← Book details Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 67

Sashe 27

Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rufe wayarta tayi tareda sakawa cikin aljihun kayan baccin jikinta ta nufi ruwan tean dasuka kashe kansu tuni tana kokarin zubawa ta dago a natse cikin girmamawa tace"
Wani Abu za'a kawo?

Black tea za'a kawo mun.

Gyada Kai tayi batareda ta dagoba
Ya juya ya fice.

Dayake Taci cake dinta sama Sama Tasha tea din tana Gama sha nasa data Dora Yana mutuwa ta juye Masa tareda jera cakes biyu a gefe ta kashe komai ta fito kitchen din.

Bata gansa Palo ba Dan Haka saita qarasa bakin kofar bedroom dinsa cikin nutsuwa tayi knocking ahankali tareda dakatawa.

Saida takuma knocking kafin ahankali taji muryarsa daga cikin yace"
Yes.

Faduwa gabanta yayi sbd alamar tashigone yayi Mata saidai Bata fatar zuciyarta sufara yimasa wani daukan da kallon daya wuce na uba tunda Kai tsaye take Shiga dakin mahaifinta Dan Haka Murda kofar dakin tayi Ahankali tashigo ba haske sosai a dakin Yana zaune Kan sofa idanuwansa akan waya Bai dagoba Amma duk da hakan ta lurada idanuwansa sun sauya alamar rashin lafiya ko damuwar aiki.

Nufarsa tayi qafafunta na Dan rawa da hannuwanta Dake riqe da tea din ta Isa gabansa ta ranqwafa ta ajiye idanuwansa suka dago cikin rashin sa'a Suka sauka cikin nata take ta rikice ba tsammani ta sakarwa hannunta daya tea din cikin tsananin azaba tayi saurin kokarin ajewa tana sakin qaramar qara a bayyane jikinta na qara daukan rawa saidai sbd arikicen datake batama San ba daidai zata aje sauran tea dinba.....

Hannunsa na dama yakai ahankali ya Kama hannunta Dake rawa zata qarasa Kona kanta
Lokaci daya ta dago batareda ta iya kallonsaba
Ya karba cup din ya ajiye ahankali kafin ya dago ya kalleta da idanuwansa Dake kokarin sauyawa Yana kokarin controlling din kansa ya saketa tareda dauke kallonsa gabaki daya daga kanta can qasan maqoshi ya furta"
Ki ringa kula kina kiyayewa.

Daukan cup din tayi ta fita daga dakin Takoma kicin takuma zubo Masa wani a cup daban tadawo takawo Masa Allah yasa koda ta fita a bude tabar dakin tana dawowa sallama tayi ta shigo ta ajiye Masa ganin bata gansaba yasa Bata tsorata ba ko Shiga wani yanayin ko kadan...

Tana juyowa zata fice taji an janyota ahankali ta bayanta Tareda Bata wata kyakkyawar runguma ta bayan Yana matseta sosai cikin jikinsa hannuwansa Suka sauka Kan shafaffen cikinta yayinda tudun kirjinta da taushinsu da batada bra aciki ya shafar Masa hannu take ya qarasa kasa riqe kansa
Yasake shigarda ita jikinsa sosai Yana sake wasu numfashi a jejjere dasuka kusan sumar da Laylan wadda Tai mutuwar tsaye cikin tsananin firgici, tsoro dama dauke wuta sbd ba qaramin riqo yayi Mata ba jikinta sosai ya dauki rawa idanuwanta na kankancewa saidai ko kadan takasa motsawa sbd tsabar firgita.

Kansa ya zura cikin wuyanta ya shaqa wani qamshinta Mai shegen dadin gaske Yana sake matseta da hannuwansa ba zato ya saketa tareda birkitota ya daga cak ya aje zaune Kan mirron dakin kayan Kai duk wasu Suka watso qasa bai tsaya komaiba ya kamo kanta da hannayensa ya Kai bakinsa ya hade da nata cikin yanayi na zazzafar sha'awarsa data Gama galabaitar dashi Dan Haka yahau kissing dinta cikin yanayin dayayi Masa masifar dadin gaske,
Kokarin qwatar kanta tayi Amma Bai Bata damar hakan sbd yariga ya tare gabanta Babu wani motsin dazata iya ba cikin jikinsa ba,
Hannu yasa ya Kama rigar jikinta ya farka tareda jefarwa fararen jikinta suka bayyana a filin Allah gabansa
Yakai hannuwansa masu taushi yafara yamutsa tako Ina har Lokacin bakinsa na cikin nata wani irin rough kiss yake Bata da gabaki daya jikinta ya mutu mutus Dan kuwa kasa yunqurin kwatar kanta tayi tanajin hannuwansa Babu inda basa tabawa ajikinta cikin yanayi Mai zafi da Dadi.

