← Book details Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 21

Sashe 11

Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Taron, wanda aka gudanar a dakin taron (Musa Abdullahi Auditorium) dake cikin sabuwar Jami’ar Bayero, ya samu halartar kusoshin ilimi na Najeriya da shuwagabanni, malamai da sarakuna. Farfesoshi da Dactoci, har da mataimakin shugaban kasa.
A jawabin mai girma V.C Proffesor Attahiru Jega, ya ce yau shekaru ashirin kenan da jami’ar ta ba da shaidar MBBS mai daraja ta daya, daga nan ba ta kara samu ba sai yau a kan Dr. Ibraheem Mansur Takai. Don haka ‘chevening scholarship’ dake tallafawa hazikan ‘graduates’ na kasashe masu tasowa dake karkashin majalisar Turai ta bashi zabin duk kasar da yake so ya yi specializing a duk fannin da ya zaba. V.Cn ya kare bayanin sa da cewa “Dr. Ibraheem congratulations!”
Ya fada tare da mika masa hannu suka gaisa, sannan ya mika masa kwalinsa, ya karkata masa hularsa. Sannan ya dafa kafadunsa yana girgizawa.
Sai da Nabila ta san yadda ta yi ta kutsa cikin jama’a tana daukar I.M da V.C hoto duk motsin da sukayi, daga karsh Baba Dacta ya rungumo suka jero tare suna sakkowa daga kan steps din zuwa wajen Mami, wadda ke tsaye harde da hannuwa a kirji, fuskarta ta kasa rabo da kayataccen murmushin dake tattausan bakinta. Itama ta rungume shi Nabilan na ta daukar su hoto.

