← Book details Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 67

Sashe 49

Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsit sukai gabaki daya dakin suna kallonsa,
Anne da Momy da Abba dasukasan batada aure da mamaki da suke kallonsa,
Umma Jamila kuwa cikin kasa boye halin data shiga tayi saurin cewa"
Takardar ciki ta nuna ita ko me?

Miqawa Anne takardar yakuma Yi ganin tana Masa kallon buqatan qarin ya kalli sauran Yan dakin yaga duka iyayen Sa'adahn ne ya maida kallonsa kan Anne cikin nutsuwa yace"
Takardar pregnancy test ne tareda scanning Amma banajin nata ne sbd ba'a qasar Nan akaisa ba,
A America ne,Los Angeles....

Anne najin hakan ta karba takardar da sauri ta karance tsaf taga abinda yake ciki da sauri ta dago ta kalli Sa'adah Dake zaune tanajinsu Bata iya cewa komai sai rufe Ido datai cikin yanayi na rashin abin Yi.

Qamshin Bois elite ne yafara shigowa dakin Abba da Anne dasukan asalin waye Mai wannan qamshin Suka kalla kofa kafin shigowarsa
Tukuna ya shigo A Abdoul na bayansa
Dukkaninsu suka waiwayo suka kallesa yaqaraso cikin tsananin kwarjininsa daya Hana su umma Jamila tada hayaniyar murnar batun ciki da ake lokacin....

Haj Karima ce tayi qarfin halin gaidasa tana maida kallonta Kan Anne Baki washe tace"
Barka da arziki,
Ashe ciwon dai harda juna biyu ajikinta,
Allah ya raba lafiya yasa anbude hanyar tara zuria kenan...

Kujerar da A Abdoul ya gyara Masa ya zauna Yana kallon Abba dake neman rudewa da zancen da ake...

Anne ganin Kar rashin fahimtar tayi yawa ta bude Baki tana dauke kallonta daga kan Turaki daya Gama cika musu Ido dakin da kwarjini tace"
Ba sunan Sa'adah ne ajiki ba, takardar ba tata bace sbd ba komai ajikin Sa'adah.

Miqawa Turaki takardar tayi tana cewa"
Duba kagani ko zaka gane sakamakon waye.

Karba yayi tareda Dan kallon takardar akan sunan Mrs AB TURAKI idonsa yafara sauka kafin ya kalla date din jike jikin takardar.

Da sauri ya gangara da idonsa Kan signing dinta Dake qasan takardar.

Wani irin yanayi Mai wuyar fassarawa ya Shiga saidai mutanen Dake gurin ya sanyashi dannewa ya kame,
Miqawa A Abdoul takardar yayi bayan ya nade Yana miqewa yace"
Allah yabata lfy.

Kofa ya nufa ya fice A Abdoul na bayansa
Yan dakin duka kowa tsit yakuma Yi Dan su Kam Basu gane komaiba Kuma yanzu.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 43_*
Yana ficewa Momy taqi waiwayowa ta kalli Yan uwanta da duk anbi anhansu gane komai,
Sunanson nuna mrnarsu da farin cikin wannan samu daya samesu Amma Kuma ganin daga uban gayyar Turakin ya fice baice komaiba hakama Anne takasa cewa komai Dan itama kanta duk da tana zargin cikin idan bana Laylan bane Amma Kuma da wuya hakan ta faru, ita Tama Rasa tunanin kamawa,
Abbansu Sa'adahn ma kasa Kama kowanne tunanin yayi Dan Sam Bai kawo ma Laylah a zancenba tunda yasan karatu takeyi tukuna,
Kuma Turakin ma baida ranar amsarta amatsayin Mata shiyasa ma zai nema sallamarta daga Turakin Dan gudun shiga haqqin takurawa Amininsa.

Momy ce kawai tunanin farko daya shigeta shine tabbacin cikin Laylah ce take dauke dashi ba kowaba, sbd sanin barewa bazatai gudu 'danta yayi rarrafeba,
Ms Na'ima tayi babban kuskuren daukan riqon Laylah sbd batasan cin Amana a jininsu yakeba.. yanzu gashi itada Yan uwanta za'a kunno Mata masifa Dan kuwa su umma Jamila Allah kawai yanda zasu dauka wannan al'amari da aka rufesu baibai tsabar son Rai da cin Amana irin na Kawu saidu daya daura auren.

