← Book details Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 21

Sashe 18

Rayuwar Rayhana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana referring kowane motion dinsa a kanta da KARYA....... Bayan kuma sau tari tsoron kar zuciyarsa ta ce ya yi KARYAR yake kidima shi ya yi mata KARYAR. Ya damu da RAYHANAH fiye da kowa da komi a duniya, amma yana KARYATAWA da kalubalantar kansa a kullum. Wani gini ne ke tsiro na TAUSAYI da KAUNA tun ranad da suka baro Takai.
[12/24/2019, 17:56] Takori: Khalipha ya ci gaba da kallon labaran CNN da Mu’azzam Kanti ke kwararowa (Alkawari Bayan Rai). Lokaci-lokaci ya kan duba agogon (RADO) baki dake daure a hannunsa, sai kuma ya dan dubi kofar dakin nasu. Amma ko keyar Rayhana babu har karfe goma. Tuni Azizah ta yi barci a dakin Mami. Yana jin sanda Jawahir ta yi musu light off (wato ta kashe wutar dakin).
Sai ya mike a hankali jikinshi babu kwari ya nufi dakinsa ya sunce ya daura tawul ya sakarwa kanshi shower, amma zuciyarshi ta ki yin sanyi. A azabce take matuka da zazzafar soyayya, wadda shi kansa bai san ya zai yi ya amayar da ita ba ga kankanuwar yarinya kamar Raihanah mai shekaru goma sha biyar wadda kuma ke matukar ganin girmansa.
Ya daura Pjs ya kwanta a sofa, ya janyo kwalin Marlboro ya soma tada karamin hadari da hayakinta, duk don ya samu sassauci a zuciyarsa, ya danne wannan al’amari da ya kutso cikin rayuwarsa ba da tsammaninsa ba, zuwa sanda Rahane za ta kara girma ta mallaki cikakken hankali yadda za ta fahimci al’amarin, at least ko sakandire ne ta gama. Ya san Daddy ba zai hana shi ba idan ya ce yana so. To balle kuma Mami da ta mai da Rayhan diyar cikinta.
Barci a wannan daren rabi-da-rabi Khalipha ya yi shi. Karshe shida dai-dai ya ji Daddy na buga mishi kofa, abinda bai taba yi ba.
Idanunshi jajir kuma mitsi-mitsi cikin mugun barci mai dadi ya bude kofar. Kafin ya gaida Daddyn ya ce, “In ce ko ka yi sallah Khalipha
Ya amsa “Eh, Daddy na yi”.
To ka canzo kayan jikinka mu tafi Takai”.
Tuni ya nemi barcin ya rasa, ya ce, “Lafiya Daddy?”
Ya ce, “Shiryo dai mu yi sauri kamin yaran nan su farka”.
Saboda zullumi Khalipha a bai-bai yasa rigarsa, ya suro hula da takalmi ya bi bayan Daddy.
Sai da suka hau titi dodar, sannan ne yake gaya mishi Hakimi ne ya kirashi a waya ya ce da shi Malam Rashidu ya fadi a bayi (toilet) rabin jikinshi ya mutu (Pralysed) jiya da daddare.
Khalipha ya ce, “Subhanallah! To ai Daddy da mun taho da Rayha”.
Ya ce, “Zamu taho dashi asibiti ne ai, idan na ga yanayin jikin nasa. Ba zan so ta ganshi in a bad condition ba, ka san damuwarta da mahaifinta”.
Khalipha dai shiru ya yi, amma kar ki so ki tona zuciyarshi da damuwa ta yiwa yawa. Har ya fi Daddy damuwa. Har suka shigo garin Takai bai kara yin magana ba.
Da hantsi suka isa Takai. A kofar gidan Hakimi suka yi parking. A dakin Hajiya Karima suka karya kumallo, kafin su shiga wajen da aka warewa Mal. Rashidu.
Yana kwance bai san wanda yake kanshi ba, har Baba Dacta ya gama dube-dube da aune-aunenshi a kansa bai san ana yi ba. Bakinsa a karkace rabin fuskarshi ya mutu. Duk wani taimakon gaggawa da ake yiwa masu lalurar Dr. Mansur ya ba shi, sannan ya gayawa Hakimi za su tafi da shi asibiti, kwararru a fanninsa su duba shi.
La’asar lis suna cikin asibitin koyarwa na Kano. A take aka ba shi gado a (aminity) aka soma bincikarsa tare da gwaje-gwaje da dora shi a kan tretment din da ya dace da shi a (physiothearapy department).
Sai magariba suka koma gida a gajiye likis. Suka yi sallah suka ci abinci suka samu nutsuwa. Bayan sunyi sallar isha’i suka koma asibitin, zuwa lokacin ya bude idonsa amma baya magana, sai dai duk abin da suke cewa yana jinsu. Yana ta motsi da bakin yana son gaya musu wani abin amma ya kasa.