Kwana biyu da taron Baba Dacta ya shiryawa I.M walima a nan reception din gidan. ‘yan’uwa ne na jiki, abokan arziki da abokan aiki na Baba Dacta da Mami, dangin Mami daga Jos, abokan Ibraheem da na Nabila, hatta Hakimin Takai ya zo da iyalansa.
Don haka Dacta ya kama musu daki a Tahir. Don duk girman gidan nan cika ya yi da ‘yan’uwa da abokan arziki.
Addu’o’i aka fara yi, sannan daya daga cikin malaman Ibraheem (Consultant Dr. Bello Sajoh) ya ba da tarihin Ya Himu, hazakarsa da determinations dinsa kan karatunsa.
Sannan ya ja hankalin iyaye kan su karfafi ‘ya’yansu da karatu a fannin kiwon lafiya don taimakon kasarmu da al’ummar mu. Ba wai bamu da masu hazaka bane a Arewa kamar ‘ya’yan Kudu da sauran kasashen da suka ci gaba, a’a, determination wato (kuduri) yaran Kudu dana sauran kasashen da suka cigaba suka fi namu da jajircewa kan goal attainment, sai kuma ZUCIYA.
Ya ce,
“har yanzu Najeriya tana sahun underdeveloped societis, bai yarda da cewa tana shaun developing ba, saboda rashin zuciya da lalaci irin namu, muyi ta diban miliyoyinmu muna kai wa Turawa don suyi mana magani muna kara bunkasa su alhalin ba a fimu da komai ba.
Maimakon masu kudinmu da shuwagabanninmu su yi amfani da miliyoyin wajen gyara asibitocinmu da kawo magunguna masu inganci da kayan aiki ko da a matsayin sadakatul jariya ne. A’a, sai suke kaiwa Turawa suna karawa mai karfi-karfi, kasarmu kuwa da marasa hali ko oho!
Ka je asibitin gwamnati irin su Murtala da asibitocin koyarwar mu ka ga yadda ake wulakanta talaka da masu haihuwa. Lafiya ita ce gaba da komai, karatun kiwon lafiya bai yi tsamarin da al’umma ke duban shi da shi ba, nutsuwa kawai yake bukata da jajircewa.
Masu hazakarmu sun tattare a (Social Science) maimakon (Physical Science) da Arewa ke bukata, ba don rashin kwakwalwa ba sai tsoro da muka sawa zuciyarmu a kan ilimin. Don haka ne ‘yan Kudu suka fi mu ci gaba a fannin, suka fi yawa a kasashen ketare domin neman ilimin Kimiyya.
Dr. Bello ya ci gaba da cewa,
“a yanzu sabuwar gwamnatin da muke ciki ta yi alkawura na daukar nauyin daliban Arewa a fannin kiwon lafiya, amma fa sai da hadin kan iyaye. Dutyn sune su ba wa ‘ya’yansu maza da mata kwarin gwiwa a kan ilimin kimiyya, musamman mata a kan (Gynaecology) wanda yake halastacce a addininmu.
Ya ba da misali da Ya Himu, kwata-kwata shekarunsa ashirin da bakwai amma saboda samun kulawa da iyaye tsayayyu a kan al’amarinshi da kwarin gwiwar da ya sanyawa ransa da zuciya yau ga shi a cikakken likita (General Practioner) da zai iya duba kowacce irin cuta ta yara ko ta manya ya yi (prescribing) ya fadi maganinta, da yadda za ayi a kauce mata da kuma yadda za a shawo kanta in ta yi qamari. Me ya fi wannan amfani ga al’umma? Me ya fi wannan zama abin alfahari a zuciyar iyaye?”
Jama’ar sun ji dadin tunasarwar Dr. Bello, iyaye da yawa sun dauki shawararsa. Ba irin cimar da ba a ci ba.
Ibraheem ya samu kyaututtuka na alfarma. Hakimi mukullin dalleliyar mota ne. Su su Rahane yawo kawai suke cikin mutane ita ba ta ma san taron me ake yi ba sai da Jawahir ta gaya mata.
Yaya Khalipha ya tafi jihar Sokoto inda aka tura shi bautar kasa. Mami na zaune a falo tana waya da Khalipha, Himu ya fito cikin shiri da alama fita zai yi.
Ta yi mishi alamar ya dakata ta karasa magana da Khalipha. Ta gama ta ajiye sannan ta dube shi ta ce, “Ya za ka fita ba ka karya ba?’
Ya yi dan tsaki ya ce, “Ban jin cin abincin yanzu, heart burn ke damuna”.
Ta mike ta isa ga table ta hada mishi shayi mai kauri tana firfitawa ta ce, “Atleast ka sha wannan, rashin cin abincinka ya fara damuna Ibrahim.
Wai me ke damun ka ne? Na lura tunda aka yi maganar auren nan duk ka bi ka rasa kuzari. Nabilan ce ba ka so ko ya ya ne? Idan ka san ba sonta kake ba don me za ka bata mata lokaci har zuwa yanzu kana yi mata yawo da hankali?
Yarinyar nan ta ki kowa sai kai, iyakar soyayya ta gaskiya ta nuna maka, ba ta cancanci rana daya ka juya mata baya ba”.
Ta dauko GESTID tana girgizawa, shi kuma ya soma kurbar tean a tsaye. Sai da ya shanye ta zuba gestid din a cokali ta ba shi da hannun ta cikin bakin sa. Fuskarsa da zuciyarsa cike da jin dadin kauna da kulawar da uwarsu ke musu, kamar wasu kananan yara.
Ita kwata-kwata bata ganin girman su, kullum yadda take treating su Jawahid haka take treating dinsu, wani zubin har sai Dr. Mansur ya ankarar da ita. Ya ce, “Mami nifa ba yanzu zan yi aure ba, don haka ki ajiye zancen Nabila aside. In ta samu miji ku rufawa kanku asiri ku aurar da ita. Ba zan taba auren macen da ta fara cewa tana sona ba!”.
Baki Mami ta saki, ta ce, “Mai sonka kuwa ai shine masoyinka. Bakin da ya furta SO, baya dawowa ya furta kiyayya”.
Murmushi ya yi, ya sumbaci goshinta ya yi gaba.
“Sai na dawo Mami ba nisa zan yi ba”.
Ta ce, “Nima rainin hankalin za ka yi mini Himu?”
Birki ya ja, sannan ya juyo. Cikin damuwa ya ce, “Mami ya ya za ayi na raina miki hankali? Cewa nake ra’ayin da ke zuciyata kika tambaye ni? Na gaya miki gaskiyar abin da zuciyata ta yarda da shi. Bayan wannan ma ba zan yi auren zumunci ba Mami”.
Ta ce, “Hujjah?”
Ya ce, (cikin bude ido kadan) “Hujjoji barkatai”.
“Kamar wanne da wanne?”
Komawa ya yi cikin kujera ya zauna, ita ma Mamin haka, dab da shi ta zauna.
“Idan ma’auratan suka samu kuskuren fahimtar juna, kowanne zai bi bayan bangarensa ne. Sai ki ga su ma’auratan har sun manta sun shirya a tsakanin su amma abin zai yi ta zama a zuciyar iyayen nasu, a dinga kallon juna da shi. Daga nan zumunci zai baci, kin ga garin hada zumunci an lalata shi.
Irin zumuncin da na taso na gani tsakanin Mai martaba Hakimi da Daddy ban taba ganin irin sa ba. Bazan yardain zamo sanadin da zai yi tuntube ba ko kankani. Ina son yadda suka faro shi suna yin sada gaskiya su cigaba da yin sa har karshen rayuwar sub a tareda mun samar da tangarda a cikin sa ba.
Idan na auri Nabila ko laifi tayi min bazan iya hukuntata ba, zan yi ta yi mata uzuri da Baba Hakimi, haka shima ko wacce irin cuta zan yi mata bazai tada kai ba balle ya kalla, nikuma yadda bana son a danne hakkina haka bana danne hakkin kowa. Don haka auren zumunta baya cikin tsarina, don a ganina auren mugunta ne kawai.”.
Murmushi ta yi ta ce, “Hujjarka is invalid. Kai dai kawai ka ce baka ra’ayin Nabila, don in kana sonta har zuciyarka ba za ka tsaya yin la’akari da wadannan kananan abubuwan ba”.
Ya ce, “To Mami maganin kada a ji, kada a yi”.
Ya mike ya fice ta bishi da idanuwa. Sannan ita ma ta mike ta soma shirin tafiya ofis.
Chapter 11 · 0% Book details