← Book details Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 67

Sashe 63

Noor Albi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har akai sallar asuba siddika na zaune tana yawon bandaki sbd tsoro da jiran wani tashin hankali daga Zinat Amma shiru
Dan haka tana Gama sallah ko wanka batayiba ta fito tana aikin kaida kawo na aiki a kitchen ko zataji wani zancen Amma shiru duk da hakan hankalinta har lokacin a matuqar tashe yake.

Qarfe goma Suka fito Haj Zinat shiye tsaf cikin wani arnen tsadadden lace brown sai handbag dinta da takarman Dior sai qamshi take zubawa.

Ms Na'ima kuwa doguwar Rigar Dubai ce ajikinta ta wani tsaddaden material blue fuskarta ta fada sosai a dare daya sbd qwar da aka Bata Mai tsananin karfice wadda har lokacin ajikinta Bai saketaba saima tsananin juyar Mata da qwaqwalwa datake qara Yi Amma allurar da akai Mata yasa Bata iya komai sai jikinta a sake sake take ba qwari sai sun Isa zata banka Mata wata qwayar abun ya tashi.

Dan Haka ko breakfast Basu tsaya sunyiba Suka fice zuwa airport.

Suna fita da awa daya siddika ta Isa dakin Haj Zinat ta hau bincike jikinta na wata irin rawar tsoro da tashin hankali ta ringa watsi da Kaya tana bincike dakin.

Daqyar tagano jakar data fita da ita jiyan da gwalagwalan Ms Na'ima tadawo da ita Kila ba'a siya yanda takeso ba Dan Haka Bata tsaya Bata lokaciba ta dauke jakar ta fito ta nufi kitchen ta zazzage kwandon sharar ta dauki ledar takardun ta fito sanyeda doguwar Riga da qaramar hijabi ko ganin gabanta batayi Sosai
Har saidata ga anason Gane Bata hayyacinta tukuna tayi kokarin saita kanta ta dauka drp din mota zuwa Gidan TURAKI.
*******Cikin kwanakin datayi a gidan tasamu kwanciyar hankali da nutsuwa
Hakama anty Sa'adah zuwan laylan yasa tasamu kanta cikin wata sabuwar rayuwar kwanciyar hankali da nutsuwa sbd zuwanta yasa shaquwa da sabuwar kauna ta qaru tsakaninta da Abbansu sbd dama ba wani shaquwa tsakaninsu Sosai.

Momy gabaki daya tun zuwan Laylah ta Rasa walwalarta ta zaman gidan
Koyaushe Bata zama gida,
Abba baida magana saita Laylah da cikinta,
Ga yarta da abban sun koma tamkar wasu bayin Laylan hidimarta kawai suka sani,
Ta bangare daya ma Sa'adahn batada lfya tana fama da yawan habon jini koyaushe Amma taqi tsayawa suje asibiti sbd idan adacan zafi ne yanzu suna rayuwar AC koina tayaya za'ace zafi ne tafi kyautata zaton Dan kanoma ne sbd idan yayiwa mutum tsanani yakan saka hakan wani lokaci...

Ita babbar damuwarta kada ya taba lafiyar Mara Kota mahaifar Sa'adah
Ganin yanda takewa Laylah ta tabbatarda tanajin tsananin kewar inama zatai auren ta Haifa nata 'yayan.

Yau tunda safe ta shirya itada Sa'adah Suka nufi asibiti sbd Abba da kansa yace Sa'adahn taje asibiti.

Daga Laylah sai Ruky da hadiza Dake aiki ne a gidan ko Abban bayanan ya fita tareda Abdullahi zuwa tsohon gidansa da ake gini.

Zaune take Palo sanyeda doguwar Riga Mai qaramin hannu sai farar hula akanta
Fuskarta tayi fresh sbd hutu.

Furar dataji Madara d fresh nono takesha cikin cup tana duba wayarta dataketa Kiran Abbahh Bata shiga,
Yau tun safe take kiransa takasa samu..

Hankalinta baya Kan tv Dake aiki Yana Kan wayar hannunta Dan Haka ko dataji sallama bata dagoba sai data aje wayarta Dake hannunta gefe tareda kallon kofar tunaninta su Anty Sa'adah ne suka dawo.

