita fa ko babu injin nan za ta iya zamanta lafiya, tunda tana da lafiya falil-lahil hamdu.
Rannan da yamma kuma Jawahir tana falo, Abida ta ja Azizah daki ta cire mata pampers. Ta yi kashi fal! Rahane na kwance a gadonta cikin bargo kanta ke ciwo sosai ga zazzabi-zazzabi na neman kama ta. Ba ta son wannan na’ura mai mayar da daki kamar firinji. Duk da Mami ta ce a daina kunnawa sai lokacin zafi su kam basa iyawa sai sun kunna in za su kwanta in ba haka ba ba za su iya barci ba.
Abida ta kunso kashin pampers ta dawo dakin kamar abin arziki ta ce, “RAYHA!’
Ta dan janye bargon ta fiddo fuskarta idanunta duk sun kankance sunyi jawur alamun ciwon kai mai zafi. Ba ta yi wata-wata ba ta kifa mata kashin a fuska.
Dai-dai lokacin da Jawahir ta shigo. Cikin karaji ta ce, “Abidaaaa!”
Wannan ya janyo hankalin Himu da Khalipha wadanda ke zaune a falo suka yo dakin aguje saboda yadda ta yi maganar da karfi da kururuwa, tsammani suka yi Abidar mutuwa ta yi.
Ta ce, “Ku duba ku gani, kashin Azizah ta kifa mata a fuska”.
Ai kuwa Khalipa ya kama Abida da duka don dama bai iya fushi ba, kuma tarata yake yau ta kai shi bango.
Shi kuwa Ibraheem juyawa ya yi ya fita ya ma bar gidan zuciyarsa na wani irin harbawa, tsigar jikinsa na tashi, don baya son ya yi kowanne action a kan Rayhanah balle har ya fassara reaction din sa a kanta.
Chapter 17 · 0% Book details