← Book details Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 67

Sashe 9

Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin ba wani taimako daga kowa yasa Sa'adah zame Laylan daga jikinta da sauri jikinta na rawa ta debo ruwan zafin da laylan tashigo dasu tun farko tazo tazubawa laylan da yawa a fuskarta tana Kiran sunanta cikin fatar tadawo hayyacinta....

Kamar bazata dawo hayyacin nataba sai gashi ta bude idanuwanta ta zubawa fuskar anty Sa'adah din dake kanta cikin firgici tana jiran farkawarta....

Batareda ta motsaba ta maida idanuwanta Kan hancin anty Sa'adah din Dake digar da jini alamar habo
Duk da halin datake ciki sai data Kai hannu Kan hancin Sa'adah din da qaramin sauti tace'
Jini hancinki anty Sa'adah.

Da sauri Sa'adahn ta saketa tana tare hancin cikin mamaki da Dan sauran firgicin data Shiga na halinda Laylan da abban suke ta miqe tana juyawa da sauri ta fice zuwa waje hannunta toshe da hancin ta nufa bakin fanfo ta kunna tana gogewa da hannunta tana wanke hannun a fanfo.

A sulale Laylah ta fito ta nufi dakinta ta shige ta zube qasa Kan dadduma tareda cusa kanta cikin qafafunta kanta na tsananin sarawa kamar zai juye
Gashi Babu Wanda zata tambaya Ya Abbanta sai lokacinda Abdullahi yadawo,
Shin Abbanta Yana Raye kuwa
Kokuwa shima ya rasu ya barta a duniyar da Babu komai acikinta sai son zuciya da zabi.

Ta bangaren Sa'adah tana Gama wankewa ciki tayo ta nufi dakin Momy data bar palon Takoma dakinta ta zauna bakin gado tareda dafe kanta dake tsananin Mata ciwo itama
Ta qaraso gurin momyn ta zauna gefenta tareda riqo dayan hannun momyn da idanuwanta sukai jajir itama idanuwanta suka ciko da hawayen tausayin momyn cikin tsananin kulawa da sanyin jiki tace"
Inshallah wata Rana Zaki komai ya wanke daga zuciyarki
Kici gaba da daurewa ahakan yafi kibar zuciyarki ta ri jayeki
karki Bari shedan yafi qarfinki,
Wata Rana zakiji zuciyarki ta saki gabaki daya
Amma Dan Allah Momy ki sassauta muku ku dukan sbd zuwa yanzu Babu Wanda baya cikin mawuyacin hali acikinku,
Abba lafiyarsa da rayuwarsa gabaki daya acikin jarabawa suke
Ta yanda ma ko yaso neman yafiyarki bazai iyaba Dan Allah Momy ki saki komai kibar rayuwarki tasamu salama da nutsuwarda kowace irin zuciya ke samu.

Na Miki alqawarin idan ganin Laylah ne damuwar daga ranar da nayi aure zanbar gidan Nan Zan tafi da ita bazata sake dawowa ba har sai ranarda zuciyarki ta samu aminci da ita wannan shine alqawarina agareki umma sbd bakisan iya qaddarar da Allah ya rubuto a tsakaninki da itaba Dan kuwa dagani har ita bakisan waye Zai zana gatankiba alokacinda tsufa ko ciwo ya riskeki,
Inaji ajikina Laylah zata zame Miki farin ciki abin alfahari Inshallah
Amma saikin bar zuciyarki ta amsa qaddarar da Allah yariga ya rubuto a tsakaninku wadda ta Dade da wucewa ki yadda cewa Laylah 'ya ce daga wata uwar.

Ko motsawa momyn batayiba Dan kuwa sosai takejin nauyi Mai qarfi a zuciyarta,
Ita kanta tanason yayewa zuciyarta uqubar datake ciki Dan kuwa tsawon shekarun itama batayisu cikin farin cikiba ko kadan saidai Haka Allah ya halicceta da tata zuciyar riqon Mai qarfi.

Har tsakiyar dare Babu wani bayani daga asibiti sai zaman jiran tsammani da kowa keyi a dakinsa batareda kowannensu ya rintsa ba.