Duk wani abin dake gaban madubin dakin sun Gama watsoshi qasa sbd komai yagama daukan zafi a yanayinsun
Musamman daya Gama farka kayan jikinsu ya watsar a tsakiyar dakin
Yakuma daukan cak ajikinsa batareda ya raba bakinsa da nataba dayake Bata wani rough passion kiss daya Gama rikita kwanyarta gabaki daya komai ta daina fahimtar abinda yake
Ya nufi lafiyayyan qaton gadonsa Dake shimfide da fararen beddings masu shegen taushi ya Haye da ita sai Alokacin ya zare bakinsa a nata Yana kissing wuyanta zuwa kirjinta Dake sama Yana qasa tsabar tashin hankali da tsoro
Shikuma hakan ya qarasa birkita desire dinsa yafara kokarin Yin babban aikin ta qanqamesa tana sakin kukan Mai tsananin qarfi tana Kiran sunansa a wahalce tareda girgiza Kai cikin magiya.....

Dakatawa yayi cak cikin wani Irin mummunan yanayi Yana Dan dawowa kansa yaga abinda yake Shirin aikatawa
Take ya saketa Yana komawa gefe cikin mummunan yanayi ya sauka gadon tareda zarar towel daya fito toilet dashi dazu ya daura ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwa cikin yanayi Mai matuqar wahalar gaske.
##MAMUH#*_Mamuhgee 24_*
Jikinta amatuqar mace yake Yana rawa ta janyo rigarsa Dake gefenta ta rufawa jikinta ta sauko gadon tareda nufar kofa ta fice dakin ta nufi Wanda take ciki tashige.

Tana Shiga daki toilet ta nufa da sauri itama ta sakarwa kanta ruwa tana Jero Ajiyar zuciya ba kakkautawa sbd ba qaramin yamutsa kwanyarta da birkita tayiba da abinda yafaru mintinan dasuka wuce a bedroom dinsa.

Saidataji tana neman shidewa ta fito ruwan tadauro towel ta fito ko kanta daya jiqe da ruwan data sakarwa kanta Bata busarba ta saka wasu kayan baccin ta kwanata tareda duqunqunewa cikin bargo.

Asubar fari ta tashi sbd dama Bata samu damar bacci ba ko kadan
Dukkanin abinda yafaru ya tsaya Mata cikin Kai koina ta juya hannuwansa takeji suna yawo jikinta,
Bakinta kuwa harda safen datai brush tanajin sauran qamshin Lebon mint mouth wash aciki.

Wayarta tahau dubawa Bata ganiba Dan Haka tayi amfani da iPad dinta tayiwa kanta booking ticket na komawa Atlanta
Ta tashi tayo wanka ta shirya cikin dogon pencil skirt da Riga ta Dora kimono har qasa akai ta fito janyeda akwatinta cikin sa'a kuwa batagansa ba bare motsinsa ta fito ta tari taxi sai airport.

Kodata Isa Atlanta Sofia takira tazo ta dauketa takawota gida lokacin mum Na'ima na babban palon gidan tareda Haj Zinat suna fira hankali kwance suna jiran agama hada dining suje cin abincin Rana.

Tare suka kalleta dukkaninsu cikin kulawa da farin ciki Haj Zinat tace"
Masha Allah Laylah tadawo
Ashe da rabon zamu hadu kafin natafi.

Janyo hannunt
a ms Na'ima tayi tana cewa"
Happy to see back baby,.so ku gaisa da Zinat tanata son ganinki kafin ta tafi kuwa..

Wani irin nauyin mum din takeji Mai tsanani da kunyar kanta Dan sai tanajin Kamar wani zaisan abunda yafaru tsakaninta da Turakin acan
Ta qaraso a darare gabansu tana Dan sakin murmushin Dole da sanyin murya tace"
Sannu da suwa Momy Zinat,
Ya hanya?