Albarkacin Baba Dacta duka likitocin dake kula da shi basu dauke shi da wasa ba, kula suke da shi sosai ba dare ba rana. Khalipha shi ya kwana da shi.
Washe gari da safe Dacta ya zo da Mami don ita kwanan asibitin ta yi, suka duba jikin nasa yana samun sauki ba laifi ba kamar jiya ba.
Har ya yiwa Khalipha murmushi, Khalipha ya matsa gare shi shima ya yi murmushin.
Ya ce, “Sannu Baba, Allah zai baka lafiya ka ji?”
Ga mamakinsa sai ya ga ya yi masa alamar ya daga kai. Khalipha ya ce, “Zan je in yi wanka in dawo Baba”.
Sai ya rike hannunsa da hannunsa mai lafiyar ya ki saki, yana ta kakarin magana. Da Khalipha ya nutsu ya fahimci cewa yake “Ka zo da RAHANE”.
Ya ce, “To Baba Rayhanah za ta zo”.
Da yake Asabar ce duk suna gida, Khalipha ya dube su daya bayan daya, Jawahir ce kewa Azizah kitso, Rahane na shafa mata lallen Rani a kan yatsunta. Abida dama ba ta dawo ba.
Basu ankara da shigowar shi ba saboda karar t.v don haka shima ya wuce dakinsa a hankali, babu wacce ta ankara da shigowarsa.
Sai da ya yi wanka ya shirya ya fito dining nan suka san ma yana cikin gidan. Kowacce gaishe shi take don tunda suka dan kara tasawa suka daina damukarsa sai dai gaisuwa ta ladabi.
Ya dubi Rayhanah kadan ya ce, “Ki shirya asibiti zamu yanzu Rayhanah”.
A hankali ta juyo ta dube shi tana son ta tambaye shi waye ba lafiya? Amma ta kasa sakamakon kwayar idanunshi dake sanya mata wani al’amari da ke taba zuciyarta da ilahirin gangar jikinta.
Tsam ta mike ta dauko hijabi irin dogon nan mai hannuwa ta saka ba tare da ta tsaya ko duba madubi ba, da takalmi flat. Ta bi bayan Yaya Khalipha wanda har ya tada mota.
Karo na farko a rayuwarta da ta shiga motar Khalipha. Wani ni’imtaccen sanyin A.C wanda ya cakude da kamshin (car fresh) din citrus da turaren da Khalipha ya yi amfani Azzaro Chrome (Legend) shi ya soma bakuntarta a sanda ta shiga gefen Khalipha ta zauna.
Ya dan juya kadan ya dube ta suka hada ido, inda ya gano alamomin tambaya fal cikin idanunta amma ta kasa furtawa. Ya fi minti uku bai yi magana ba kuma bai ja motar ba.
Rahane ta gaza hakuri ta ce, “Don Allah Yaya Khalifa waye ba lafiya?”
Ya kunna motar a hankali ya fara yin reverse, sannan ya ce da ita, “Ki yi hakuri Rayhanah, Baba Rashidu ne ba lafiya amma mun taho da shi nan asibiti har ya fara samun sauki”.
Kwalla fal idonta ta ce, “Tun yaushe ne?”
Khalipha ya ce, “Tun jiya, ai sammakon da muka yi ni da Daddy Takai muka tafi”.
Ta jinjina kai sai ga hawaye ya balle a ka kundukukinta. Ta yi saurin juyawa tana kallon titi kada Yaya Khalipha ya gani.
Yana gaba tana binshi a baya har dakin aminity na male-ward din inda Malam Rashidu ke kwance.
Da sauri Rahane ta karasa gaban Baban ta kama hannunsa, wannan lokacin kuka ne sosai ya kwace mata da ta fahimci halin da Babanta ke ciki.
Khalipha (cikin bugun zuciya) da hawayen da Raiha ke fitarwa ya ce,
“To kuwa zan maida ke gida Rayha, ciwo ba mutuwa bane, ke da za ki ba shi karfin gwiwa da kalamai masu dadi sai ki yi masa kuka?”
Ta soma share hawayen da gefen hijabinta. Dai-dai lokacin da Khalipha ya matso kusa da Baban, don ganin kamar ya bude ido.
Ya ce, “Baba ga Rayhanah ta zo, Baba Allah ya baka lafiya”.
Sai ya mika mata hannunshi mai lafiyar ta kama, jikinta har rawa yake yi. Kamar wanda ya warke a take ya bude ido garau yana kallon diyar tasa, tausayinta yake ji sosai, don ya san ba ta da kowa a duniya da za ta bugi kirji ta ce nata ne sai shi sai Ubangijin da ya halicceta.
Yana ji a jikinsa wannan rashin lafiyar tasa ba ta tashi ba ce. Bayin Allah na gari (Saliheen) Allah kan nuna musu karshen rayuwarsu. Duk da haka ya daure ya tattara kuzarin da Allah ya ba shi a lokacin muryarshi da sanyi kwarai ya ce,

“Rahanen-Iya diyar Yalwati-na!!!”.
Chapter 18 · 0% Book details