Cup din hannunta ne ya subuce Mata lokaci daya tana sauke kafarta data miqe daga Kan table dake gabanta gabanta yayi mummunan faduwa ta miqe tsaye tana kallon umma Jamila dake gaba Haj Karima na biyo bayanta sai Anty fatima.

Cak umma Jamila ta tsaya tana kallon fuskarta da kyau sbd kwanakin tana fama da Ido ta waiwayo ta kalli Haj Karima Dake qarasowa ciki idonta akan cikin Laylan itakuma tace"
Haj karima wannan Kuma dai gata Kamar 'yar Mahmoud da kishiyar zainab kokuwa idon ne?

Anty Fatima datake qanwarsu tace"
LAYLAH?????

Qarasowa suka fara Yi umma Jamila na sake qure kallonta akan Laylan da mugun mamaki tace"
Harda tsarabar cikinta tadawowa Mahmoud gashinan ajikinta.

Wata muguwar dariya Haj Karima tasaki tana nufar kujera ta zauna tace"
Allah sarki,
Shikuwa Mahmoud ahaka zai qare daga haihuwar 'yar da ba'a tabbatarda aurensa da uwartaba sai samun jikan wata hanyar.

Hannu umma Jamila takai ta janyeta da qarfi ta watsar gefe tareda zaunawa tana cewa"
Can ya matse musu idan shege dari zata Haifa su Suka sani,
Fata dai wlh baza'a haifawa zainab shege acikin gidaba,
tunda bin baza ta zaba taj ta bisu can kowama ya huta.

Tashi tayi daga jefar da ita da umma Jamilan tayi tareda Dan sauke Kai cikin girmamawa ta gaidasu Amma Babu Wanda ya kalleta bare ya tanka
Ta juya tabar gurin jiki Amace ta shige daki.

Tana shiga su Momy na shigowa
Tun a haraba da Momy taga motar umma Jamila tasan suna gidan hankalinta yaso tashi Amma Kuma ta Dake tunda ba ruwanta da shaanin Laylahn ita yanzu ta yarta da aka dinga diban jinin Dan gwaje gwaje take.
##MAMUH#*_Mamuhgee 55_*
Momy na shigowa palon ta kallo daya tayiwa fuskokinsu ta dauke Kai tana qarasowa ta zauna tareda bude Baki a sanyaye ta gaidasu sbd ganin yanda umma Jamila ke Mata kallon datasan maganar da za'a fada Mata bamai Dadi bace.

Ita kanta Sa'adah jikinta mutuwa ya sakeyi akan na zazzabin data dawo dashi na dibar jininta da aka ringa Yi dakuma kaida kawo,
Daqyar ta iya driving dinsu Suka dawo gidan.

Cikin sanyin murya ta gaidasu ta juya ta nufi dakinta ta shige.

Gabaki daya jikinta a mace yayi yayi Sanyi sosai hakanan yau zuciyarta take sakayau Bata Jin nauyin komai Kamar wadda ba zuciyar a kirjinta.

Laylah na zaune tashigo Bata iya cewa komaiba ta wuce toilet tayo wanka da alwala tafito daureda qaton towel ta shirya cikin Riga da skirt na atamap ta Sanya qatuwar hijab ta tada sallah.

Tana idarwa hadiza ta shigo ta kawo Mata abinci Amma Sam batajin cin abincin
Ruwa kawai Tasha ta Haye gado ta kwanta tareda rufe ido koina na gabobin jikinta suna Mata ciwo.

Cikin kulawa Laylah tayi Mata sannu tareda gyara Mata rufarta Jikinta na sanyi tace"
Anty Sa'adah ko dai zaki koma Abuja ne saikiga likata acan?

Girgiza Kai tayi tana cewa"
Bafa komai bane Momy ce itama duk tabi ta daga hankalinta.

Wani sanyayyan murmushi Laylan tasake ahankali Jin abinda anty Sa'adahn tafada,
Ahankali tace"
Momy Dole zata damu tunda bakida lafiya Kuma jikinki ya nuna hakan.