Anne Bata Gane sauran zancen da ake
a dakin sbd hankalinta gabaki daya baya Kai tunani take shiga daban daban na wannan takardar...

A saninta babu wata Mrs AB TURAKI Bayan Na'ima da Laylah,
Babu Kuma wata tsautsayi ko kaddaran dazai kawo sakamakon awon cikin Na'ima hannun Sa'adah,
Laylah ce kawai duniya sukeda kusancinda al'amari irin wannan Bata zaizo hannun Sa'adah...

Idan Natane to shi wannan ciki Kuma.....

Lumshe ido tayi Ahankali tana cire zancen cikin kanta gabaki daya Dan kuwa bazata taba Gane komaiba ayanzu zata saka ido taga Inda ciki zai bullo daga Mr Turakin koma wacece acikinsu.

Gida ta miqe ta wuce tabarsu suna buqatan kebancewa da Momy Suma Amma ta Hana kanta sakat da aikin hidimarta Sa'adah da zata bawa tea Mara zafi Dole Suka tafi Suka barta ba Dan sunbar zancenba Wanda Dole ayisa ai.

Saida suka wuce kafin Abba ma ya fito ya wuce da drivernsa da motarsa da aka Ware Masa.
********
Tunda suka baro asibitin Yana zaune a motar Bai ce komaiba Yana zaune hankalinsa kwance Kamar Babu komai cikin ransa
Saidai wasu feelings da tsantsar nutsuwa yakeji na wanzuwa cikin ransa.

Harsuka Isa gida Babu wata magana daya furta
Dan Haka A Abdoul na ganin yafito motar ya Ciro takardar da tuni ya sanyata cikin envelope ya miqa Masa a ladabce Yana cewa"
Mu kwana lafiya.

Karban envelope din yayi tareda wacewa ya nufi hanyar shiga makeken palonsa Dake sashensa dayafi na kowa girma a gidan ya shige.

Yana shigewa A Abdoul ma motarsa Dake gidan yanufa ya bude ya shige tareda tayarwa yabar gidan ya nufi gidansu Dan Mahaifiyarsa anan Abuja take zama duk da mahaifinsa ya Jima da rasuwa.

Bai tsaya palonsa ba Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa ya shige tareda nufar jikin drawer gefen gadonsa ya janyo ya sake tareda rufewa Yana aje wayar hannunsa ta nufi toilet yashige.

Wanka yayo yafito sanye da farar bathrobe ya nufi gaban mirror ya tsaya Yana goge jikinsa da qaramar towel fara.

Abubuwan daya Saba na kafin kwanciyarsa yayi kafin ya Sanya fararen pyjamas da slippers masu taushin gaske
qamshinsa na Bois elite na sake mamaye dakin ya nufi Kan sofa Dake dakin ya zauna anatse tareda daukan wayarsa Dake silent sbd rashin son damuwa
Kai tsaye numbernta dake sama yasaka kira.

"Hello Abbah" tafada cikin muryarta Mai taushi dake son bayyanarda kewarsa datai.

Boyayyan numfashi ya sake sbd koyaushe muryarta ta sauka kunnensa tana motsa duk wani jini dake yawo jikinsa.

Ahankali ya bude Baki Kai tsaye ya sakar Mata tambayar"
Are you pregnant?

Wata nawa ne?

Yana Nan ko kuwa?

Tsit tayi Jin tambayar data zuwar Mata a bazata
Kuma cikin yanayi na kamewarsa yayi Mata tambayar Dan Haka sai jikinta yayi Sanyi tana neman daburcewa,
Cikin kame kame tace"
Abbah kayi.....

Akaro na farko a rayuwarsu daya sakar Mata tsawa Yana cewa"
Amsa nake fara so, are you pregnant, yes or no
Ahankali tayi qasa da murya cikin sanyin jiki tace"
Yes Abbah.

Rufe ido yayi ahankali cikin yanayinda yakasa fassarawa tsawon mintuna kafin ya bude idon ya sake bude Baki ahankali yace"
Meyasa bansaniba?

Tsawon wane lokaci
Abba Ina tsoron mum ne tasani,
Nima bansan dashiba farko
Daga baya ne nasani
I'm sorry abbah, kayi hkr Dan Allah"" hawaye ne Suka balle Mata Jin yanayinsa kaman ransa ya baci akan rashin fadar Masa din.