Laylah daqyar taga safiyar ta waye Mata tayi sallah hakanan ta fito tafara ayyukan Dake kanta batareda jikinta ya bayyanarda halinda zuciyarta take ciki ba,
Sa'adah da itama Bata cikin walwalar sbd tunanin Halinda Laylan take ciki da Abban danma takira abdullahi taji jikin Abban Wanda har lokacin Ba wani labari Mai Dadi
Tafito Dan Taya Laylah aiki sbd rage Mata damuwa duk da tasan Bata nunawa.

Ganin irin yanayin laylan na sanyi data qara yasata dauko wayarta takira Mata Abdullahi ta miqa Mata wayar cikin qarfin hali ta tambaya jikin Abban
Abdullahi ya tabbatar Mata da Abban Yana Raye saidai kam Yana kwance Babu wani Sauki saidai daga ubangiji.

Adduar samun lafiya Tai Masa ta miqawa Sa'adah wayar tana cewa"
Nagode anty Sa'adah.

Dafa kanta Sa'adah tayi tana cewa"
Kiyi kokari ki fitarda damuwarki zakiji sassauci cikin zuciyarki.

Wani irin murmushi kawai tayi tana cigaba da juye ruwan Lipton din data dafa acikin flask.

Itada anty Sa'adah yau sukai aikin abincin Rana kafin Anty Sa'adah din tasata tayi wanka tace ta shiryo suje asibitin.

Cikin sanyi ta shirya suka nufa asibiti a napep
Koda suka Isa Abdullahi bayanan yaje gida wanka da cin abinci ya Dan huta kafin yadawo Dan Haka su suka wuni a asibitin
Takasa dauke ido daga kan mahaifinta da cikin lokaci qanqani ciwo ya qarasa zabgesa Dan kuwa fuskarsa tuni Tayi wani irin rama Mai tsanani raunar da zuciyar duk wani Mai qaunarsa.

Anty Sa'adah ma zuru tayi ta zuba Masa nata idanuwan tanajin tausayin kanta da Babu shaquwa tsakaninta da mahaifinta Wanda Momy da 'yan uwanta ke nesantata dashi sbd cusa Mata Jin zafinsa akan abinda yayiwa momyn saidai har ga Allah tasan akwai tsananin tausayi da qaunar mahaifinta cikin ranta,tana nesanta kanta dashi sbd karta qarawa momyn takaicinsu Abban da Laylah
Saidai Bata iya nesanta kanta da Laylah Dan lura da hakan shine abinda Abban yafi so da kauna
Ta zabi tasakasa farin ciki daga nesa ta hanyar bawa Laylah dukkanin kulawarta da qaunarta.
#MAMUH#
Kuyi following Dina Dan samun posting akan lokaci dama sauran novels Dina complete
Mamuhgee @Arewabooks
*_Rabo sai Mai shi...Bata taba saka ran shigowarsa ko zama jigo a rayuwarta ba sbd kallon datake Masa amatsayin Uba,Abokin mahaifinta,Amininsa Kuma Mariqi.!_*
*_Soyayyace tashiga tsakaninsu Mai girma da qarfi batareda sun ankare da hakanba bayan dukkaninsu sun haramtawa kansu hakan,Shin ta yaya zata kalla mijin yayarta,Yar uwarta wadda ta riqeta tamkar yanda uwa me riqon 'da amatsayin nata mijin TAYAYA ZATA KALLA AMININ MAHAIFINTA A MATSAYIN MIJINTA?_*
*_Qaddararsuce wannan kokuwa itace rabonsa tun farko?_*
Follow me @ArewaBooks
Mamuhgee For my latest updates
*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_
*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_
*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_
*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_
*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya
*_09032345899_*
*KATIN MTN*
09166221261
*_Mamuhgee 8_*
_ArewaBooks@Mamuhgee_
Yini sukai a asibitin sai dare suka koma gida suka Bar Abdullahi
Koda suka Isa gida Momy na kwance a daki zazzabi Mai qarfi ya kwantar da ita Dan Haka cikin daren Laylah tahau wani aikin ta Dora Mata ruwan tea da maganinta na Hausa data fiye Sha takawo Mata lokacin Sa'adah na zaune gefen gadon tana Mata sannu cikin kulawa ita ta karba maganin da tea din Laylah ta juya ta fice taje ta rufe gida tadawo tayi sallar ishai da basuyiba acan asibiti tayi dakinta ta kwanta tareda rufe idanuwanta kawai.