Yanda Laylah tayi mganar cikeda sanyin jiki Dana murya yasa anty Sa'adahn bude idonta ta zubawa Laylahn sbd tajiyo 'dacin rashin mahaifiya acikin sautin maganarta.

Ahankali ta bude Baki tace"
Laylah kinsan cewa kinfimu gata dagani har Momy?

Rashin mahaifiya bashine rashin uwa ba,
Kina tareda soyayyar mahaifinki tun lokacinda kike qaramarki cikin Hali na maraicin uwa,
Kin taso cikin Rashi na makusanta Amma Kuma nida Momy mun rayuwa cikin Yan uwan da makusantan Amma Kuma a qasqance sbd ganin Ana tallafe damu,
Ki godewa Allah da wani kadaicin da wani rashin makusantan alkhairi ne tunda gashi yanzu daga mu din har makusantan mu muna qarqashin inuwarki,
Wani gatan da Jin dadin da Turaki ya sakar Mana bana kusancinsa da Abba bane kawai na girman dakike dashi ne a zuciyarsa..

Dan Haka Laylah ki daina Jin daci arayuwarki Dan bakida maraici yanzu.

Murmushi Mai ciwo Laylah tasaki tareda maida hawayen dasuka ciko idanuwanta ta bude Baki akaro na farko datai maganar maraicinta na rashin uwa tace"
Anty Sa'adah duk gatan dazan samu a duniya zanso inada mahaifiyar da zata kalleni tasan ciwona da damuwata saidai Allah Bai kaddareni da samun wannan gatanba saiya bani wani gatan na daban...

Tashi zaune anty Sa'adah tayi tana kallon fuskarta tace"
Laylah maraicin mahaifiyar data haifeki kawai Zakiyi sbd Babu Wanda zai taba maye gurbinta Amma na tabbata Anne da abbah turaki bazasu taba Bari kiyi wani maraicinba har lokacinda Momy zata bude Miki zuciyarta ki Shiga ta karbeki amatsayi na 'ya..

Wani sanyayyan murmushi takuma saki hawayen datake riqewa Suka ga gangaro Mata sbd tasan qaddararta da Momy Allah Bai rubuto musu zama makusantaba.

Murmushi Sa'adah tayi tana cewa"
Kina mamaki ne?

Inshallah wata Rana zaki samu gurbi Mai girma a azuciyarta.

Shiru kawai Laylah tayi Bata sake cewa komaiba har bacci ya dauke Anty Sa'adahn
Ta zuba Mata idanuwanta dasukai ja sbd hawayen datayi.,
Anty Sa'adah zuciyarta Mai tsafta ce shiyasa take ganin Momy zata kaunace kamar 'ya wataran,
Ita basai momyn ta karbetaba ahakama tana kaunarta sbd itace mahaifiyar Anty Sa'adah.

Wayarta Dake gefenta takuma dauka ta saka Kiran Abbahh Amma still Bata shiga,
Hakanan takejin kadaici da maraici na shigarta Dan Haka ta koma Kan kujera ta zauna rakube tana kallon fuskar Anty Sa'adah Dake bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Hayaniya ce ta kaure a Palo ba zata ba tsammani sai ganin umma Jamila tayi akanta tana dago fuskarta kuwa ta kifa Mata wasu fararen Marika a jere tareda finciko ta tayo Palo da ita jikin har wani irin rawa yake tana cewa"
Nafada nakuma fada wannan itace muguwar qaddarar rayuwarki Zainab Dake da 'yarki Kika qi Jina ga irin kyakkwan sakamakon data nuna na cewan ita jinin Mahmoud da uwarta ne,
Mahmoud ne da matsiyacin Kawun can suka daure gindi akai wannan gagarumar cin amanar ta sauyawa Sa'adah Miji a daurawa wannan maciyar Amanar butulu wadda Bata gade alkhairi,
Tsawon shekaru Muna dakon aure Sa'adah keyi shine sai yanzu kike sanar damu riqonta akeyi a gidan turaki
Kutumar uban riko duk inda yake
Wlh yau Mahmoud saina wanke Masa allon rashin mutinci.
Chapter 63 · 0% Book details