Yaya su Anty farida?

Lafiya kalau Laylah
Ya karatu?

Da rayuwan Atlanta?

Kinata kokari ko?

Allah ya taimaka kinji?

Amin Momy Zinat nagode.

Kallon Ms Na'ima tayi a sanyaye tace"
Mum ya gida?

Bakizoba nadawo sbd school Sofia nata kirana.

Da kulawa tace"
Barin nayi har Zinat ta tashi tafiya saimuje LA din tareda ita itama ta duba Abban naki dama daga can ta wuce.

Murmushin yake kawai tayi tareda nufar hanyar dazata kaita bedroom dinta tana cewa"
Ok Bari na shiga ciki da ciwon Kai na dawo sbd mura.

Tana shigewa dakinta Cindy dake gyara Mata dakin tun shigowarta ta Isa dakin tafara gyara Mata kafin tashigo ta kalli Laylan tana cewa"
Welcome Ms Laylah.

Kai kawai ta gyada tareda aje kayan hannunta tayi hanyar toilet tashige.

Kodata fito Cindy tagama komai ta fice Dan Haka sallah kawai tayi ta Haye gado ta kwanta ko abinci Bata fito taciba taredasu mum Na'iman Dan wani irin mutuwar jiki yake tareda ita.

Sai dare ta daure ta fito sbd mum Na'iman datake ta tambayar lafiyarta kalau kuwa
Dole ta sake tafito sukaci abincin dare tare harma ta zauna Palo tana Amfani da iPad dinta kusan karfe goma kafin ta tashi tashige.

Washe gari tanada zuwa school Dan Haka tana tashi wanka tayi sama sama Tai breakfast sbd tayi latti ta wuce makaranta.

Kwana biyu Bata zama Sosai sbd makaranta kafin tasamu kanta har tana hutawa gida sosai
Daga bayama dasuka samu break koyaushe tana kicin taredasu Cindy matuqar tana gida Dan mum Na'iman kam tayi busy Sosai Bata zama sunata hidimar business dinsu dasuke na kayan da Haj Zinat zata tafi dasu.

Ranar data cika kwana Tara da dawowa ranar Turaki ya dawo gidan tana fitowa daga dakinta da safe ya nufa dining room sanyeda fararen Riga da wando kanta sanyeda hular sanyi fara itama ta shiga Kai tsaye
Sai ganinsa tayi zaune Kan kujerarsa sanyeda milk Balenciaga polo shirt da milk Wandon Alexander yayi wani irin fresh haske gabaki daya yacika dakin da qamshinsa fuskarsa na Kan abincin dayake ci Bai dagoba.

Rudewa take nemanyi sbd faduwar da gabanta yayi na rashin tsammanin ganinsa ta saci kallon Ms Na'ima Dake zaune tana cin abincin tana Masa Dan surutu ta daidaita kanta da murya Mai Dan sanyi tace"
Ina kwana Abba.

Dagowa yayi a zuba Mata fararen idanuwansa dasuka qarasa rudar da ita Amma ta Dan Dake tana kallon Ms Na'ima tace"
Good morning mum.

Morning Laylah
Qaraso Mana,
Abbanki ma gashi yadawo
Zo muyi family breakfast.

A sulale ta qaraso tana zaunawa batareda takuma dagowaba.

Gurin yayi tsit suna cin abinci sai Ms Na'ima Dake zuba zancenta na kisisinar son bin Haj Zinat dazatai Dubai su qarasa siyayyar kayan manyan shagunansu Dake Nigeria din Dan Haka kudi takeso sosai yabata dakuma qarin kamar yanason daukar tsarin zamanta a gida a Yan kwanakin ta lura saidai tunda yariga ya Saba Mata da baya takurata sai hakan yazo Mata wani iri bakuma tanajin zata iya zama guri daya.

Suna gamawa ita tafara tashi ta bar gurin Dan tanajin takurar zaman dama
Daki Takoma ta kunna wayarta da Cindy tabata tana fitowa tace A Abdoul ne yace tabata.

Cajin wayar tasaka tareda Shiga ciki tana duba abubuwa.
Chapter 27 · 0% Book details