Lumshe ido yayi yanajin yanda numfashin kukanta ke sauka cikin kunnensa Yana taba zuciyarsa
Sai daya sauke ajiyan zuciya ahankali kafin cikin nutsuwa ya bude Baki yace"
Ya Isa Haka,
Daina kukan,
tell me, is everything okay?

I mean the baby, kinajin komai lafiya?

Ki taba ganin likita?

Share hawayenta tayi tanajin kewarsa na sake kamata sbd cikinta yafara motsawa yanzu,
Gabaki daya cikin tsoro da tashin hankalin dawowar mum take ta bude Baki ahankali cikin yarinta tace"
Abba yayi girma Ana ganinsa,idan mum tadawo zata gansa,
Bansan me zataceba..

Babu abinda zai faru okay
Zan dawo da wuri zan kaiki kiga likita da kaina,
Ki ringa kula sosai yanzu, and ki daina saka su skinny jeans dasu kayanki masu matsewan nan Zaki takura kanki da babyn.

Zansaka akawo Miki nurse dazata ringa kuka Dake kafin nadawo.

Kwantawa tayi Kan kujeran datake zaune tana Jin son Abbanta na sake shigewa koina nata musamman cikin jikinta yanzu duk lokacinda ta Dora hannu akansa Abban takeji har cikin jininta sonsa na sake kamata.

Ahankali ta furta"
"Abbah, are you happy with th...."
kasa qarasawa tayi sbd nauyinda kalmar Tayi Mata saidai Kamar daga sama taji saukan muryarsa Mai dadi da Kamala cikin kunnenta yace"
I love the baby,and I love his mother....

I love you both.

Cikin tsananin farin ciki da nutsuwa
jikinta na mutuwa da kalamansa tace"
We love you too Abbah.

Ms Na'ima Dake tsaye bakin kofar bedroom din nasa kasa tsayuwa tayi sbd wani jiri jiri datake gani,
Me take ji Abu kamar a mafarkinta.

I love you taji abakin Turaki,
Maganar baby da uwar baby yake bayan saninta Sa'adah na asibiti Kuma tabbas sun biya kudin gaske likitan asibitin da aka fara kaita ya tabbatar musu da Babu ciki ajikinta suna murnar ya zube me take Shirin ji yanzu??????

Innalillahiiiii"" tafada a fili idonta na rage ganin haske ta juya da sauri Takoma inda ta fito tana bude idanuwanta da hannuwanta Dan bakin Rai Bata gani Sosai.

Tana Shiga palonta a haukace ta zubawa siddika Kira tana cewa"
Kaini dakina bana gani Sosai.

Da sauri siddika takaita daki ta fito sbd ganin masifar Dake cikeda idon dayasa Bata gani Sosai...

Hannu ta Dora akai tanason kurma ihu Amma maqoshinta yaqi budewa ta zube bakin kujera tana cewa"
Wace kaddararrarce Turaki yake cewa I love you harda baby?

Neman Mata Turaki ya fara kokuwa wani auren yayi Basu saniba?

Nashiga goma na lalace,
Mata nawa Turaki yakeson nabi Ina hallakawa
Walh bazan yarda da wannan masifarba,
Ko ba aure yayiwa koma wacece wannan cikin bazata Bari a haifesaba,
Ta yarda tayi koma menene Amma wlh bazata yarda wata ta haifawa Turaki 'yayaba.....

A haukace ta dauki wayarta tafara neman numbern Zinat....

Tana dauka cikin yanayin tashin hankali Mai tsanani da rudewa tace"
Zinat abun yamun yawa Turaki zai cinnamun hauka,
Zinat Turaki wata yayiwa ciki wlh,
Zinat Turaki I love you yake furtawa wata....

Zuciyata bugawa zatai..

Cikin gajiya da wannan masifa itama Zinat din tace"
Ki nutsu Na'ima tunda kema kingano Cinna Miki hauka al'amarin Turaki zaiyi,
Tashin hankali bazai Bari musan abinda mukeson saniba...

Turaki yagama bamu mamakin duniya tunda yayi aure bare yanzu Dan yayiwa wata Mai rubutacciyar qaddara a hannunmu ciki,
Fatan dai kin gano wani Abu akanta ba haukar banza kikayoba Kika dawo?
Chapter 49 · 0% Book details