Washe gari tunda safe tayi dukkanin ayyukanta tayi wanka ta zauna ko anty Sa'adah zatace suje asibiti sai gashi batace din ba
Momy ce kawai ta shirya ta fice zuwa asibitin Dan ji daga likitoci dake jiranta.

Lokacinda Dr Abbakar yagama yimata bayanin Abban yariga yashiga coma sai ranarda Allah yayi ikon tashinsa shiru tayi tareda qurawa Abban idanuwanta dasukai jajir
gabaki daya kamanninsa sun sauya
Oxygen ne a bakinsa Wanda yake Dan taimakawa rayuwarsa datake hannun ubangiji Dan Jan numfashin duniya,
Fuskarsa tayi haske fayau kamar Wanda babu digon jini a jikinsa
Ta sauke Kai tana Jin inama zata iya dawo da baya gaba data dawo musu da bayarsu dasuke su kadai daga ita saishi
Tabasa dukkanin kaunarta da kulawarta data Saba basa,
Bata buqatan Yan uwanta ko nasa su kadai takeson suyi rayuwa
Idanma zaiyi aure saiya fada Mata ta rarrashi zuciyarta ta dauka
Amma duk wannan bazai yiyuba sbd wannan shine asalin hukuncinta sakamakonta na bujirewa iyaye.

Duk yanda taso kasa daurewa tayi bayan fitar Dr Abbakar Saida wasu irin hawaye masu tsananin zafi da Daci suka kubuce Mata ta Sunkuyar dakai sunata gangarowa Kan fuskarta zuwa kirjinta ta rintse ido kukanta yafara fitarda sauti ahankali Mai tsima zuciya.

Ta Jima cikin wannan halin tana kuka Mai quna da radadin zuciya kafin ta danne ta share hawayenta tareda goge fuskarta ta miqe ta fice batareda tambayar kudin lalurar asibitinba sbd sanin asibitin da likitocin asibitin duk na Turaki ne Wanda takanas sbd qarin lalurar Abban ya budeta Dan Haka komai na Abban a asibitin na musamman ne ko sisi basa biya.

Gida tadawo tashige daki tashige ta lalubo nata maganin Hawan jinin tana kokarin fitowa neman ruwa saiga Laylah tashigo dakin daukeda ruwa a jug takawo Mata masu Dan sanyi ganin tadawo cikin zafin Rana da ake kwadawa.

Qurawa jug din idanuwanta dasukai jajir tayi Momy tayi tanajin idanuwan na kokarin sake cikowa da hawaye ta miqa hannu ta karba jug din da cup ta aje tana zubawa tasha maganinta batareda ta dago ta kalli fuskar Laylah dinba wadda itama tuni ta sauke Kai tareda juyawa zuciyarta na sake karyarwa da yanayin data ga momyn aciki wadda itama ta tabbatarda rayuwar kawai takeyi ba acikin Jin dadiba sbd damuwar dukkanin komai da komai ma.

Bayan fitar Laylah komawa Momy tayi ta kwanta bakin gado tareda rufe idanuwanta dasukai ja da nauyi tanajin yanda zuciyarta ke azabtar da ita.

Itama laylah kasa komawa dakinta tayi ta zauna tsakar gidan sbd rashin sanin mezatai,ga Anty Sa'adah na daki sbd yauma wani irin habo tayi Mai yawa Wanda yasata kwantawa ko zata samu damarsa Wanda take ganin zafin da ake zubawa yau dinne yasata habon jinin ta hanci duk da Bata taba yinsaba sai jiya dakuma yau dinma dayazo Mata.

Yini tayi Babu kowa daya fito daga momyn har Anty Sa'adah din
Kowa da halinda yake ciki
Itama daurewa kawai takeyi Amma tana cikin tsananin pressure da wani irin yanayi datake ji Wanda ake Kira da asalin depression Dan kuwa ko numfashi tayi Jin takeyi kamar mutuwa zatafi Mata sauki akansa,
Batada Wanda zatai magana dashi kokuma muamala dashi dazai rage Mata tsananin nauyi da zuciyarta take ciki akan halinda Abbanta take ciki.
Chapter 9 · 0% Book details